4
Duk sa’ad da Sama’ila ya yi magana dukan Isra’ila sukan saurare shi.
Filistiyawa sun kama akwatin alkawari
Isra’ilawa suka fita yaƙi da Filistiyawa. Isra’ilawa suka kafa sansani a Ebenezer*Ebenezer wato, dutsen taimako, Filistiyawa kuma a Afek. Filistiyawa suka tunƙuro mayaƙansu domin su sadu da Isra’ilawa, yaƙi kuwa ya yi tsanani har Isra’ilawa suka sha kashi a hannun Filistiyawa. Filistiyawa suka kashe Isra’ilawa kusan mutum dubu huɗu a bakin dāgā. Lokacin da mayaƙan suka komo sansani, dattawan Isra’ilawa suka yi tambaya suka ce, “Me ya sa Ubangiji ya sa muka sha ɗibga a hannun Filistiyawa? Bari mu kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Shilo. Domin yă tafi tare da mu yă ba mu nasara kan abokan gābanmu.”
Saboda haka mutanen suka aika waɗansu maza zuwa Shilo, suka kuwa tafi suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji Maɗaukaki wanda yake zaune tsakanin Kerubobi. ’Ya’yan Eli biyun nan Hofni da Finehas suna wurin tare da akwatin alkawarin Ubangiji.
Da aka shigo da akwatin alkawarin Ubangiji a cikin sansani, sai Isra’ilawa suka tā da babbar murya har ƙasa ta jijjiga. Da jin wannan, Filistiyawa suka yi tambaya suka ce, “Me ke kawo wannan ihu mai ƙarfi haka a sansanin Isra’ilawa?”
Da suka gane cewa akwatin alkawarin Ubangiji ne ya shiga sansanin, sai Filistiyawa suka ji tsoro, suka ce, “Wani allah ya shiga cikin sansanin. Mun shiga uku! Ba a taɓa yin wani abu haka ba. Kaiton mu! Wa zai kuɓutar da mu daga hannun waɗannan manyan alloli? Su ne allolin da suka buga Masarawa da irin annoba masu yawa a jeji. Ku yi ƙarfin hali, ku yi mazantaka, ku Filistiyawa, domin kada ku zama bayin Ibraniyawa kamar yadda suke a gare ku. Ku yi mazantaka, ku yi yaƙi.”
10 Saboda haka Filistiyawa suka yi yaƙi, Isra’ilawa kuwa suka sha ɗibga, kowane mutum kuwa ya gudu zuwa tentinsa. Kisan kuwa ya yi muni ƙwarai. Isra’ilawa sun rasa mayaƙa dubu talatin. 11 Aka ƙwace akwatin alkawarin Ubangiji. Aka kuma kashe ’ya’yan Eli biyu, Hofni da Finehas.
Mutuwar Eli
12 A wannan rana wani mutumin Benyamin ya ruga da bakin dāgā ya shigo Shilo, taguwarsa a yage, kansa kuma a rufe da ƙasa. 13 Da ya iso sai ga Eli zaune a kujera kusa da hanya yana kallo, domin tsoron da yake da shi saboda akwatin alkawarin Allah. Da mutumin ya shigo a garin ya ba da labarin abin da ya faru sai dukan gari ya ruɗe da ihu.
14 Eli ya ji ihun ya yi tambaya ya ce, mene ne dalilin wannan ihu?
Mutumin ya rugo wurin Eli, 15 wanda yake da shekaru tasa’in da takwas da haihuwa, idanunsa kuma ƙarfi ya ƙare, baya iya gani.
16 Mutumin ya gaya wa Eli cewa, “Shigowata ke nan daga bakin dāgā. Na kuɓuce daga can yau ɗin nan.”
Eli ya ce, “Me ya faru da ’ya’yana?”
17 Mutumin da ya kawo labarin ya ce, “Isra’ilawa sun gudu a gaban Filistiyawa, mayaƙan kuma sun sha mummunar ɗibga. ’Ya’yanka Hofni da Finehas su ma sun mutu. Aka kuma ƙwace akwatin alkawarin Allah.”
18 Da ya ambaci akwatin alkawarin Allah, sai Eli ya fāɗi da baya daga kujeransa kusa da ƙofa, wuyarsa ta karye, ya kuma mutu domin ya tsufa ƙwarai. Ya yi shugabancin Isra’ila shekaru arba’in.
19 Matar Finehas, ɗansa tana da ciki a lokacin ta kuma kusa haihuwa. Sa’ad da ta ji labari cewa an ƙwace akwatin alkawarin Allah, ta kuma labarin surukinta da mijinta sun mutu, sai ta shiga naƙuda, ta kuma haihu. Amma naƙuda ta sha ƙarfinta. 20 Da tana mutuwa, matan da suke lura da ita suka ce, “Kada ki karaya kin haifi ɗa namiji.” Amma ba tă ba da amsa ko tă kula ba.
21 Ta ba wa yaron suna Ikabod, ma’ana “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila”, domin an ƙwace akwatin alkawarin Allah, domin kuma mutuwar surukinta da na mijinta. 22 Ta ce, “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila, gama an ƙwace akwatin alkawarin Allah.”

*4:1 Ebenezer wato, dutsen taimako