11
Shawulu ya ceci birnin Yabesh
1 Nahash mutumin Ammon ya haura ya kewaye Yabesh Gileyad da yaƙi. Dukan mutanen Yabesh suka ce masa, “Ka ƙulla amana da mu, mu kuwa za mu bauta maka.”
2 Amma Nahash ya ce, “Zan ƙulla amana da ku kawai a kan sharaɗin cewa zan ƙwaƙulo idon dama na kowannenku, ta haka za a kunyata Isra’ila.”
3 Dattawan Yabesh suka ce masa, “Ka ba mu kwana bakwai don mu aika manzanni a dukan ƙasar Isra’ila idan ba mu sami wanda zai cece mu ba, za mu ba da kanmu gare ka.”
4 Da manzannin suka zo Gibeya garin Shawulu, suka gaya wa mutane wannan sharaɗin, suka yi kuka mai zafi. 5 A daidai wannan lokacin kuwa Shawulu yana dawowa daga gona tare da shanunsa na noma, sai ya ce, “Me ya faru, mutane suna kuka haka?” Sai suka faɗa masa abin da mutanen Yabesh suka faɗa musu.
6 Da Shawulu ya ji, sa Ruhun Allah ya sauko a kansa da iko, ya husata ƙwarai. 7 Ya ɗauki shanu biyu, ya yayyanka su gunduwa-gunduwa, ya aika da su ko’ina a ƙasar Isra’ila ta wurin manzanni cewa, “Duk wanda bai fita ya bi Shawulu da Sama’ila ba, haka za a yi da shanunsa.” Mutanen suka ji tsoron Ubangiji suka fita gaba ɗaya kamar mutum guda. 8 Mutanen Isra’ila sun kai dubu ɗari uku. Mutanen Yahuda kuma dubu talatin, sa’ad da Shawulu ya tara su a Bezek.
9 Suka ce wa ’yan aikan da suka zo, “Ku faɗa wa mutanen Yabesh Gileyad, ‘Gobe, kafin rana tă yi zafi, za ku sami ceto.’ ” Sa’ad da ’yan aikan suka tafi, suka ba da saƙon nan ga mutanen Yabesh, sai suka farin ciki. 10 Suka ce wa Ammonawa, “Gobe za mu miƙa wuya gare ku, ku kuma yi duk abin da kuka ga dama.”
11 Gari yana wayewa, sai Shawulu ya raba mutane kashi uku, a sa’a ta ƙarshe na daren sai suka fāɗa wa sansanin Ammonawa, suka kuma karkashe su har lokacin da rana ta yi zafi. Waɗanda suka kuɓuce kuwa suka warwatsu, har babu biyunsu da aka bari tare.
An tabbatar da Shawulu sarki
12 Sai mutane suka ce wa Sama’ila, “Su wa suka ce, ‘Shawulu zai yi mulkinmu?’ A kawo mana su mu kashe.”
13 Shawulu ya ce, “Ba wanda zai mutu yau, gama Ubangiji ya kuɓutar da Isra’ila a wannan rana.”
14 Sai Sama’ila ya ce wa mutane, “Ku zo mu tafi Gilgal, a can za a yi wankan sarauta.” 15 Don haka dukan mutane suka tafi Gilgal, suka tabbatar da Shawulu sarki a gaban Ubangiji. A can suka miƙa hadaya ta salama a gaban Ubangiji, Shawulu kuwa da dukan Isra’ila suka yi babban liyafa.