8
Babban firist na sabuwar yarjejjeniya
1 Abin da muke magana a nan shi ne, muna da irin wannan babban firist, wanda ya zauna a hannun dama na kursiyin Maɗaukaki a sama, 2 wanda yake hidima a cikin wuri mai tsarki, tabanakul na gaskiya wanda Ubangiji ne ya kafa, ba mutum ba.
3 Da yake dole kowane babban firist da aka naɗa yă miƙa baye-baye da hadayu, haka ma wannan ya bukaci yă kasance da abin da zai miƙa. 4 Da a ce yana a duniya ne, da bai zama firist ba, domin a nan akwai mutanen da doka ta naɗa don su miƙa baye-baye. 5 Suna hidima a cikin tsattsarkan wuri wanda yake hoto da kuma siffar abin da yake cikin sama. Shi ya sa aka gargaɗi Musa sa’ad da yana dab da gina tabanakul cewa, “Ka lura fa, ka yi kome daidai bisa ga zānen da aka nuna maka a kan dutsen.”*Fit 25.40 6 Amma hidimar da Yesu ya karɓa tana da fifiko a kan tasu, kamar yadda alkawarin da shi ne yake matsakanci ya fi na dā fifiko nesa, an kuma kafa shi a kan alkawura mafi kyau.
7 Gama da a ce alkawari na fari ba shi da wani laifi, da ba sai an sāke neman wani ba. 8 Amma Allah ya sami mutane da laifi†Za a fassara waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā laifi ya kuma ce wa mutane. ya ce,
“Ina gaya muku lokaci yana zuwa,
sa’ad da zan yi sabon alkawari
da gidan Isra’ila
da kuma gidan Yahuda.
9 Ba zai zama kamar irin alkawarin
da na yi da kakanni-kakanninsu
sa’ad da na kama hannunsu
don in fitar da su daga Masar ba,
domin ba su yi aminci da alkawarina ba,
sai na juya musu baya,
in ji Ubangiji.
10 Wannan shi ne alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila,
bayan lokacin nan,
in ji Ubangiji.
Zan sa dokokina a cikin zukatansu,
in kuma rubuta su a kan zukatansu.
Zan zama Allahnsu,
su kuwa za su zama mutanena.
11 Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa ba,
balle mutum yă ce wa ɗan’uwansa, ‘Ka san Ubangiji,’
domin dukansu za su san ni,
daga ƙaraminsu zuwa babba.
12 Gama zan gafarta muguntarsu
ba zan kuma ƙara tuna da zunubansu ba.”‡Irm 31.31-34
13 Ta wurin kira wannan alkawari “sabo,” ya mai da na farin tsoho ke nan; abin da yake tsoho yana kuma daɗa tsufa, zai shuɗe nan ba da daɗewa ba.