8
Isra’ila za tă girbe guguwa
“Ka sa kakaki a leɓunanka!
Gaggafa tana a bisan gidan Ubangiji
domin mutane sun tā da alkawarina
suka kuma tayar wa dokata.
Isra’ila ta yi mini kuka,
‘Ya Allahnmu, mun yarda da kai!’
Amma Isra’ila sun ƙi abin da yake mai kyau;
abokin gāba zai fafare su.
Suna naɗa sarakuna, ba da izinina ba;
sun zaɓa shugabanni ba da yardanta ba.
Da azurfa da zinariya
sun ƙera gumaka wa kansu
wanda zai kai zuwa ga hallakarsu.
Ku zubar da gunkin maraƙinku, ya Samariya!
Fushina yana ƙuna a kansu.
Sai yaushe za su rabu da gumaka?
Su daga Isra’ila ne!
Wannan maraƙi, mai aikin hannu ne ya yi shi;
gunki ne ba Allah ba.
Za a farfashe shi kucu-kucu,
waccan maraƙin Samariya.
 
“Gama sun shuka iska
don haka za su girbe guguwa.
Hatsin da yake tsaye ba shi da kai,
ba zai yi tsaba ba.
Ko da ya yi tsaba ma,
baƙi ne za su ci.
An haɗiye Isra’ila;
yanzu tana cikin al’ummai
kamar abin da ba shi da amfani.
Gama sun haura zuwa Assuriya
kamar jakin jejin da yake yawo shi kaɗai.
Efraim ya sayar da kansa ga maza.
10 Ko da yake sun sayar da kansu a cikin al’ummai,
yanzu zan tattara su wuri ɗaya.
Za su fara lalacewa
a ƙarƙashi danniyar babban sarki.
 
11 “Ko da yake Efraim ya gina bagadai masu yawa don hadayun zunubi,
waɗannan sun zama bagade don yin zunubi.
12 Na rubuta musu abubuwa masu yawa na dokata,
amma suka ɗauke su tamƙar wani baƙon abu ne.
13 Suna miƙa hadayun da aka ba ni
su kuma ci nama,
amma Ubangiji ba ya jin daɗinsu.
Yanzu zai tuna da muguntarsu
yă kuma hukunta zunubansu.
Za su koma Masar.
14 Isra’ila ya manta da Mahaliccinsa
ya kuma gina fadodi;
Yahuda ya gina katanga a yawancin garuruwansa.
Amma zan aiko da wuta a bisa biranensu
da zai cinye kagaransu.”