Mai Hadishi
1
Kome ba shi da amfani
1 Kalmomin Malami,*Ko kuwa shugaban taro; haka ma a ayoyi 2 da kuma 12. ɗan Dawuda, Sarki a Urushalima.
2 “Ba amfani! Ba amfani!”
In ji Malami.
“Gaba ɗaya ba amfani!
Kome ba shi da amfani!”
3 Wace riba ce mutum yake samu daga wahalar
da yake fama a duniya?
4 Zamanai sukan zo zamanai su wuce,
amma duniya tana nan har abada.
5 Rana takan fito rana ta kuma fāɗi,
ta kuma gaggauta zuwa inda takan fito.
6 Iska takan hura zuwa kudu ta kuma juya zuwa arewa;
tă yi ta kewayewa, tă yi ta koma inda take fitowa.
7 Dukan rafuffuka sukan gangara zuwa teku,
duk da haka teku ba ya cika.
Daga inda rafuffukan suke fitowa,
a can suke komawa kuma.
8 Dukan abubuwa suna kawo gajiya,
gaban magana.
Ido ba ya gaji da gani,
haka ma kunne yă ƙoshi da ji.
9 Abin da ya taɓa kasancewa, zai sāke kasance,
abin da aka yi za a sāke yi kuma;
babu wani abu sabo a duniya.
10 Akwai wani abin da za a ce,
“Duba! Ga wani abu sabo”?
Abin yana nan, tun dā can,
ya kasance kafin lokacinmu.
11 Ba a tunawa da mutanen dā,
haka su ma da ba a haifa ba tukuna
waɗanda za su biyo bayansu
ba za a tuna da su ba.
Hikima ba ta da amfani
12 Ni, Malami, sarki ne bisa Isra’ila a Urushalima. 13 Na dauri aniyata in gwada don in bincika ta wurin hikima dukan abin da ake yi a duniya. Kaya mai nauyi ne Allah ya ɗora a kan mutane! 14 Na ga dukan abubuwan da ake yi a duniya, dukansu ba su da amfani, naushin iska ne kawai.
15 Abin da yake tanƙwararre ba zai miƙu ba;
ba za a kuma iya ƙidaya abin da ba shi ba.
16 Na yi tunani a raina na ce, “Duba, na yi girma, na kuma ƙaru da hikima fiye da duk wanda ya taɓa mulki a bisa Urushalima kafin ni; na ɗanɗana hikima mai yawa da kuma ilimi.” 17 Sa’an nan na ɗaura aniyata ga fahimtar hikima, in kuma san bambanci tsakanin hauka da wauta, amma na koyi cewa wannan ma, naushin iska ne kawai.
18 Gama yawan hikima yakan kawo yawan baƙin ciki;
yawan sani, yawan ɓacin rai.