7
Hikima
Suna mai kyau ya fi turare mai ƙanshi,
kuma ranar mutuwa ta fi ranar haihuwa.
Gara a tafi gidan makoki
da a je gidan biki,
gama mutuwa ce ƙaddarar kowane mutum;
ya kamata masu rai su lura da haka.
Baƙin ciki ya fi dariya,
gama baƙin ciki yakan kawo gyara.
Zuciyar masu hikima tana a gidan makoki,
amma zuciya wawaye tana a gidan shagali.
Gara ka saurari tsawatawar mai hikima
da ka saurari waƙar wawaye.
Kamar ƙarar ƙayar da take karce gindin tukunya,
haka dariyar wawaye take.
Wannan ma ba shi da amfani.
 
Zalunci yakan mai da mutum mai hikima wawa,
cin hanci kuma yakan lalace hali.
 
Ƙarshen abu ya fi farkonsa,
haƙuri kuma ya fi girman kai.
Kada ranka yă yi saurin tashi,
gama fushi yana zama a cinyar wawaye.
 
10 Kada ka ce, “Me ya sa kwanakin dā sun fi waɗannan?”
Gama ba daidai ba ne a yi irin waɗannan tambayoyi.
 
11 Hikima, kamar gādo, abu mai kyau ne
tana kuma da amfani ga waɗanda suka ga rana.
12 Hikima mafaka ce
takan kāre mutum kamar yadda kuɗi suke yi.
Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita
ita ce amfanin ilimi.
13 Ku lura da abin da Allah ya yi.
Wa zai iya miƙe
abin da ya tanƙware?
14 Sa’ad da al’amura suke tafiya daidai, ka yi farin ciki,
amma sa’ad da suka lalace, ka tuna,
Allah ne ya yi wancan
shi ne kuma ya yi wannan.
Saboda haka, mutum ba zai san
wani abu game da nan gabansa ba.
15 A cikin rayuwan nan ta rashin amfani nawa, na lura da waɗannan abubuwa biyu,
mai adalci yana hallakawa cikin adalcinsa,
mai mugunta kuma yana tsawon rai cikin muguntarsa.
16 Kada ka cika yin adalci, fiye da kima,
kada kuma ka cika yin hikima,
don me za ka hallaka kanka!
17 Kada ka cika yin mugunta,
kada kuma ka cika yin wauta,
don me za ka mutu kafin lokacinka?
18 Yana da kyau ka kama ɗaya
ba tare da ka saki wancan ba.
Mai tsoron Allah zai guji wuce gona da iri.*Ko kuwa zai bi su biyu
 
19 Hikima takan sa mutum guda mai hikima yă yi ƙarfi
fiye da masu mulki goma a cikin birni.
 
20 Babu mai adalci a duniya
wanda yake yin abin da yake daidai da bai taɓa yin zunubi ba.
 
21 Kada ka mai da hankali ga dukan abin da mutane suke faɗi,
in ba haka ba wata rana za ka ji bayinka suna zaginka.
22 Gama kai kanka ka sani
cewa sau da yawa ka zagi waɗansu.
23 Dukan waɗannan na gwada su ta wurin hikima na kuma ce,
“Na ƙudurta in zama mai hikima,”
amma abin ya fi ƙarfina.
24 Ko da me hikima take,
Abin ya yi mana zurfi ƙwarai, yana da wuyar ganewa,
wa zai iya gane shi?
25 Saboda haka na mai da hankalina ga fahimi,
don in bincika in nemi hikima da yadda aka tsara abubuwa,
in kuma fahimci wawancin mugunta
da haukar wauta.
 
26 Sai na iske wani abin da ya fi mutuwa ɗaci
mace wadda take tarko ne,
wadda zuciyarta tarko ne
wadda kuma hannuwanta sarƙa ne.
Mutumin da ya gamshi Allah zai tsere mata,
amma za tă kama mai zunubi.
27 Malami ya ce, “Duba, abin da na gane ke nan.
“Na tara abu guda da wani, don in gane tsarin abubuwa,
28 yayinda nake cikin nema
amma ban samu ba,
sai na sami adali guda cikin dubu,
amma ba mace mai adalci guda a cikinsu duka.
29 Wannan ne kaɗai abin da na gane.
Allah ya yi mutum tsab
amma sai muka rikitar da kanmu.”
 

*7:18 Ko kuwa zai bi su biyu