19
A Dutsen Sinai
A rana ta farko a cikin watan uku bayan da Isra’ilawa suka bar Masar, a wannan rana, suka iso Hamadar Sinai. Bayan da suka tashi daga Refidim, suka shiga Hamadar Sinai, sai Isra’ilawa suka yi sansani a gaban dutsen.
Sai Musa ya hau kan dutsen don yă sadu da Allah, Ubangiji kuwa ya kira shi daga dutsen ya ce, “Wannan shi ne abin da za ka faɗa wa gidan Yaƙub, da kuma abin da za ka faɗa wa mutanen Isra’ila. ‘Ku da kanku kun ga abin da na yi wa Masar, da yadda na ɗauko ku a kan fikafikan gaggafa na kawo ku wurina. Yanzu, in kuka yi mini cikakken biyayya, kuka kuma kiyaye yarjejjeniyata, to, za ku zama keɓeɓɓiyar taska a gare ni a cikin dukan al’ummai. Ko da yake duk duniya tawa ce, za ku zama firistoci masu tsarki da kuma al’umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne kalmomin da za ka faɗa wa Isra’ilawa.”
Sai Musa ya koma ya aika a kira dukan dattawan mutane, ya bayyana dukan kalmomin da Ubangiji ya umarta, ya faɗa. Dukan mutane suka amsa gaba ɗaya suka ce, “Za mu yi duk abin da Ubangiji ya faɗa.” Sai Musa ya mayar wa Ubangiji amsar da mutane suka bayar.
Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ina zuwa wurinka a cikin baƙin hadari, domin mutane su ji ni ina maganar da kai, domin su amince da kai koyaushe.” Sa’an nan Musa ya faɗa wa Ubangiji abin da mutane suka ce.
10 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tafi wurin mutanen, ka tsarkake su yau da gobe, ka sa su wanke tufafinsu. 11 Su zama da shiri a rana ta uku, gama a ranar ce Ubangiji zai sauko a kan Dutsen Sinai a idon dukan mutane. 12 Sai ka yi wa jama’a iyaka kewaye da dutsen, ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ku mai da hankali, kada ku hau dutsen ko ku taɓa gefensa. Duk wanda ya taɓa dutsen, lalle za a kashe shi. 13 Za a jajjefe shi da duwatsu, ko a harbe shi da kibiyoyi, ba hannun da zai taɓa shi. Mutum ko dabbar da ya taɓa, ba za a bar shi da rai ba.’ Lokacin da aka ji muryar ƙaho ne kawai za su iya taru a gindin dutsen.”
14 Bayan da Musa ya gangara wurin mutane, ya tsarkake su, sai suka wanke tufafinsu. 15 Sa’an nan ya ce wa mutane, “Ku shirya kanku domin rana ta uku. Ku ƙame kanku daga yin jima’i.”
16 A safiyar rana ta uku, aka yi tsawa, da walƙiyoyi, sai ga girgije mai duhu a bisa dutsen, aka tsananta busar ƙaho, sai dukan jama’ar da suke cikin sansani suka yi rawar jiki. 17 Sa’an nan Musa ya jagoranci mutane daga sansani domin su sadu da Allah, sai suka tsaya a gefen dutsen. 18 Dutsen Sinai kuwa ya tunnuƙe duka da hayaƙi, gama Ubangiji ya sauko a bisan dutsen cikin wuta. Hayaƙin ya hau kamar hayaƙin da yake fitowa daga matoya, duk dutsen ya yi rawa da ƙarfi, 19 sai karar ƙaho ya yi ta ƙaruwa. Sa’an nan Musa ya yi magana, murya Allah kuwa ta amsa masa.
20 Ubangiji ya sauko a kan ƙwanƙolin Dutsen Sinai, ya kira Musa zuwa ƙwanƙolin dutsen. Musa kuwa ya haura 21 sai Ubangiji ya ce masa, “Ka sauka ka faɗa wa jama’a, kada su kuskura su ƙetare layin iyakan nan, garin son zuwa don ganin Ubangiji, gama duk waɗanda suka yi haka za su mutu. 22 Ko firistocin da za su kusato Ubangiji sai su tsarkake kansu, don kada in hallaka su.”
23 Musa ya ce wa Ubangiji, “Mutanen ba za su hau Dutsen Sinai ba, gama kai da kanka ka gargaɗe mu, ‘Ku sa iyaka kewaye da dutsen ku kuma tsarkake shi.’ ”
24 Ubangiji ya amsa, “Sauka ka kawo Haruna tare da kai. Amma kada firistoci da mutane su zarce iyakan nan, a kan za su zo wurin Ubangiji, don kada in hallaka su.”
25 Saboda haka Musa ya sauka wurin mutane ya kuma faɗa musu.