16
Misalin rashin amincin Urushalima
1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 2 “Ɗan mutum, ka sa Urushalima ta san ayyukanta masu banƙyama 3 ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wa Urushalima, Asalinki da haihuwarki daga ƙasar Kan’ana ne; mahaifinki mutumin Amoriyawa ne, mahaifiyarki kuma mutuniyar Hitti ce. 4 A ranar da aka haife ki ba a yanke cibiyarki ba, ba a kuma yi miki wanka don a tsabtacce ki ba, ba a kuma goge ki da gishiri ba ko a naɗe ki cikin tsummoki. 5 Ba wanda ya dube ki da tausayi ko ya nuna miki isashen jinƙai don yă yi miki ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa. A maimako, sai aka jefar da ke a fili, gama a ranar da aka haife ki an ji ƙyamarki.
6 “ ‘Sa’an nan na wuce na ga kina birgima cikin jininki, yayinda kike kwance can cikin jininki sai na ce miki, “Ki rayu!”*Kaɗan cikin rubuce-rubucen Ibraniyanci, Seftuwajin, da kuma Siriyak; yawancin rubuce-rubucen Ibraniyanci na da “Ki rayu!” Kuma yayinda kike kwance cikin jininki na ce miki, “Ki rayu!” 7 Na sa kin yi girma kamar tsiro a fili. Kin yi girma kika kuma yi tsayi kika zama mafiya kyau na kayan ado.†Ko kuwa kika zama budurwa Nononki suka fito, gashinki kuwa suka yi girma, duk da haka tsirara kike tik.
8 “ ‘Daga baya na wuce, da na dube ki sai na ga cewa kin yi girma sosai har kin kai a ƙaunace ki, na yafa gefen tufafina a kanki na kuma rufe tsiraincinki. Na rantse miki, na ƙulla alkawari da ke, kin kuwa zama tawa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
9 “ ‘Na yi miki wanka na wanke miki jini daga gare ki na kuma shafa miki mai. 10 Na rufe ki da rigar da aka yi wa ado na kuma sa miki takalman fata. Na sa miki riga ta lilin mai kyau na kuma rufe ki da riguna masu tsada. 11 Na yi miki ado da kayan ado masu daraja, na sa miki mundaye a hannuwanki da abin wuya a wuyanki, 12 na kuma sa miki zobe a hancinki, abin kunne a kunnuwanki da rawani mai kyau a kanki. 13 Haka kuwa aka caɓa miki zinariya da azurfa; tufafinki kuwa na lilin mai kyau da riguna masu tsada waɗanda aka yi musu ado. Abincinki na gari mai laushi ne, zuma da man zaitun. Kika zama kyakkyawa har kika kuma zama sarauniya. 14 Sunanki ya yaɗu a cikin al’ummai saboda kyanki, domin darajar da na ba ki ya sa kyanki ya zama cikakke, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
15 “ ‘Amma kika dogara ga kyanki kika kuma yi amfani da sunan da kika yi don ki zama karuwa. Kin yi ta jibga alherai a kan kowa da ya wuce, sai kyanki ya zama naki. 16 Kin ɗauki waɗansu tufafinki don ki yi wa kanki masujadai masu ado, inda kike karuwancinki. Irin waɗannan abubuwa bai kamata su faru ba, bai kuma kamata su taɓa faruwa ba. 17 Kika kuma ɗauki kayan ado masu kyau da na ba ki, kayan adon da aka yi da zinariya da azurfa, kika yi wa kanki gumakan maza kika kuma yi ta yin karuwanci da su. 18 Kika ɗauki rigunanki masu ado don ki sa a kansu, kika kuma miƙa maina da turarena a gabansu. 19 Haka ma abincin da na tanada miki, lallausan gari, man zaitun, da zuman da na ba ki ki ci, kin miƙa su kamar turare mai ƙanshi a gabansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
20 “ ‘Kika kuma kwashe ’ya’yanki maza da mata waɗanda kin haifa mini kika miƙa su kamar abinci ga gumakanki. Karuwancinki bai isa ba ne? 21 Kin kashe ’ya’yana kika kuma miƙa su‡Ko kuwa kika kuma sa suka wuce ta cikin wuta ga gumaka. 22 Cikin dukan ayyukan banƙyamarki da karuwancinki ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba, sa’ad da kike tsirara tik, kina birgima cikin jininki.
23 “ ‘Kaito! Kaitonki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Bugu da ƙari a kan dukan waɗansu muguntarki, 24 kin gina wa kanki ɗakunan sama da gidajen tsafi a kowane dandali. 25 A kowane titi kin gina ɗakin tsafi kika kuma wulaƙanta kyanki, kina miƙa jikinki da ƙarin fasikanci ga duk mai wucewa. 26 Kin yi karuwanci da Masarawa, maƙwabtanki masu kwaɗayi, kika tsokane ni har na yi fushi da ƙarin fasikancinki. 27 Saboda haka na miƙa hannuna gāba da ke na kuma rage iyakarki; na ba da ke ga abokan gābanki masu haɗama, ’yan matan Filistiyawa, waɗanda suka sha mamaki saboda halinki na lalata. 28 Kin kuma yi karuwanci da Assuriyawa, domin ba kya ƙoshi; kai ko bayan wannan, ba ki ƙoshi ba. 29 Sai kika ƙara fasikancinki da ya haɗa da ƙasar cinikin Babilon,§Ko kuwa Kaldiya amma duk da haka ba ki ƙoshi ba.
30 “ ‘Kina da rashin ƙarfi a zuci, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, sa’ad da kika yi duk waɗannan abubuwa, kina yi kamar karuwar da aka watsa! 31 Sa’ad da kika gina ɗakunan samanki a kowane gefen titi kika kuma gina ɗakunan tsafinki a kowane dandali, ba kamar karuwa kike ba, domin kin karɓi kuɗi.
32 “ ‘Ke mazinaciyar mace! Kin gwammace baƙi a maimakon mijinki! 33 Kowace karuwa kan karɓi kuɗi, amma kina ba da kyautai ga dukan kwartayenki, kina ba su cin hanci don su zo wurinki daga ko’ina don alherai marasa ƙa’ida. 34 Saboda haka cikin karuwancinki kin sha bamban da saura; babu wanda yake binki saboda alheranki. Ke dai dabam ce, gama kikan biya kuma ba mai biyanki.
35 “ ‘Saboda haka, ke karuwa, ki ji maganar Ubangiji! 36 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kin zubar da dukiyarki*Ko kuwa sha’awar kika bayyana tsiraicinki cikin fasikancinki da kwartayenki, kuma saboda dukan gumakan banƙyamarki, kuma saboda kin ba su jinin ’ya’yansu, 37 saboda haka zan tattara dukan kwartayenki, waɗanda kike jin daɗinsu, waɗanda kike ƙauna da waɗanda kike ƙi. Zan tattara su gāba da ke daga dukan kewaye zan kuma tuɓe ki a gabansu, za su kuwa ga dukan tsiraicinki. 38 Zan hukunta ki da hukuncin matan da suke zina da kuma waɗanda suke zub da jini; zan kawo hakkin jini na fushina da kuma fushin kishina. 39 Sa’an nan zan miƙa ki ga kwartayenki, za su kuwa rurrushe ɗakunan samanki su kuma farfashe ɗakunan tsafinki. Za su tuɓe miki tufafinki su kuma kwashe kayan adonki masu kyau su bar ki tsirara tik. 40 Za su kawo taron jama’a a kanki, waɗanda za su jajjefe ki da dutse su sassare ki gunduwa-gunduwa da takubansu. 41 Za su ƙone gidajenki su kuma hukunta ki a idon mata masu yawa. Zan kawo ƙarshen karuwancinki, ba za ki kuma ƙara biyan kwartayenki ba. 42 Sa’an nan fushina a kanki zai huce fushin kishina kuma ya kwanta; zan huce ba kuwa zan ƙara yin fushi ba.
43 “ ‘Domin ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba amma kika husatar da ni da waɗannan abubuwa, tabbatacce zan sāka miki alhakin ayyukanki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ba kin ƙara lalata ga dukan waɗansu ayyuka masu banƙyamarki ba?
44 “ ‘Duk mai yin amfani da karin magana zai faɗi wannan karin magana a kanki cewa, “Kamar yadda mahaifiya take haka ’yar take.” 45 Ke ’yar mahaifiyarki ce da gaske, wadda ta ƙi mijinta da ’ya’yanta; ke kuma ’yar’uwar ’yar’uwanki mata ce da gaske, waɗanda suka ƙi mazansu da ’ya’yansu. Mahaifiyarki mutuniyar Hitti ce, mahaifinki kuma mutumin Amoriyawa ne. 46 Babbar ’yar’uwarki mutuniyar Samariya ce, wadda take zaune da ’ya’yanta mata wajen arewa da ke; ƙanuwarki ita ce Sodom wadda take zaune kudu da ke tare da ’ya’yanta mata. 47 Ba ki bi hanyoyinsu da abubuwansu na banƙyama kaɗai ba, sai ka ce wannan ya yi miki kaɗan, amma kin lalace fiye da su. 48 Muddin in raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ’yar’uwarki Sodom da ’ya’yanta mata ba su yi abin da ’ya’yanki mata suka yi ba.
49 “ ‘To, fa, ga zunubin ’yar’uwarki Sodom. Ita da ’ya’yanta mata sun yi girman kai, sun ƙoshi fiye da kima kuma ba su kula da wani abu ba; ba su taimaki matalauta da kuma masu bukata ba. 50 Su masu girman kai ne kuma suka aikata abubuwa masu banƙyama a gabana. Saboda haka na kau da su kamar yadda ka gani. 51 Samariya ba tă aikata ko rabin zunubanki ba. Kin aikata abubuwa masu banƙyama fiye da su, suka kuma sa ’yan’uwanki mata suka zama kamar masu adalci ta wurin dukan waɗannan abubuwa da kika aikata. 52 Ki sha kunyarki, gama kin yi rangwame wa ’yan’uwanki mata. Saboda zunubanki sun yi muni fiye da nasu, sai suka zama kamar sun fi ki adalci. Saboda haka, ki sha kunya ki kuma sha ƙasƙancinki, gama kin sa ’yan’uwanki mata suka zama kamar su masu adalci ne.
53 “ ‘Amma fa, zan komo da nasarar Sodom da ’ya’yanta mata da ta Samariya da ’ya’yanta mata, nasararki kuma tare da su, 54 domin ki sha ƙasƙancinki ki kuma sha kunyar dukan abin da kika aikata ta wurin ta’azantar da su. 55 ’Yan’uwanki kuwa, Sodom da ’ya’yanta mata da Samariya tare da ’ya’yanta mata, za su koma kamar yadda suke a dā; ke kuma da ’ya’yanki mata za ku koma kamar yadda kike a dā. 56 Ba za ki ma iya ambaci ’yar’uwarki Sodom a ranar fariyarki ba, 57 kafin a tone muguntarki. Ko da ma haka, yanzu ’ya’yan Arameyawa mata da dukan maƙwabtanta da kuma ’ya’yan Filistiyawa mata suna miki dariyar, dukan waɗanda suke kewaye da ke da suka rena ki. 58 Za ki ɗauki hakkin lalatarki da kuma ayyukanki masu banƙyama, in ji Ubangiji.
59 “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan hukunta kamar yadda ya dace da ke, domin kin ƙyale rantsuwana ta wurin karya alkawari. 60 Duk da haka zan tuna da alkawarin da na yi da ke a kwanakin ƙuruciyarki, zan kuma kafa madawwamin alkawari da ke. 61 Sa’an nan za ki tuna da hanyoyinki ki kuma ji kunya sa’ad da kika karɓi ’yan’uwanki mata, waɗanda suka girme ki da kuma waɗanda kika girme su. Zan ba da su kamar ’ya’ya mata gare ki, amma ba bisa alkawarina da ke ba. 62 Ta haka zan kafa alkawarina da ke, za ki kuma san cewa ni ne Ubangiji. 63 Sa’an nan, sa’ad da na yi kafara saboda ke domin dukan abin da kika aikata, za ki tuna ki kuma ji kunya har ki kāsa buɗe bakinki saboda kunya, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
*16:6 Kaɗan cikin rubuce-rubucen Ibraniyanci, Seftuwajin, da kuma Siriyak; yawancin rubuce-rubucen Ibraniyanci na da “Ki rayu!” Kuma yayinda kike kwance cikin jininki na ce miki, “Ki rayu!”
†16:7 Ko kuwa kika zama budurwa
‡16:21 Ko kuwa kika kuma sa suka wuce ta cikin wuta
§16:29 Ko kuwa Kaldiya
*16:36 Ko kuwa sha’awar