3
Rashin sanin Allah a kwanakin ƙarshe
Amma fa ka san wannan, za a yi lokutan shan wahala a kwanakin ƙarshe. Mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki, marasa ƙauna, marasa gafartawa, masu ɓata sunayen waɗansu, marasa kamunkai, masu ƙeta, marasa ƙaunar nagarta, masu cin amana, marasa hankali, waɗanda sun cika da ɗaga kai, masu son jin daɗi a maimakon ƙaunar Allah suna riƙe da siffofin ibada, amma suna mūsun ikonta. Kada wani abu yă haɗa ka da su.
Irin su ne suke saɗaɗawa su shiga gidaje suna rinjayar mata marasa ƙarfin hali, waɗanda zunubai suka sha kansu, mugayen sha’awace-sha’awace kuma sun ɗauke hankulansu, kullum suna koyo amma ba sa taɓa iya yarda da gaskiya. Kamar dai yadda Yannes da Yamberes*Yannes da Yamberes. Babu waɗannan sunaye a Tsohon Alkawari, amma bisa ga masanan tarihin Yahudawa, mutanen nan su ne bokaye biyun nan na ƙasar Masar da suka yi gāba da Musa lokacin da ya so yă fitar da ’ya’yan Isra’ila daga ƙasar Masar (Dubi Fit 7.11,22; 9.11) suka tayar wa Musa, haka waɗannan mutane ma suke tayar wa gaskiya, mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda, in ana zancen bangaskiya ne, to, fa ba sa ciki. Sai dai ba za su yi nisa ba, don rashin hankalinsu zai bayyana ga kowa, kamar na mutanen nan biyu.
Umarnin Bulus ga Timoti
10 Kai kam, ka san kome game da koyarwata, da halina, da niyyata, bangaskiya, haƙuri, ƙauna, jimiri, 11 tsanani, shan wahala, irin abubuwan da suka faru da ni a Antiyok, Ikoniyum da kuma Listira, tsananin da na jure. Duk da haka Ubangiji ya cece ni daga dukansu. 12 Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani. 13 Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu. 14 Amma kai kam, ka ci gaba da abin da ka koya ka kuma tabbatar, gama ka san waɗanda ka koye su daga gare su, 15 da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. 16 Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci, 17 domin mutumin Allah yă zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.

*3:8 Yannes da Yamberes. Babu waɗannan sunaye a Tsohon Alkawari, amma bisa ga masanan tarihin Yahudawa, mutanen nan su ne bokaye biyun nan na ƙasar Masar da suka yi gāba da Musa lokacin da ya so yă fitar da ’ya’yan Isra’ila daga ƙasar Masar (Dubi Fit 7.11,22; 9.11)