5
Shawara game da gwauraye, dattawa da kuma bayi
Kada ka tsawata wa dattijo, sai dai ka gargaɗe shi a matsayinka. Ka ɗauki samari a matsayin ’yan’uwanka, tsofaffin mata kuwa sai ka ce uwaye, ’yan mata kuma a matsayin ’yan’uwa da matuƙar tsarki.
Ka girmama gwauraye waɗanda suke cikin bukata ta ainihi. Amma in gwauruwa tana da ’ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah. Gwauruwa wadda ba ta da kowa da zai taimake ta, za tă sa zuciyarta ga Allah, tana roƙo da addu’o’i dare da rana gare shi don taimako. Amma gwauruwar da take zaman jin daɗi, matacciya ce tun tana da rai. Ka umarce su game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi. In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.
Kada a lasafta gwauruwa cikin jerin gwauraye sai ta wuce shekara sittin, ta kuma yi zaman aminci ga mijinta,* Ko kuwa ta auri miji guda kawai 10 aka kuma santa sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon ’ya’ya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau.
11 Game da gwauraye masu ƙuruciya kuwa, kada ka sa su cikin wannan lissafi. Gama sa’ad da sha’awar jikinsu ta kāsa daurewa game da wa’adin da suka yi da Kiristi, sai su so yin aure. 12 Ta haka suna jawo wa kansu hukunci, saboda sun karya alkawarinsu na farko. 13 Ban da haka, sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida-gida. Ba kawai sun zama masu zaman banza ba, har ma sun zama masu gulma da masu shisshigi, suna faɗin abubuwan da bai kamata su faɗa ba. 14 Saboda haka ina ba wa gwauraye masu ƙuruciya shawara su yi aure, su sami ’ya’ya, su lura da gidajensu kada kuwa su ba abokin gāba zarafin ɓata suna. 15 Waɗansu dai sun riga sun bauɗe sun bi Shaiɗan.
16 In mace mai bi tana da gwauraye a iyalinta, ya kamata tă taimake su, kada tă bar wa ikkilisiya wannan nauyi, domin ikkilisiya ta sami zarafin taimakon gwaurayen da suke da bukata ta ainihi.
17 Dattawan da suka bi da al’amuran ikkilisiya da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman waɗanda aikinsu wa’azi ne da kuma koyarwa. 18 Gama Nassi ya ce, “Kada ka sa wa bijimi takunkumi yayinda yake sussukar hatsi,” M Sh 25.4 da kuma, “Ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.” Luk 10.7 19 Kada ka saurari ƙara game da dattijo sai da shaidu biyu ko uku. 20 Amman waɗannan dattawa waɗanda suke yin zunubi kuwa sai ka kwaɓe su a gaban jama’a, don saura su ji tsoro. 21 Na gama ka da Allah, da Kiristi Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala’iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka nuna bambanci.
22 Kada ka yi garajen ɗibiya hannuwa, kada kuma ka yi tarayya a cikin zunuban waɗansu. Ka kiyaye kanka da tsarki.
23 Ka daina shan ruwa kaɗai, yi amfani da ruwan inabi kaɗan saboda cikinka da kuma yawan rashin lafiyarka.
24 Zunuban waɗansu mutane a fili suke, suna shan gabansu zuwa hukunci; zunuban waɗansu kuwa sukan bi su a baya. 25 Haka ma ayyuka nagari a fili suke, ko ba ma a fili suke ba, ba a iya ɓoye su.

*5:9 Ko kuwa ta auri miji guda kawai

5:18 M Sh 25.4

5:18 Luk 10.7