16
Hagar da Ishmayel
1 To, Saira, matar Abram, ba tă haifa masa ’ya’ya ba. Amma tana da wata baiwa mutuniyar Masar mai suna Hagar, 2 saboda haka sai ta ce wa Abram, “Ubangiji ya hana mini haihuwar ’ya’ya. Tafi ka kwana da baiwata; wataƙila in sami iyali ta wurinta.”
Abram kuwa ya yarda da abin da Saira ta faɗa. 3 Saboda haka bayan Abram ya yi zama a Kan’ana shekaru goma, Saira matarsa ta ɗauki Hagar baiwarta ta ba wa mijinta tă zama matarsa. 4 Abram kuwa ya kwana da Hagar, ta kuma yi ciki.
Sa’ad da Hagar ta gane tana da ciki, sai ta fara rena uwargijiyarta. 5 Sai Saira ta ce wa Abram, “Kai ne da alhakin wahalan nan da nake sha. Na sa baiwata a hannunka, yanzu da ta sani tana da ciki, sai ta fara rena ni. Bari Ubangiji yă shari’anta tsakanina da kai.”
6 Abram ya ce, “Baiwarki tana a hannunki? Ki yi da ita yadda kika ga ya fi kyau.” Sai Saira ta wulaƙanta Hagar; saboda haka ta gudu daga gare ta.
7 Mala’ikan Ubangiji ya sami Hagar kusa da maɓulɓula a jeji, ita ce maɓulɓular da take gefen hanya zuwa Shur. 8 Ya kuma ce mata, “Hagar, baiwar Saira, daga ina kika fito, kuma ina za ki?”
Ta amsa ta ce, “Ina gudu ne daga wurin uwargijiyata Saira.”
9 Sai mala’ikan Ubangiji ya ce mata, “Koma wurin uwargijiyarki Saira, ki yi mata biyayya.” 10 Mala’ikan ya ƙara da cewa, “Zan ƙara zuriyarki har su yi yawan da ba wanda zai iya lasafta su.”
11 Mala’ikan Ubangiji ya kuma ce mata,
“Ga shi kina da ciki
za ki kuwa haifi ɗa.
Za ki ba shi suna Ishmayel,*Ishmayel yana nufin Allah yana ji.
gama Ubangiji ya ga wahalarki.
12 Zai zama mutum mai halin jakin jeji.
Hannunsa zai yi gāba da kowa,
hannun kowa kuma zai yi gāba da shi.
Zai yi zama gāba
ga dukan ’yan’uwansa.”
13 Sai ta ba wa Ubangiji wanda ya yi magana da ita, wannan suna. “Kai Allah ne wanda yake ganina,” gama ta ce, “Yanzu na ga wanda yake ganina.” 14 Shi ya sa ake kira rijiyar Beyer-Lahai-Royi†Beyer-Lahai-Royi yana nufin rijiyar Mai Rai wanda yake ganina. tana nan har yanzu, tsakanin Kadesh da Bered.
15 Haka fa Hagar ta haifa wa Abram ɗa, Abram kuwa ya ba da suna Ishmayel ga ɗan da ta haifa. 16 Abram yana da shekaru 86 sa’ad da Hagar ta haifa masa Ishmayel.