11
Matan Solomon
1 Sarki Solomon ya ƙaunaci baƙin mata. Ban da ’yar Fir’auna, ya auri Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, Sidoniyawa da Hittiyawa. 2 Sun fito daga al’ummai da Ubangiji ya ce wa Isra’ilawa, “Kada ku yi aurayya da su, domin tabbatacce za su juye zukatanku zuwa ga waɗansu alloli.” Duk da haka Solomon ya manne musu, ya nace, yana ƙaunarsu. 3 Ya auri mata ɗari bakwai, haifaffun gidan sarauta, da kuma ƙwarƙwarai ɗari uku. Matan nan nasa suka karkatar da shi. 4 Yayinda Solomon yake tsufa, matansa suka juye zuciyarsa ga bin waɗansu alloli, zuciyarsa kuwa ba tă bi Ubangiji Allahnsa ɗungum kamar yadda zuciyar Dawuda mahaifinsa ta kasance ba. 5 Ya bi Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Molek*Da Ibraniyanci Milkom; haka ma a aya 33., allahn da aka hana na Ammonawa. 6 Saboda haka Solomon ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji. Bai bi Ubangiji gaba ɗaya kamar yadda Dawuda mahaifinsa ya yi ba.
7 A kan tudu, gabas da Urushalima, Solomon ya gina masujada a can domin Kemosh, allahn da aka hana na Mowab, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa. 8 Ya yi haka domin dukan baƙin matansa, waɗanda suka ƙone turare suka kuma miƙa hadayu ga allolinsu.
9 Ubangiji ya yi fushi da Solomon domin zuciyarsa ya juye daga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya bayyana masa sau biyu. 10 Ko da yake ya hana Solomon bin waɗansu alloli, Solomon bai kiyaye umarnin Ubangiji ba. 11 Saboda haka Ubangiji ya ce wa Solomon, “Da yake halinka ke nan, ba ka kuma kiyaye alkawarina, da ƙa’idodina da na umarce ka ba, tabbatacce zan yage masarautar daga gare ka, in ba da ita ga ɗaya daga cikin bayinka. 12 Amma saboda Dawuda mahaifinka, ba zan yi haka a zamaninka ba. Zan yage ta daga hannun ɗanka. 13 Amma ba zan yage dukan masarautar daga gare shi ba, zan ba shi kabila ɗaya saboda Dawuda bawana, da kuma saboda Urushalima, wadda na zaɓa.”
Abokan gāban Solomon
14 Sai Ubangiji ya tayar wa Solomon wani abokin gāba, mai suna Hadad, mutumin Edom daga gidan sarautar Edom. 15 A shekarun baya Dawuda ya ci Edom da yaƙi. Yowab, shugaban sojojinsa ya tafi can domin yă binne Isra’ilawa waɗanda suka mutu a yaƙi. Sa’ad da suke a can, sojojin Isra’ila suka kashe kowane ɗa namiji a Edom. 16 Yowab da dukan Isra’ilawa suka zauna a can, wata shida, sai da suka hallaka dukan mutane a Edom. 17 Amma Hadad yana ɗan yaro a lokaci, wanda ya gudu zuwa Masar tare da shugabannin mutanen Edom waɗanda suka yi wa mahaifinsa hidima. 18 Suka taso daga Midiyan suka tafi Faran. Sa’an nan suka ɗauki mutane daga Faran suka tafi Masar, zuwa wurin Fir’auna wanda ya ba wa Hadad gida da ƙasa, ya kuma tanada masa da abinci.
19 Fir’auna ya ji daɗin Hadad har ya ba shi ’yar’uwar matarsa, Sarauniya Tafenes, aure. 20 ’Yar’uwar Tafenes ta haifi masa ɗa wanda ya kira Genubat, wanda Tafenes ta yi renonsa a fadan sarki. A can, Genubat ya yi zama da ’ya’yan Fir’auna.
21 Yayinda yake a Masar, Hadad ya ji Dawuda ya huta tare da kakanninsa, ya kuma ji cewa Yowab shugaban mayaƙa ya mutu. Sai Hadad ya ce wa Fir’auna, “Bari in tafi, don in koma ƙasata.”
22 Fir’auna ya tambaye shi, ya ce, “Me ka rasa a nan da kake so ka koma garinka?”
Ya ce, “Ba kome, amma ka dai bar ni in tafi!”
23 Allah kuwa ya tayar wa Solomon wani abokin gāba, mai suna Rezon, ɗan Eliyada, wanda ya gudu daga maigidansa, Hadadezer sarkin Zoba. 24 Rezon ya tattara mutane kewaye da shi, ya zama kuma shugaban ’yan tawaye sa’ad da Dawuda ya hallaka mayaƙan Zoba; ’yan tawayen suka tafi Damaskus, inda suka zauna, suka kuma yi mulki. 25 Rezon ya zama babban abokin gāban Isra’ila cikin dukan kwanakin mulkin Solomon. Ya ƙara rikici a kan rikicin Hadad. Rezon ya ƙi mulkin Isra’ila da dukan ransa. Saboda haka Rezon ya yi mulki a Aram ya kuma ƙi jinin Isra’ila.
Yerobowam ya yi wa Solomon tawaye
26 Haka ma Yerobowam, ɗan Nebat, shi ma ya yi wa sarki tawaye. Shi ɗaya ne daga shugabannin Solomon, shi mutumin Efraim ne daga Zereda, mahaifiyarsa kuwa gwauruwa ce, mai suna Zeruwa.
27 Ga yadda ya tayar wa sarki Solomon. Sarki Solomon ya gina madogaran gini†Ko kuwa Millo, ya ciccika wurare a katangar birnin Dawuda mahaifinsa da ƙasa. 28 To, Yerobowam mutum ne mai fasaha. Sa’ad da Solomon ya ga yadda matashin yake aiki da himma, sai ya sa shi yă lura da dukan aikin gandu na gidan Yusuf.
29 Da Yerobowam ya fita Urushalima, sai annabi Ahiya, mutumin Shilo ya tarar da shi a hanya. Lokacin kuwa Ahiya yana saye da sabuwar riga, ba kowa a filin sai su biyu kaɗai. 30 Sai Ahiya ya kama sabuwar rigar da yake saye da ita ya yage ta gida goma sha biyu. 31 Sa’an nan ya ce wa Yerobowam, “Ɗauki gida goma wa kanka, gama abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce ke nan, ‘Duba, zan yage masarauta daga hannun Solomon in ba ka kabilu goma. 32 Amma saboda bawana Dawuda da kuma birnin Urushalima, wadda na zaɓa daga dukan kabilan Isra’ila, zai sami kabila guda. 33 Zan yi wannan domin sun yashe ni, suka kuma yi wa Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Kemosh, allahn Mowabawa, da kuma Molek, allahn Ammonawa sujada, ba su yi tafiya a hanyoyina ba, ba su kuwa yi abin da yake daidai a idanuna ba, ba su kiyaye farillaina da dokokina kamar yadda Dawuda, mahaifin Solomon ya yi ba.
34 “ ‘Amma ba zan ɗauki dukan masarautar daga hannun Solomon ba; na naɗa shi sarki, dukan kwanaki ransa saboda Dawuda bawana, wanda na zaɓa, wanda kuma ya kiyaye umarnai da farillaina. 35 Zan ɗauke masarautar daga hannuwan ɗansa ne, in ba ka kabilu goma. 36 Zan ba da ɗaya ga ɗansa don kullum Dawuda bawana yă kasance da fitila a gabana a Urushalima, birnin da na zaɓa in sa Sunana. 37 Amma fa, ga kai, zan ɗauke ka, za ka kuwa yi mulki bisa dukan abin da zuciyarka take so; za ka zama sarki a bisa Isra’ila. 38 In ka aikata dukan abin da na umarce ka, ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi abin da yake daidai a idanuna ta wurin kiyaye farillaina da umarnaina, kamar yadda Dawuda bawana ya yi, zan kasance tare da kai. Zan gina maka masarauta mai dawwama kamar wadda na gina wa Dawuda, zan kuma ba da Isra’ila gare ka. 39 Zan ƙasƙantar da zuriyar Dawuda saboda wannan, amma ba har abada ba.’ ”
40 Solomon ya yi ƙoƙari yă kashe Yerobowam, amma Yerobowam ya tsere zuwa Masar, zuwa wurin sarki Shishak, ya zauna a can sai bayan mutuwar Solomon.
Mutuwar Solomon
(2 Tarihi 9.29-31)
41 Game da sauran ayyukan mulkin Solomon, da dukan abubuwan da ya yi, da hikimar da ya nuna, an rubuta su a littafin tarihin Solomon. 42 Solomon ya yi mulki a Urushalima, a bisa dukan Isra’ila, shekaru arba’in. 43 Sa’an nan ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a birnin Dawuda mahaifinsa. Sai Rehobowam ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.