19
An yi annabcin ceton Urushalima
(Ishaya 37.1-13)
Da sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakketa tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya shiga haikalin Ubangiji. Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna marubuci da shugabannin firistoci, dukansu sanye da tufafin makoki, zuwa wurin annabi Ishaya ɗan Amoz. Suka ce masa, “Hezekiya ya ce, yau ranar wahala ce, da ta cin mutunci, da ta shan kunya, ga shi, ’ya’ya suna gab da a haife su, amma ba ƙarfin da za a yi yunƙuri a haife su. Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka ya ji dukan maganganun sarkin yaƙi, wanda maigidansa, sarkin Assuriya, ya aiko don yă rena Allah mai rai. Bari Ubangiji Allahnka yă tsawata masa saboda maganar da ya ji. Saboda haka ka yi addu’a domin raguwar da har yanzu suke a raye.”
Da fadawan sarki Hezekiya suka isa wurin Ishaya, Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku, in ji Ubangiji, ‘Kada abin da ka ji yă firgita ka, wato, waɗannan kalmomin da karen nan na sarkin Assuriya ya yi saɓo da su. Saurara! Zan sa masa wani ruhun da zai sa yă ji wata jita-jitar da za tă sa yă koma ƙasarsa. A can zan sa a kashe shi da takobi a ƙasarsa.’ ”
Da sarkin yaƙin ya ji cewa sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye, ya kuma iske sarkin yana yaƙi da Libna.
To, Sennakerib ya sami labari cewa Tirhaka, mutumin Kush*Wato, daga yanki bisa Nilu sarkin Masar, yana zuwa masa da yaƙi. Saboda haka ya sāke aika manzanni zuwa wurin Hezekiya cewa, 10 “Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda, kada ka bar allahn da kake dogara gare shi yă ruɗe ka cewa, ‘Urushalima ba za tă fāɗi a hannun sarkin Assuriya ba.’ 11 Ba shakka ka riga ka ji abin da sarkin Assuriya ya yi da dukan ƙasashe, yana hallaka su gaba ɗaya. Kai kuwa kana ji za a cece ka? 12 Allolin al’umman da kakannina suka hallaka, sun cece su ne, allolin Gozan, da na Haran, da na Rezef, da kuma na mutane Eden da suke a Tel Assar? 13 Ina sarkin Hamat, da sarkin Arfad, da sarkin birnin Sefarfayim, ko na Hena da kuma na Iffa?”
Addu’ar Hezekiya
(Ishaya 37.14-20)
14 Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga manzannin ya karanta. Sa’an nan ya tashi ya tafi haikalin Ubangiji ya shimfiɗa wasiƙar a gaban Ubangiji. 15 Hezekiya kuwa ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda yake zaune tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah bisa dukan mulkokin duniya. Kai ka yi sama da duniya. 16 Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka ji; ka buɗe idanunka ya Ubangiji ka gani; ka saurari kalmomin da Sennakerib ya aiko don yă yi wa Allah mai rai ba’a.
17 “Da gaske ne, ya Ubangiji, cewa sarakunan Assuriya sun hallakar da waɗannan al’ummai da ƙasashensu. 18 Sun jefar da allolinsu cikin wuta, suka hallaka su, gama ba alloli ba ne, katakai ne da kuma duwatsu, ayyukan hannuwan mutane. 19 To, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga hannunsa, don dukan mulkokin duniya su san cewa kai kaɗai, ya Ubangiji ne Allah.”
Ishaya ya yi annabcin fāɗuwar Sennakerib
(Ishaya 37.21-35)
20 Sai Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo zuwa wurin Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, na ji addu’arka game da Sennakerib sarkin Assuriya. 21 Ga abin da Ubangiji yana cewa game da shi,
“ ‘Budurwar Sihiyona
ta rena ka tana kuma yin maka ba’a.
Diyar Urushalima
ta kaɗa kanta yayinda kake gudu.
22 Wane ne ka zaga, ka kuma yi masa saɓo?
Wa kake gāba da shi har ka ɗaga muryarka,
har ka tā da idanunka da fahariya?
Kana gāba da Mai Tsarki na Isra’ila!
23 Ta wurin manzanninka
ka tara wa Ubangiji zagi.
Ka kuma ce,
“Da yawa kekunan yaƙina
na haye kan ƙwanƙolin duwatsu,
wurin mafi tsawo na Lebanon.
Na sassare itacen al’ul nasa mafi tsawo
mafi daraja na itacen fir nasa.
Na ratsa har can tsakiyar kurmi,
mafi kyau na kurminsa.
24 Na tona rijiyoyi a ƙasashen waje
na kuma sha ruwa a can.
Da tafin ƙafafuna
na busar da dukan rafuffukan Masar.”
 
25 “ ‘Ba ka taɓa ji ba?
Tun da daɗewa na ƙaddara haka.
Tuntuni kuwa na shirya shi;
yanzu kuma na sa ya faru,
cewa ka mai da birane masu katanga
tarin duwatsu.
26 Ƙarfin mutanensu ya tsiyaye,
suka razana aka kuma kunyata su.
Suna kama da tsirai a gona,
kamar sabon toho
kamar ciyawa mai tohuwa bisa rufin ɗaki
wanda ya bushe saboda zafi, kafin yă yi girma.
 
27 “ ‘Amma na san wurin zamanka
da fitarka da shigarka
da yadda kake fushi da ni.
28 Domin kana fushi da ni
reninka ya iso kunnuwata,
zan sa ƙugiyata a hancinka
da linzamina a bakinka,
zan kuma sa ka koma
a ta hanyar da ka zo.’
29 “Wannan zai zama alama a gare ka, ya Hezekiya,
“Bana, za ku ci amfanin gonar da ya tsira da kansa,
baɗi kuma amfanin gonar da ya tsiro daga na bara.
Amma a shekara ta uku, za ku yi shuki, ku kuma girbe,
ku dasa gonakin inabi, ku kuma ci ’ya’yansa.
30 Sau ɗaya kuma ragowar masarautar Yahuda
za tă yi saiwoyi a ƙasa ta kuma ba da ’ya’ya a bisa.
31 Gama daga Urushalima za a sami ragowa,
daga Dutsen Sihiyona kuma za a sami waɗanda suka tsira.
Himmar Ubangiji Maɗaukaki za tă cika wannan.
 
32 “Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce game da sarkin Assuriya,
“Ba zai shiga birnin nan ba
ko yă harba kibiya a nan.
Ba zai kusace ta da garkuwa
ko yă yi mata zoben yaƙi ba.
33 Ta hanyar da ya zo ne zai koma;
ba zai shiga birnin nan ba, in ji Ubangiji.
34 Zan kāre birnin nan in cece ta,
saboda kaina da kuma bawana Dawuda.”
(Ishaya 37.36-38)
35 A daren nan mala’ikan Ubangiji ya fita ya kashe dakaru dubu ɗari da tamanin da biyu a sansanin Assuriyawa. Da mutane suka farka da safe, sai ga gawawwaki ko’ina. 36 Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya tā da sansanin ya kuma janye. Ya koma Ninebe ya zauna a can.
37 Wata rana yayinda yake sujada a haikalin Nisrok, allahnsa, sai ’ya’yansa maza, Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka gudu zuwa ƙasar Ararat. Sai Esar-Haddon ɗansa ya gāje shi.

*19:9 Wato, daga yanki bisa Nilu