34
Sababbin allunan dutse
(Maimaitawar Shari’a 10.1-5)
1 Ubangiji ya ce wa Musa “Sassaƙa alluna biyu kamar na farko, ni kuwa in rubuta kalmomin da suke cikin alluna na farko da ka farfasa. 2 Ka shirya da safe, ka hauro kan Dutsen Sinai. Ka gabatar da kanka a gare ni a can kan dutse. 3 Ba wani da zai zo tare da kai, ko a gan shi ko’ina a kan dutsen, kada garkunan tumaki ko na shanu su yi kiwo kusa da dutsen.”
4 Saboda haka Musa ya sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na fari, sai ya hau Dutsen Sinai da sassafe, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, yana kuma ɗauke da alluna biyu na dutse a hannuwansa. 5 Sa’an nan Ubangiji ya sauko a cikin girgije ya tsaya can tare da shi, ya kuma yi shelar sunansa. 6 Sai Ubangiji ya wuce a gaban Musa, ya yi shela ya ce, “Ni ne Ubangiji Allah mai tausayi, mai alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna da aminci, 7 nakan nuna ƙauna wa dubbai, nakan kuma gafarta mugunta, tawaye da zunubi. Amma ba na barin mai laifi, ba tare da na hore shi ba; nakan hukunta ’ya’ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu saboda laifin iyaye.”
8 Musa ya yi sauri ya rusuna har ƙasa, ya yi sujada. 9 Ya ce, “Ya Ubangiji, in na sami tagomashi a idanunka, bari Ubangiji yă tafi tare da mu. Ko da yake wannan mutane masu taurinkai ne, ka gafarta muguntanmu da zunubanmu, ka kuma sāke sa mu zama abin gādonka.”
(Fitowa 23.14-19; Maimaitawar Shari’a 7.1-5; 16.1-17)
10 Sai Ubangiji ya ce, “Ga shi na yi alkawari da kai. A gaban dukan mutanenka zan yi abubuwan banmamakin da ba a taɓa yinsa a cikin wata al’umma a duniya ba. Mutanen da kuke zaune cikinsu za su ga aikin bantsoro, da Ni Ubangiji zan yi muku. 11 Ku yi biyayya da umarnin da na ba ka yau. Zan kora muku Amoriyawa, Kan’aniyawa, Hittiyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa. 12 Ku kula, kada ku yi yarjejjeniya da waɗanda suke zaune a ƙasar da za ku tafi, in ba haka ba, za su zama muku tarko. 13 Ku rurrushe bagadansu, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu, ku sassare ginshiƙan Asheransu.*Wato, alamun alliya Ashera 14 Kada ku bauta wa wani allah, gama Ubangiji, wanda sunansa Kishi, Allah ne mai kishi.
15 “Ku kula, kada ku yi yarjejjeniya da mazaunan wannan ƙasa, don kada sa’ad da suke yi wa allolinsu sujada, suna miƙa musu hadaya, su gayyace ku, ku ci hadayar da suka miƙa wa allolinsu. 16 Kada ku auro wa ’ya’yanku maza ’yan matansu, waɗanda suke yi wa alloli sujada, har su sa ’ya’yanku su bi allolinsu.
17 “Kada ku yi alloli na zubi.
18 “Sai ku yi Bikin Burodi Marar Yisti. Ku kuma ci burodi marar yisti har kwana bakwai, kamar yadda na umarce ku. Ku yi wannan a ƙayyadadden lokacinsa a watan Abib, gama a cikin watan ne kuka fita daga Masar.
19 “Ɗan fari na kowane mutum zai zama nawa, har da ɗan farin na dabbobi, ko na garken shanu ko na tumaki. 20 Ku fanshi ɗan farin jaki da na tunkiya, amma in ba ku fanshe shi ba, ku karya wuyansa. Ku fanshi duk ’ya’yan farinku maza.
“Kada wani yă zo gabana hannu wofi.
21 “Kwana shida za ku yi aiki, amma a rana ta bakwai za ku huta; ko da lokacin noma ne, ko lokacin girbi, sai ku huta.
22 “Ku kiyaye Bikin Makoni wato, bikin girbin nunan fari na alkama, da Bikin Gama Tattara amfanin gonaki, a ƙarshen shekara. 23 Sau uku a shekara, dukan mazanku za su bayyana a gaban Ubangiji Mai Iko Duka, Allah na Isra’ila. 24 Zan kore al’umma daga gabanku, in fadada kan iyakarku, babu wanda zai yi ƙyashin ƙasarku a lokutan nan uku na shekara da kuka haura don ku bayyana a gaban Ubangiji, Allahnku.
25 “Kada ku miƙa mini jinin hadaya tare da wani abin da yana da yisti, kada kuma ku bar kowace hadaya ta Bikin Ƙetarewa ta kwana.
26 “Ku kawo nunan farin amfanin gonarku mafi kyau a gidan Ubangiji, Allahnku.
“Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madarar mahaifiyarsa.”
27 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka rubuta waɗannan kalmomi, gama bisa ga kalmomin nan, na yi alkawari da kai da kuma Isra’ila.” 28 Musa ya kasance tare da Ubangiji kwana arba’in da dare arba’in, bai ci ba, bai sha ba. Ya kuma rubuta kalmomin alkawari a kan alluna, wato, dokoki goma.
Fuskar Musa mai haske
29 Sa’ad da Musa ya sauko daga kan Dutsen Sinai tare da alluna biyu na Alkawari a hannuwansa, bai san cewa fuskarsa tana ƙyalli ba saboda zaman da ya yi a gaban Ubangiji. 30 Da Haruna da dukan Isra’ila suka ga Musa, fuskarsa kuma tana ƙyalli, sai suka ji tsoron zuwa kusa da shi. 31 Amma Musa ya kira su, sai Haruna da dukan shugabannin jama’ar suka zo wurinsa, ya kuwa yi musu magana. 32 Daga baya sai dukan Isra’ilawa suka zo kusa da shi, ya kuma ba su dukan dokokin da Ubangiji ya ba shi a Dutsen Sinai.
33 Da Musa ya gama magana da su, sai ya lulluɓe fuskarsa. 34 Amma duk sa’ad da ya je gaban Ubangiji don yă yi magana da shi, sai yă tuɓe lulluɓin har sai ya fito. Kuma duk sa’ad da ya fito yă faɗa wa Isra’ilawa abin da aka umarce shi, 35 sai su ga fuskarsa tana ƙyalli. Sa’an nan Musa yă sāke lulluɓe fuskarsa, har sai ya shiga don yă yi magana da Ubangiji.