24
1 A zamani Yehohiyakim, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kawo wa ƙasar farmaki, Yehohiyakim dai ya zama abokin tarayyarsa na tsawon shekara uku. Daga baya kuma sai ya canja ra’ayi ya yi wa Nebukadnezzar tawaye. 2 Ubangiji ya aiki maharan Babiloniyawa,*Ko kuwa Kaldiyawa da na Arameyawa, da na Mowabawa, da na Ammonawa. Ya aike su su hallaka Yahuda bisa ga maganar Ubangiji wadda ya furta ta bakin bayinsa annabawa. 3 Ba shakka waɗannan abubuwa sun faru da Yahuda bisa ga umarnin Ubangiji domin yă kawar da su daga gabansa saboda zunuban Manasse da dukan abin da ya yi, 4 haɗe da zub da jinin marasa laifi. Gama ya ƙazantar da Urushalima da jinin marasa laifi. Ubangiji kuwa bai yi niyyar yafewa ba.
5 Game da sauran ayyukan mulkin Yehohiyakim da abubuwan da ya aikata, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. 6 Yehohiyakim ya huta da kakanninsa. Yehohiyacin ɗansa ya gāje shi.
7 Sarkin Masar bai sāke fita daga ƙasarsa don yaƙi ba domin sarkin Babilon ya mamaye yankin, daga Rafin Masar har zuwa Kogin Yuferites.
Yehohiyacin sarkin Yahuda
(2 Tarihi 36.9,10)
8 Yehohiyacin yana da shekara goma sha takwas da ya zama sarki, ya kuma yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Nehushta ’yar Elnatan, mutuniyar Urushalima. 9 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa ya yi.
10 A wannan lokaci, hafsoshin Nebukadnezzar sarkin Babilon suka kawo wa Urushalima yaƙi, suka kuma kewaye ta. 11 Nebukadnezzar na Babilon da kansa kuwa ya zo birnin yayinda hafsoshinsa suka kewaye ta. 12 Yehohiyacin sarkin Yahuda, da mahaifiyarsa, da masu yi masa hidima, da hakimansa, da kuma fadawansa duk suka miƙa kansu ga Nebukadnezzar.
A shekara ta takwas ta mulkin sarkin Babilon, sarkin Babilon ya mai da Yehohiyacin ɗan kurkuku. 13 Yadda Ubangiji ya faɗa, Nebukadnezzar ya kwashe dukan dukiyar haikalin Ubangiji, da ta fadan sarki, ya kuma kwashe dukan kayan zinariyar da Solomon sarkin Isra’ila ya ƙera domin haikalin Ubangiji. 14 Ya kwashi dukan mutanen Urushalima zuwa bauta, ya kwashi dukan fadawa, da mayaƙa, da masu sana’a, da maƙera, yawansu ya kai dubu goma. Ba wanda ya ragu, sai matalautan ƙasar.
15 Nebukadnezzar ya ɗauki Yehohiyacin ya kai bauta a Babilon. Ya kuma kwashe mahaifiyar sarki, da matansa, da fadawansa, da manyan mutanen ƙasar daga Urushalima ya kai Babilon. 16 Sarkin Babilon kuma ya kwashe dukan mayaƙa dubu bakwai, ƙarfafu, shiryayyu don yaƙi, da masu sana’a, da maƙera dubu ɗaya, ya kai Babilon. 17 Sarkin Babilon ya sa Mattaniya, ɗan’uwan mahaifin Yehohiyacin, ya zama sarki a madadinsa, ya canja masa suna zuwa Zedekiya.
Zedekiya sarkin Yahuda
(2 Tarihi 36.11-16; Irmiya 52.1-3)
18 Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hamutal ’yar Irmiya; mutuniyar Libna. 19 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda Yehohiyakim ya yi. 20 Saboda fushin Ubangiji ne dukan waɗannan abubuwa suka faru da Urushalima, da kuma Yahuda, a ƙarshe kuma ya kawar da su daga fuskarsa.
Fāɗuwar Urushalima
To, sai Zedekiya ya yi wa sarkin Babilon tawaye.