1 Timoti
1
Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu da kuma na Yesu Kiristi begenmu,
 
Zuwa ga Timoti ɗana na gaske cikin bangaskiya.
 
Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai.
 
Gargaɗi game da malaman ƙarya
Kamar yadda na gargaɗe ka sa’ad da zan je Makidoniya, ka zauna can Afisa domin ka umarci waɗansu mutane kada su koyar da ƙa’idodin ƙarya nan gaba ko su ba da kansu ga tatsuniyoyi da ƙididdigar asali marar iyaka. Waɗannan suna kawo faɗa a maimakon aikin Allah wanda yake ta wurin bangaskiya. Maƙasudin wannan umarnin dai ƙauna ce, wadda take zuwa daga zuciya mai tsabta da lamiri mai kyau da kuma sahihiyar bangaskiya. Waɗansu sun bauɗe daga waɗannan al’amura, suka koma ga maganganu marasa ma’ana. So suke su zama malaman doka, ba tare da fahimtar abin da suke faɗa ba, balle abubuwan da suke ta nacewa a kai.
Mun san cewa doka tana da kyau in an yi amfani da ita yadda ya kamata. Mun kuma san cewa an yi doka ba domin masu adalci ba sai dai masu tawaye, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai, 10 da masu zina da kuma da maza masu kwana da maza, ko mata masu kwana da mata, da masu cinikin bayi da masu ƙarya da kuma masu shaidar ƙarya, da kuma duk wani abin da ya saɓa wa sahihiyar koyarwa, 11 da take bisa ga bishara mai ɗaukaka ta Allah mai albarka, wadda ya danƙa mini.
Alherin Ubangiji ga Bulus
12 Na gode wa Kiristi Yesu Ubangijinmu, wanda ya ba ni ƙarfi, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa. 13 Ko da yake a dā ni mai saɓo da mai tsanantawa da kuma mai rikici ne, aka nuna mini jinƙai saboda na yi haka cikin jahilci ne da kuma rashin bangaskiya. 14 An zubo mini alherin Ubangijinmu a yalwace, tare da bangaskiya da ƙaunar da take cikin Kiristi Yesu.
15 Ga wata magana tabbatacciya wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa. Kiristi Yesu ya zo duniya domin ceton masu zunubi, wanda nake mafi muni a cikinsu. 16 Amma saboda wannan dalilin ne aka nuna mini jinƙai domin ta wurina, mafi zunubi duka, Kiristi Yesu yă iya bayyana matuƙar haƙurinsa a matsayin misali ga waɗanda za su gaskata shi su kuma sami rai madawwami. 17 Bari girma da ɗaukaka su tabbata har abada abadin ga Sarki madawwami, wanda ba ya mutuwa, wanda ba a ganinsa, wanda kuma shi ne kaɗai Allah! Amin.
18 Timoti, ɗana, na ba ka wannan umarni bisa ga annabce-annabcen da aka yi a dā game da kai, domin ta wurin binsu ka iya yin yaƙi mai kyau, 19 kana riƙe da bangaskiya da kuma lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunne ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu. 20 Cikinsu kuwa akwai Himenayus da Alekzanda, waɗanda na miƙa ga Shaiɗan don su horo su bar yin saɓo.