3
1 Saboda haka da muka kāsa daurewa, sai muka ga ya fi kyau a bar mu a Atens mu kaɗai. 2 Muka aiki Timoti, wanda yake ɗan’uwanmu da kuma abokin aikin Allah a cikin yaɗa bisharar Kiristi, don yă gina ku yă kuma ƙarfafa ku cikin bangaskiyarku, 3 don kada kowa yă raunana ta wurin waɗannan gwaje-gwajen. Kun sani sarai cewa an ƙaddara mu don waɗannan. 4 Gaskiyar ita ce, sa’ad da muke tare da ku, mun sha gaya muku cewa za a tsananta mana. Haka kuwa ya faru, kamar dai yadda kuka sani. 5 Saboda wannan, sa’ad da ban iya jimrewa ba, sai na aika domin in sami labarin bangaskiyarku, da fata kada yă zama mai jarraban nan ya riga ya jarrabce ku, ƙoƙarinmu kuma yă zama banza.
Rahoton mai ƙarfafawa na Timoti
6 Amma ga shi yanzu Timoti ya dawo mana daga wurinku ya kuma kawo labari mai daɗi game da bangaskiyarku da kuma ƙaunarku. Ya faɗa mana yadda kullum kuke da tunani mai kyau a kanmu, yadda kuke marmari ku gan mu, kamar dai yadda mu ma muke marmari mu gan ku. 7 Saboda haka ’yan’uwa, cikin dukan damuwarmu da tsananinmu an ƙarfafa mu game da ku saboda bangaskiyarku. 8 Gama yanzu tabbatacce muna da rai, da yake kuna nan tsaye daram a cikin Ubangiji. 9 Wace irin godiya ce za mu yi wa Allah saboda ku a kan dukan farin cikin da muke da shi a gaban Allahnmu ta dalilinku? 10 Dare da rana muna addu’a da himma domin mu sāke ganinku, mu kuma ba ku abin da kuka rasa a bangaskiyarku.
11 Yanzu bari Allahnmu da Ubanmu kansa da kuma Ubangijinmu Yesu yă shirya mana hanya mu zo wurinku. 12 Ubangiji yă sa ƙaunarku ta ƙaru ta kuma yalwata ga juna da kuma ga kowa, kamar yadda tamu take muku. 13 Bari yă ƙarfafa zukatanku har ku zama marasa aibi da kuma tsarkaka a gaban Allahnmu da Ubanmu sa’ad da Ubangijimmu Yesu ya dawo tare da dukan tsarkakansa.