Daniyel
1
Horarwar Daniyel a Babilon
A Shekara ta uku ta mulki Yehohiyakim sarkin Yahuda, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya zo Urushalima ya kuma yi mata ƙawanya. Sai Ubangiji ya bashe Yehohiyakim sarkin Yahuda a hannunsa, tare da waɗansu kayayyakin haikalin Allah. Ya ɗauki waɗannan kayan zuwa cikin haikalin allahnsa a Babilon* Shinar na Ibraniyanci cikin ma’ajin gidan allahnsa.
Sa’an nan sarkin ya umarci Ashfenaz, shugaban fadarsa yă kawo waɗansu daga cikin Isra’ilawan da suka fito daga gidan sarauta da kuma na fitattun mutane. Matasa maza waɗanda ba su da wata naƙasa kuma kyawawa, hazikai ta kowace hanyar koyo, sanannu, masu saurin fahimtar abu, da kuma waɗanda suka cancanci su yi aiki a fadar sarki. Zai koya musu harshen Babiloniyawa da kuma littattafansu. Ko kuwa Kaldiyawa Sarki kuma ya sa a ba su abinci da ruwan inabi kowace rana daga cikin abincin sarki. Za a koyar da su har shekaru uku, bayan haka kuma su shiga yin wa sarki hidima.
Daga cikin waɗannan da aka zaɓa akwai waɗansu daga Yahuda, Daniyel, Hananiya, Mishayel da kuma Azariya. Sai sarkin fada ya raɗa musu sababbin sunaye, ga Daniyel ya raɗa masa Belteshazar; ga Hananiya ya raɗa masa Shadrak; ga Mishayel ya raɗa masa Meshak; ga Azariya kuma ya raɗa masa Abednego.
Amma Daniyel ya ƙudura a zuciyarsa ba zai ƙazantar da kansa da abinci da ruwan inabin sarki ba, sai ya tambayi sarkin fada don a ba shi izinin kada yă ƙazantar da kansa ta wannan hanya. Sai Allah ya sa sarkin fada ya nuna masa tagomashi ya kuma ƙaunaci Daniyel, 10 amma sai sarkin fada ya ce wa Daniyel, “Ina jin tsoron ranka yă daɗe, sarkina wanda ya sa a ba ku abinci da ruwan inabi. Me zai sa yă ga kuna ramewa fiye da sauran samari, tsaranku? Sarki zai sa a fille mini kai saboda ku.”
11 Sai Daniyel ya ce wa mai gadi wanda sarkin fada ya sa yă kula da Daniyel, Hananiya, Mishayel da Azariya, 12 “Ina roƙonka ka gwada bayinka kwana goma. Kada ka ba mu kome sai kayan lambu mu ci da kuma baƙin ruwa mu sha. 13 Sa’an nan sai ka dubi fuskokinmu da na sauran samarin da suke ci daga abincin sarki; sa’an nan ka yi da bayinka bisa ga abin da ka gani.” 14 Sai ya amince da haka ya kuma gwada su har kwana goma.
15 A ƙarshen kwana goma sai aka ga fuskokinsu suna sheƙi, sun kuma yi ƙiba fiye da samarin da suke cin abinci irin na sarki. 16 Sai mai gadinsu ya janye abinci da ruwan inabi irin na sarki, ya ci gaba da ba su kayan lambu.
17 Ga samarin nan guda huɗu Allah ya ba su sani da ganewar dukan irin littattafai da kuma koyarwa. Daniyel kuma ya iya gane wahayi da kowane irin mafarki.
18 A ƙarshen lokacin da sarki ya sa da za a kawo su ciki, sai sarkin fada ya gabatar da su ga Nebukadnezzar. 19 Sarki kuwa ya yi magana da su, sai ya gano cewa babu wani kamar Daniyel, Hananiya, Mishayel da kuma Azariya; don haka sai suka shiga yi wa sarki hidima. 20 A dukan al’amuran hikima da na fahimta wanda sarki ya tambaye su, ya tarar sun fi dukan masu sihiri da bokaye waɗanda suke cikin mulkinsa sau goma.
21 Daniyel kuwa ya kasance a nan har shekara ta farko ta mulkin sarki Sairus.

*1:2 Shinar na Ibraniyanci

1:4 Ko kuwa Kaldiyawa