7
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Duba, na maishe ka kamar Allah ga Fir’auna, ɗan’uwanka Haruna kuma zai zama annabinka. Za ka faɗi kome da na umarce ka, ɗan’uwanka Haruna kuwa zai faɗa wa Fir’auna, yă bar Isra’ilawa su fita daga ƙasarsa. Amma zan taurare zuciyar Fir’auna, kuma ko da na ninka mu’ujizai da kuma alamu a Masar, ba zai saurare ku ba. Don haka zan miƙa hannuna a kan Masar, in murƙushe ta da bala’i iri-iri, bayan haka zan fitar da taron mutanen Isra’ila daga ƙasar Masar ta wurin hukuntaina masu girma. Masarawa kuwa za su san cewa ni ne Ubangiji sa’ad da na miƙa hannuna a kan Masar, na kuma fitar da Isra’ilawa daga gare ta.”
Musa da Haruna suka aikata yadda Ubangiji ya umarce su. Musa yana da shekara tamanin da haihuwa, Haruna kuma yana da shekara tamanin da uku, sa’ad da suka yi magana da Fir’auna.
Sandan Haruna ya zama Maciji
Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Sa’ad da Fir’auna ya ce muku, ‘Aikata wani al’ajabi,’ sai ka ce wa Haruna, ‘Ɗauki sandanka ka jefa shi a ƙasa, a gaban Fir’auna,’ zai kuwa zama maciji.”
10 Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna, suka yi yadda Ubangiji ya umarce su. Haruna ya jefa sandansa ƙasa, a gaban Fir’auna da bayinsa, sai sandan ya zama maciji. 11 Fir’auna kuwa ya kira masu hikima da masu sihiri, sai bokayen Masarawa ma suka yi irin abubuwan nan da bokancinsu. 12 Kowannensu ya jefa sandansa ƙasa, ya kuwa zama maciji. Amma sandan Haruna ya haɗiye sandunansu. 13 Duk da haka zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa saurare su ba, kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.
Annobar jini
14 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Zuciyar Fir’auna taurariya ce, ya ƙi yă bar mutanen su tafi. 15 Ka je wurin Fir’auna da safe, yayinda za shi kogi. Ka jira a bakin Nilu don ka sadu da shi, ka ɗauki sandan nan da ya canja zuwa maciji a hannunka. 16 Sa’an nan ka ce masa, ‘Ubangiji, Allah na Ibraniyawa, ya aiko ni in faɗa maka, Ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada a hamada. Amma har yanzu ba ka yi biyayya ba. 17 Ga abin da Ubangiji ya ce, da wannan za ka san cewa ni ne Ubangiji. Da sandan da yake hannuna zan bugi ruwan Nilu, zai kuma zama jini. 18 Kifi a ciki Nilu za su mutu, ruwan kuma zai yi ɗoyi; Masarawa ba za su iya shan ruwansa ba.’ ”
19 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Ka ɗauki sandanka, ka miƙa hannunka kan ruwan Masar, kan kogunansu da rafuffukansu da kududdufansu da kuma dukan tafkunansu, za su zama jini.’ Jini zai kasance ko’ina a Masar, har ma a cikin abubuwan ajiyar ruwansu*Ko kuwa har ma a kan gumakansu da aka yi da itace da kuma dutse.”
20 Musa da Haruna suka yi yadda Ubangiji ya umarta. Ya ɗaga sandansa a gaban Fir’auna da bayinsa, ya bugi ruwan Nilu, dukan ruwan kuwa ya zama jini. 21 Kifin da suke cikin Nilu suka mutu, kogin kuwa ya yi wari sosai yadda Masarawa ba su iya shan ruwan ba. Jini ya bazu ko’ina a Masar.
22 Amma bokayen Masar ma suka yi abubuwan nan da sihirinsu, sai zuciyar Fir’auna ta taurare; bai saurari Musa da Haruna ba, kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa. 23 A maimakon yă saurara, sai ya juya ya koma fadarsa, bai ma damu da abin da aka yi ba. 24 Sai dukan Masarawa suka yi ta tonon gefen Nilu don su sami ruwan sha, domin ba su iya shan ruwan kogin ba.
Annobar kwaɗi
25 Kwana bakwai suka wuce bayan da Ubangiji ya bugi kogin.

*7:19 Ko kuwa har ma a kan gumakansu