15
Ubangiji ya ƙi Shawulu a matsayin sarki
Sama’ila ya ce wa Shawulu, “Ni ne wanda Ubangiji ya aika in shafe ka ka zama sarki bisa mutanensa Isra’ila. Saurara yanzu ka ji saƙo daga wurin Ubangiji. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Zan hori Amalekawa saboda abin da suka yi wa Isra’ila sa’ad da suka ba su wahala yayinda suka fito daga Masar. Yanzu ka tafi ka yaƙi Amalekawa, ka hallaka kome da yake nasu, kada ka bar su da rai, ka kashe maza, da mata, da yara, da jarirai, da dabbobi, da tumaki, da raƙuma, da kuma jakuna.’ ”
Sai Shawulu ya tattara sojoji, ya ƙidaya su a Telayim, ya sami su dubu ɗari biyu da dubu goma daga Yahuda. Shawulu ya tafi birnin Amalek ya yi kwanto a kwari. Sai Shawulu ya ce wa Keniyawa, “Ku tashi ku bar Amalekawa don kada in hallaka ku tare da su, saboda kun yi wa dukan Isra’ilawa kirki, lokacin da suka fito daga Masar.” Saboda haka Keniyawa suka tashi suka bar Amalekawa.
Sa’an nan Shawulu ya ci Amalekawa da yaƙi tun daga Hawila har zuwa Shur, a gabashin iyakar Masar. Ya kama Agag sarkin Amalekawa da rai. Ya kuma hallaka dukan mutanensa da takobi. Amma Shawulu da sojojinsa suka bar Agag, da tumaki, da shanu, da ’yan maruƙa masu ƙiba da kuma duk abin da yake mai kyau da rai. Waɗannan ba su so su hallaka su gaba ɗaya ba, amma duk abin da ba a so da kuma marar amfani suka hallaka.
10 Sai Ubangiji ya yi magana da Sama’ila ya ce, 11 “Na damu da na naɗa Shawulu sarki, domin ya juya mini baya, bai kuma bi umarnina ba.” Sama’ila ya damu ƙwarai, ya yi kuka ga Ubangiji dukan dare.
12 Kashegari da sassafe sai Sama’ila ya tashi ya tafi domin yă sadu da Shawulu, amma aka gaya masa cewa Shawulu ya tafi Karmel. A can ya yi wa kansa abin tunawa don yă girmama kansa, daga can kuma ya juya ya gangara zuwa Gilgal.
13 Da Sama’ila ya kai wurinsa, sai Shawulu ya ce, “Ubangiji yă albarkace ka, na aikata umarnin Ubangiji.”
14 Amma Sama’ila ya ce, “Ashe, waɗannan ba kukan tumaki ke nan nake ji a kunnena ba? Wane kuka shanu ke nan nake ji?”
15 Shawulu ya amsa ya ce, “Sojoji ne suka kawo su daga Amalekawa. Sun bar tumaki da shanu masu kyau da rai don su yi wa Ubangiji Allahnka hadaya, amma sauran mun hallaka duka.”
16 Sama’ila ya ce, “Dakata, bari in faɗa maka abin da Ubangiji ya ce mini jiya da dare.”
Shawulu ya ce, “Gaya mini.”
17 Sama’ila ya ce, “Ko da yake kana ganin kanka kai ba wani abu ne ba, ashe, ba kai ne yanzu shugaban kabilan Isra’ila ba? Ubangiji ya shafe ka ka zama sarkin Isra’ila. 18 Shi kuma ya aika, ya umarce ka cewa, ‘Tafi ka hallaka Amalekawa mugayen mutanen nan duka, ka yaƙe su sai ka share su ƙaf.’ 19 Me ya sa ba ka bi umarnin Ubangiji ba? Me ya sa ka sa hannu a ganima, ka kuma yi mugun abu a gaban Ubangiji?”
20 Shawulu ya ce, “Amma na bi umarnin Ubangiji. Na bi saƙon da Ubangiji ya ba ni. Na hallaka Amalekawa, na kuma kamo Agag sarkinsu. 21 Sojoji suka kawo tumaki da shanu mafi kyau daga cikin ganimar domin a miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnka a Gilgal.”
22 Amma Sama’ila ya ce,
Ubangiji yana murna da sadaka da hadaya
fiye da biyayya ga maganar Ubangiji?
Yin biyayya ta fi hadaya
a kula kuma ta fi ƙibabbun raguna.
23 Gama tawaye yana kama da zunubi na duba,
girman kai kuma yana kama da bautar gumaka.
Saboda ka ƙi maganar Ubangiji,
shi ma ya ƙi ka da zaman sarki.”
24 Sai Shawulu ya ce wa Sama’ila, “Na yi zunubi, na ƙi bin umarnin Ubangiji, na kuma ƙi bin maganarka. Na ji tsoron mutane ne shi ya sa na bi maganarsu. 25 Yanzu fa, ina roƙonka ka yafe mini zunubina, ka koma tare da ni, domin in yi wa Ubangiji sujada.”
26 Amma Sama’ila ya ce, “Ba zan koma tare da kai ba. Ka ƙi maganar Ubangiji, Ubangiji kuma ya ƙi ka da zama sarki a bisa Isra’ila.”
27 Da Sama’ila ya juya zai tafi, sai Shawulu ya kama bakin rigarsa, sai rigar ta yage. 28 Sama’ila ya ce masa, “Ubangiji ya yage masarautar Isra’ila daga gare ka yau, ya ba wa wani daga cikin maƙwabtanka wanda ya fi ka. 29 Shi wanda yake Ɗaukakar Isra’ila ba ya ƙarya ko yă canja zuciyarsa, gama shi ba mutum ba ne da zai canja zuciyarsa.”
30 Shawulu ya ce, “Na yi zunubi. Amma ina roƙonka ka ba ni girma a gaban dattawan mutanena da kuma a gaban Isra’ila, ka koma tare da ni domin in yi wa Ubangiji Allahnka sujada.” 31 Saboda haka sai Sama’ila ya koma tare da Shawulu, Shawulu kuwa ya yi wa Ubangiji sujada.
32 Sa’an nan Sama’ila ya ce, “Kawo mini Agag sarkin Amalekawa.”
Agag kuwa ya zo wurinsa daure da sarƙa,*Ko kuwa yana rawar jiki, duk da haka yana tunani cewa, “Tabbatacce zancen mutuwa dai ya wuce.”
33 Amma Sama’ila ya ce,
“Yadda takobinka ya sa mata suka rasa ’ya’ya,
haka mahaifiyarka za tă zama marar ’ya’ya a cikin mata.”
Sama’ila kuwa ya kashe Agag a Gilgal a gaban Ubangiji.
34 Sai Sama’ila ya tafi Rama, amma Shawulu ya haura zuwa gidansa a Gibeya na Shawulu. 35 Daga wannan rana Sama’ila bai ƙara saduwa da sarki Shawulu ba, har rasuwar Sama’ila, amma ya yi baƙin ciki sosai a kan Shawulu. Ubangiji kuwa ya damu da ya sa Shawulu ya zama Sarkin Isra’ila ba.

*15:32 Ko kuwa yana rawar jiki, duk da haka