8
Zuriyar Shawulu mutumin Benyamin
Benyamin shi ne mahaifin,
Bela ɗansa na fari,
Ashbel ɗansa na biyu, Ahara na uku,
Noha na huɗu da Rafa na biyar.
’Ya’yan Bela maza su ne,
Addar, Gera, Abihud Abishuwa, Na’aman, Ahowa, Gera, Shefufan da Huram.
Waɗannan su ne zuriyar Ehud, waɗanda suke kawunan iyalan waɗanda suke zama a Geba waɗanda aka kuma kwasa zuwa Manahat.
Na’aman, da Ahiya, da Gera. Gera ne shugabansu lokacin da aka kai su bauta, shi ne ya haifi Uzza da Ahilud.
An haifa ’ya’ya maza wa Shaharayim a Mowab bayan ya saki matansa Hushim da Ba’ara. Ya haifi Yobab, Zibiya, Hodesh, Malkam, 10 Yewuz, Sakiya da Mirma ta wurin Hodesh matarsa. Waɗannan su ne ’ya’yansa, kawunan iyalai. 11 Ya haifi Abitub da Efa’al ta wurin Hushim.
12 ’Ya’yan Efa’al maza su ne,
Eber, Misham, Shemed (wanda ya gina Ono da Lod tare da ƙauyukan kewayensu), 13 da Beriya da Shema, waɗanda suke kawunan iyalan waɗanda suke zama a Aiyalon waɗanda kuma suka kori mazaunan Gat.
14 Ahiyo, Shashak, Yeremot 15 Zebadiya, Arad, Eder, 16 Mika’ilu, Isfa da Yoha su ne ’ya’yan Beriya maza.
17 Zebadiya, Meshullam, Hizki, Heber, 18 Ishmerai, Izliya da Yobab su ne ’ya’yan Efa’al maza.
19 Yakim, Zikri, Zabdi, 20 Eliyenai, Zilletai, Eliyel, 21 Adahiya, Berahiya da Shimra su ne ’ya’yan Shimeyi maza.
22 Ishfan, Eber, Eliyel, 23 Abdon, Zikri, Hanan, 24 Hananiya, Elam, Antotiya, 25 Ifdehiya da Fenuwel su ne ’ya’yan Shashak maza.
26 Shamsherai, Shehariya, Ataliya, 27 Ya’areshiya, Iliya da Zikri su ne ’ya’yan Yeroham maza.
28 Dukan waɗannan su ne kawunan iyalai, manya kamar yadda aka lissafta a cikin zuriyarsu, suka zauna a Urushalima.
 
29 Yehiyel na Gibeyon ya zauna a Gibeyon.
Sunan matarsa Ma’aka, 30 ɗansa na fari kuwa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba’al, Ner, Nadab, 31 Gedor, Ahiyo, Zeker 32 da Miklot, wanda ya zama mahaifin Shimeya. Su ma sun zauna kusa da danginsu a Urushalima.
33 Ner shi ne mahaifin Kish, Kish mahaifin Shawulu, kuma Shawulu ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab da Esh-Ba’al.
34 Ɗan Yonatan shi ne,
Merib-Ba’al*Aka kuma sani kamar Mefiboshet wanda ya zama mahaifin Mika.
35 ’Ya’yan Mika maza su ne,
Fiton, Melek, Tereya da Ahaz.
36 Ahaz shi ne mahaifin Yehowadda, Yehowadda shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza. 37 Moza shi ne mahaifin Bineya; Rafa, Eleyasa da kuma Azel.
38 Azel yana da ’ya’ya maza shida, kuma ga sunayensu.
Azrikam, Bokeru, Ishmayel, Sheyariya, Obadiya da Hanan. Dukan waɗannan ’ya’yan Azel maza ne.
39 ’Ya’yan ɗan’uwansa Eshek su ne,
Ulam ɗan farinsa, Yewush ɗansa na biyu da Elifelet na uku. 40 ’Ya’yan Ulam maza jarumawa ne sosai waɗanda suke iya riƙe baka. Suna da ’ya’ya maza masu yawa da jikoki, 150 gaba ɗaya.
Dukan waɗannan zuriyar Benyamin ne.
 

*8:34 Aka kuma sani kamar Mefiboshet