25
Mawaƙa
Dawuda tare da shugabannin mayaƙa, suka keɓe waɗansu daga ’ya’yan Asaf, Heman da Yedutun don hidimar yin annabci, suna amfani da garayu, molaye da ganguna. Ga jerin mutanen da suka yi wannan hidima.
 
Daga ’ya’yan Asaf,
Zakkur, Yusuf, Netaniya da Asarela. ’Ya’yan Asaf sun kasance a ƙarƙashin kulawar Asaf, wanda ya yi annabci a ƙarƙashin kulawar sarki.
Game da Yedutun kuwa, daga ’ya’yansa maza.
Gedaliya, Zeri, Yeshahiya, Shimeyi, Hashabiya da Mattitiya, su shida ne duka, a ƙarƙashin kulawar mahaifinsu Yedutun, wanda ya yi annabci, yana amfani da garaya a yin godiya da yabon Ubangiji.
Game da Heman kuwa, daga ’ya’yansa maza.
Bukkiya, Mattaniya, Uzziyel, Shebuwel, Yerimot; Hananiya, Hanani, Eliyata, Giddalti, Romamti-Ezer, Yoshbekasha, Malloti, Hotir da Mahaziyot. Dukan waɗannan ’ya’yan Heman ne mai duba na sarki. An ba shi su ta wurin alkawarin Allah don yă ɗaukaka shi. Allah ya ba Heman ’ya’ya maza goma sha huɗu da ’ya’ya mata uku.
 
Dukan waɗannan mutane suna a ƙarƙashin kulawar mahaifansu don kaɗe-kaɗe da bushe-bushe a cikin haikalin Ubangiji, da ganguna, molaye da garayu, don hidima a gidan Allah.
Asaf, Yedutun da Heman suna ƙarƙashin kulawar sarki. Da su da danginsu, dukansu su 288 ne kuma horarru da ƙwararru ne a kaɗe-kaɗe da bushe-bushe domin Ubangiji. Baba ko yaro, malami ko ɗalibi, duk suka jefa ƙuri’a saboda ayyukan da za su yi.
 
Ƙuri’a ta fari, wadda take don Asaf, ta fāɗo a kan Yusuf, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
ta biyu a kan Gedaliya, danginsa da ’ya’yansa maza, 12
10 ta uku a kan Zakkur, ’ya’yansa da danginsa, 12
11 ta huɗu a kan Izri, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
12 ta biyar a kan Netaniya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
13 ta shida a kan Bukkiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
14 ta bakwai a kan Yesarela, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
15 ta takwas a kan Yeshahiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
16 ta tara a kan Mattaniya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
17 ta goma a kan Shimeyi, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
18 ta goma sha ɗaya a kan Azarel, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
19 ta goma sha biyu a kan Hashabiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
20 ta goma sha uku a kan Shubayel, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
21 ta goma sha huɗu a kan Mattitiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
22 ta goma sha biya a kan Yeremot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
23 ta goma sha shida a kan Hananiya, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
24 ta goma sha bakwai a kan Yoshbekasha, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
25 ta goma sha takwas a kan Hanani, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa 12
26 ta goma sha tara a kan Malloti, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
27 ta ashirin a kan Eliyata, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
28 ta ashirin da ɗaya a kan Hotir, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
29 ta ashirin da biyu a kan Giddalti, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
30 ta ashirin da uku a kan Mahaziyot, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12
31 ta ashirin da huɗu a kan Romamti-Ezer, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa 12.