6
’Ya’ya da iyaye
Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”*M Sh 5.16
Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.
Bayi da iyayengiji
Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya. Ku nuna musu halin bangirma, kuna kuma yin musu biyayya cikin dukan abu, da zuciya ɗaya kamar ga Kiristi kuke yi. Ku yi aiki sosai, ba don kawai ku gamshe su sa’ad da suke kallonku ba. Da yake ku bayin Kiristi ne, ku aikata nufin Allah da dukan zuciyarku. Ku yi aikinku da kyakkyawar niyya, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba mutane ba. Gama kun san cewa Ubangiji zai ba da lada ga kowa gwargwadon kowane aiki nagarin da ya yi, ko shi bawa ne, ko ’yantacce.
Ku kuma masu bayi, dole ku bi da bayinku da kyau. Ku daina ba su tsoro. Ku tuna, ku da su, Maigida ɗaya kuke da shi a sama, kuma ba ya nuna bambanci.
Kayan yaƙi na Allah
10 A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yă ba ku ƙarfi. 11 Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan. 12 Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. 13 Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge. 14 Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya tă zama ɗamararku, adalci yă zama sulkenku, 15 shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku. 16 Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita. 17 Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.
18 A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a. 19 Ku kuma yi addu’a domina, don duk sa’ad da na buɗe bakina, in sami kalmomi babu tsoro, don in sanar da asirin bishara, 20 wadda nake jakadanta cikin sarƙoƙi. Ku yi addu’a don in iya yin shelarta babu tsoro, yadda ya kamata in yi.
 
Gaisuwar ƙarshe
21 Tikikus, ƙaunataccen ɗan’uwa da kuma amintaccen bawa cikin Ubangiji, zai faɗa muku kome, domin ku ma ku san yadda nake, da kuma abin da nake yi. 22 Na aike shi gare ku musamman don wannan, domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa ku.
 
23 ’Yan’uwa, salama tare da ƙauna da kuma bangaskiya daga Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi su kasance tare da ku.
 
24 Alheri yă tabbata ga dukan masu ƙaunar Ubangiji Yesu Kiristi da ƙauna marar ƙarewa.

*6:3 M Sh 5.16