15
Azariya sarkin Yahuda
(2 Tarihi 26.1-23)
1 A shekara ta ashirin da bakwai ta mulkin Yerobowam sarkin Isra’ila, Azariya ɗan Amaziya, sarkin Yahuda ya fara mulki. 2 Yana da shekara goma sha shida sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyu. Sunan mahaifiyarsa Yekoliya daga Urushalima. 3 Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, yadda mahaifinsa Amaziya ya yi. 4 Amma bai kawar da masujadan kan tudu ba; mutane kuwa suka yi ta yin hadaya da ƙona turare a can.
5 Ubangiji ya sa wa sarki ciwon kuturta har mutuwarsa, ya kuma zauna a keɓe.*Ko kuwa a gidan da aka fisshe shi daga ɗauka ɗawainiya Yotam ɗan sarki, shi ne ya gudanar da sha’anin fada, ya kuma shugabanci mutanen ƙasar.
6 Game da sauran ayyukan mulkin Azariya, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. 7 Azariya ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi kusa da su a Birnin Dawuda. Yotam ɗansa, kuma ya gāje shi.
Zakariya sarkin Isra’ila
8 A shekara ta talatin da takwas ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Zakariya ɗan Yerobowam ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki wata shida. 9 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa ya yi. Bai bar aikata zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila suka yi ba.
10 Sai Shallum ɗan Yabesh ya ƙulla wa Zakariya maƙarƙashiya. Ya tasam masa a gaban jama’a,†Da Ibraniyanci; waɗansu rubuce-rubucen hannu na Seftuwajin suna da in Ibileyam ya kashe shi, ya kuma gāje shi. 11 Game da sauran ayyukan mulkin Zakariya, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. 12 Ta haka maganar Ubangiji da ya yi wa Yehu ta cika, wadda ya ce, “Zuriyarka za tă zauna a kursiyin Isra’ila har tsara ta huɗu.”‡2Sar 10.30.
Shallum sarkin Isra’ila
13 Shallum ɗan Yabesh ya zama sarki a shekara ta talatin da tara ta mulkin Uzziya sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki na wata ɗaya a Samariya. 14 Sa’an nan Menahem ɗan Gadi ya gangara daga Tirza ya haura zuwa Samariya. Ya tasam wa Shallum ɗan Yabesh a Samariya, ya kashe shi, ya kuma gāje shi.
15 Game da sauran ayyukan mulkin Shallum, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
16 A lokacin nan sai Menahem ya taso daga Tirza, ya kai wa Tifsa hari da kowa wanda yake a birnin da kewayenta, don sun ƙi su buɗe ƙofofinsu. Ya kori Tifsa daga aiki, ya kuma tsattsaga cikin dukan mata masu juna biyu.
Menahem sarkin Isra’ila
17 A shekara ta talatin da takwas ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Menahem ɗan Gadi ya zama sarkin Isra’ila, ya yi mulki a Samariya shekara goma. 18 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. A duk tsawon mulkinsa, bai rabu da zunuban da Yerobowam ɗan Nebat ya sa Isra’ila suka aikata ba.
19 Sai Ful§Wanda kuma ake kira Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya kai wa ƙasar hari, Menahem kuwa ya ba shi talenti dubu na azurfa don yă sami goyon bayansa, yă kuma ƙarfafa kahuwa mulkin. 20 Menahem ya tara kuɗin ne ta hanyar haraji a Isra’ila inda ya sa kowane attajiri ya ba da shekel hamsin don a ba sarkin Assuriya. Sa’an nan sarkin Assuriya ya janye, bai ƙara kasance a ƙasar ba.
21 Game da sauran ayyukan mulkin Menahem, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. 22 Menahem ya huta tare da kakanninsa. Fekahiya ɗansa kuma ya gāje shi.
Fekahiya sarkin Isra’ila
23 A shekara ta hamsin ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Fekahiya ɗan Menahem ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki shekara biyu. 24 Fekahiya ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat wanda ya sa Isra’ila ya aikata ba. 25 Ɗaya daga cikin manyan fadawansa, Feka ɗan Remaliya, ya ƙulla masa maƙarƙashiya. Ɗauke da mutanen Gileyad hamsin, ya kashe Fekahiya tare da Argob da kuma Ariye a fadan sarki a Samariya. Ta haka Feka ya kashe Fekahiya ya kuma gāje shi.
26 Game da sauran ayyukan mulkin Fekahiya, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
Feka sarkin Isra’ila
27 A shekara ta hamsin da biyu ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Feka ɗan Remaliya ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya yi mulki shekara ashirin. 28 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai kauce wa zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta yi ba.
29 A zamanin Feka sarkin Isra’ila, Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya zo ya kama Iyon, Abel-Bet-Ma’aka, Yanowa da Kedesh da kuma Hazor. Ya kame Gileyad da Galili, haɗe da dukan ƙasar Naftali, ya kuma kwashi mutanen zuwa Assuriya. 30 Sa’an nan Hosheya ɗan Ela ya ƙulla wa Feka ɗan Remaliya maƙarƙashiya. Ya fāɗa masa ya kuma kashe shi, sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki a shekara ta shirin ta mulkin Yotam ɗan Uzziya.
31 Game da sauran ayyukan mulkin Feka da duk abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
Yotam sarkin Yahuda
(2 Tarihi 27.1-9)
32 A shekara ta biyu ta mulkin Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila, Yotam ɗan Uzziya sarkin Yahuda ya fara mulki. 33 Ya zama sarki yana da shekara ashirin da biyar, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Sunan mahaifiyarsa Yerusha, ’yar Zadok. 34 Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa Uzziya ya yi. 35 Duk da haka, bai kawar da masujadan kan tudu ba; mutane suka ci gaba da yin hadaya da ƙona turare a can. Yotam ya sāke gina Ƙofar Bisa ta haikalin Ubangiji.
36 Game da sauran ayyukan mulkin Yotam da aikin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. 37 (A kwanakin nan Ubangiji ya fara aikan Rezin sarkin Aram da Feka ɗan Remaliya, su yi gāba da Yahuda.) 38 Yotam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda, birnin mahaifinsa. Ahaz ɗansa kuma ya gāje shi.