23
1 Bulus ya zuba wa Majalisar ido ya ce, “’Yan’uwana, na cika aikina ga Allah cikin lamiri mai kyau har yă zuwa yau.” 2 Da jin wannan Ananiyas babban firist ya umarci waɗanda suke tsaye kusa da Bulus su buge bakinsa. 3 Sai Bulus ya ce masa, “Allah zai buge ka, kai farin bango! Ka zauna a can kana hukunta ni bisa ga doka, ga shi kai kanka kana ƙetare dokar ta wurin ba da umarni a buge ni!”
4 Waɗanda suke tsaye kusa da Bulus kuwa suka ce masa, “Babban firist na Allah za ka zaga?”
5 Bulus ya amsa ya ce, “’Yan’uwa, ai, ban san cewa shi ne babban firist ba; gama yana a rubuce cewa, ‘Kada ka yi mugun magana game da mai mulkin mutanenka.’*Fit 22.28”
6 Bulus, da ya gane cewa waɗansu daga cikinsu Sadukiyawa ne sauran kuma Farisiyawa ne, sai ya ɗaga murya a Majalisar ya ce, “’Yan’uwana, ni Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ana mini shari’a saboda begen da nake da shi a kan tashin matattu.” 7 Da ya faɗi haka, sai gardama ta tashi tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, taron kuwa ya rabu biyu. 8 (Sadukiyawa suna cewa babu tashin matattu, babu mala’iku ko ruhohi. Amma Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai.)
9 Aka yi babbar hayaniya. Waɗansu daga cikin malaman dokokin da suke Farisiyawa suka miƙe tsaye suka yi gardama mai ƙarfi suna cewa, “Ba mu sami wani laifi a wurin mutumin nan ba. A ce wani ruhu ko mala’ika ne ya yi masa magana fa?” 10 Gardamar kuwa ta yi tsanani har shugaban ƙungiyar sojan ya ji tsoro za su yayyage Bulus. Ya umarci sojoji su tafi su ƙwace shi ƙarfi da yaji daga wurinsu su kawo shi cikin barikin soja.
11 Kashegari da dare Ubangiji ya tsaya kusa da Bulus ya ce, “Ka yi ƙarfin hali! Don kamar yadda ka yi shaida game da ni a Urushalima, haka kuma lalle, za ka yi shaidata a Roma.”
Ƙulla shawara don a kashe Bulus
12 Kashegari, Yahudawa suka ƙulla makirci suka kuma yi rantsuwa cewa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe Bulus. 13 Fiye da mutane arba’in ne suka ƙulla wannan makirci. 14 Suka je wajen manyan firistoci da dattawa suka ce, “Mun yi babbar rantsuwa cewa ba za mu ci kome ba sai mun kashe Bulus. 15 Saboda haka, sai ku da Majalisa sai ku roƙi shugaban ƙungiyar sojan yă kawo shi a gabanku kamar kuna so ku ƙara samun cikakken bayani game da zancensa. Mu kuwa muna a shirye mu kashe shi kafin yă iso nan.”
16 Amma da ɗan ’yar’uwar Bulus ya ji wannan makirci, sai ya tafi cikin barikin soja ya gaya wa Bulus.
17 Sai Bulus ya kira ɗaya daga cikin jarumawan ya ce, “Ka kai wannan saurayi wurin shugaban ƙungiyar soja; yana da wani abin da zai faɗa masa.” 18 Saboda haka ya ɗauke shi ya kai wajen shugaban ƙungiyar sojan.
Jarumin ya ce, “Bulus, ɗan kurkukun nan ya kira ni, ya roƙe ni in kawo wannan saurayi a wurinka domin yana da wani abin da zai faɗa maka.”
19 Sai shugaban ƙungiyar sojan ya kama hannun saurayin ya ja shi gefe, ya tambaye shi cewa, “Mene ne kake so ka gaya mini?”
20 Saurayin ya ce, “Yahudawa sun ƙulla za su roƙe ka ka kawo Bulus a gaban Majalisa gobe kamar suna neman ƙarin cikakken bayani game da Bulus. 21 Kada ka yarda da su, domin fiye da mutum arba’in daga cikinsu suna fakonsa. Sun yi rantsuwa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe shi. Suna nan a shirye yanzu, suna jira ka amince da roƙonsu.”
22 Sai shugaban ƙungiyar sojan ya sallami saurayin ya kwaɓe shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa cewa ka faɗa mini wannan.”
An tura Bulus zuwa Kaisariya
23 Sai ya kira biyu daga cikin jarumawansa, ya umarce su cewa, “Ku shirya sojoji ɗari biyu, da masu hawan dawakai saba’in da kuma masu māsu ɗari biyu su tafi Kaisariya da ƙarfe tara na daren nan. 24 Ku shirya wa Bulus dawakai da zai hau don a kai shi wurin Gwamna Felis lafiya.”
25 Ya kuma rubuta wasiƙa kamar haka,
26 Kalaudiyus Lisiyas.
Zuwa ga Mai Girma, Gwamna Felis.
Gaisuwa.
27 Yahudawa sun kama wannan mutum suna kuma dab da kashe shi, amma na zo da sojojina na ƙwato shi, saboda na ji shi ɗan ƙasar Roma ne. 28 Na so in san abin da ya sa suke zarginsa, saboda haka na kawo shi a gaban Majalisarsu. 29 Na tarar cewa zargin da ake masa ya shafi waɗansu abubuwan da suka shafi dokarsu ne, amma ba wani zargi a kansa da ya isa kisa ko a daure shi. 30 Sa’ad da na sami labari cewa akwai wani makircin da aka ƙulla masa, sai na aika shi wurinka nan da nan. Na kuma umarci masu zarginsa su kai ƙararsu gare ka.
31 Saboda haka sojojin, don cika umarni, suka ɗauki Bulus da dad dare suka kawo shi har Antifatiris. 32 Kashegari suka bar masu hawan dawakai suka ci gaba da shi, yayinda sojojin suka koma barikin soja. 33 Sa’ad da masu hawan dawakai suka isa Kaisariya, sai suka ba wa gwamna wasiƙar suka kuma miƙa masa Bulus. 34 Gwamna ya karanta wasiƙar ya kuma tambaya ko daga wanda lardi ne ya fito. Da ya ji cewa shi daga Silisiya ne, 35 sai ya ce, “Zan ji batunka lokacin da masu zarginka suka iso.” Sa’an nan ya ba da umarni a kai Bulus a tsare shi a fadar Hiridus.