7
Alamar Immanuwel
Sa’ad da Ahaz ɗan Yotam, ɗan Uzziya, yake sarkin Yahuda, Sarki Rezin na Aram da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su yaƙi Urushalima, amma ba su iya cinta da yaƙi ba.
Sai fa aka faɗa wa gidan Dawuda cewa, “Aram ya haɗa kansa*Ko kuwa ya kafa sansani a da Efraim”; saboda haka zuciyar Ahaz da ta mutanensa suka firgita, sai ka ce itatuwa a kurmin da iska ta girgiza.
Sai Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Fita, kai da ɗanka Sheyar-Yashub,Sheyar-Yashub yana nufin raguwa za tă komo. don ku sadu da Ahaz a ƙarshen wuriyar da take kawo ruwa daga Tafkin Tudu, a hanyar Filin Mai Wanki. Ka faɗa masa, ‘Ka yi hankali, ka natsu kada kuma ka ji tsoro ko ka damu, kada ka ji tsoron fushin sarki Rezin da na Aram da na ɗan Remaliya, ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin ’yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba. Aram, Efraim da ɗan Remaliya sun ƙulla maƙarƙashiya, suna cewa, “Bari mu kai wa Yahuda hari; bari mu yayyage su mu rarraba su a tsakaninmu, mu naɗa Tabeyel sarki a kansu.” Duk da haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce,
“ ‘Ba zai faru ba,
ba zai auku ba,
gama kan Aram shi ne Damaskus,
kan Damaskus kuma kawai shi ne Rezin.
Cikin shekaru sittin da biyar
za a wargaje Efraim har ba za tă iya rayuwa ta zama al’umma ba.
Kan Efraim shi ne Samariya,
kan Samariya kuma kawai shi ne ɗan Remaliya.
In ba ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiyarku ba,
ba za ku dawwama ba.’ ”
10 Ubangiji ya kuma yi magana wa Ahaz ya ce, 11 “Ka roƙi Ubangiji Allahnka yă ba ka alama, ko daga zurfafa masu zurfi ko kuwa daga can cikin sama.”
12 Amma Ahaz ya ce, “Ba zan nema ba; ba zan gwada Ubangiji ba.”
13 Sa’an nan Ishaya ya ce, “To, ku saurara, ya ku gidan Dawuda! Abin kirki kuke yi ne da kuka ƙure haƙurin jama’a? Ko haƙurin Allah ne kuma kuke so ku ƙure? 14 Saboda haka Ubangiji kansa zai ba ku alama. Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, za tă kuwa kira shi Immanuwel. 15 In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa. 16 Amma kafin yaron yă isa yanke shawara yă ƙi abin da yake mummuna, yă zaɓi abin da yake nagari, ƙasashen sarakunan nan biyu da kuke tsoro za su zama kango. 17 Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama’arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Efraim daga na Yahuda, zai kawo sarkin Assuriya.”
18 A wannan rana Ubangiji zai yi feɗuwa yă kira ƙudaje daga rafuffuka masu nisa na Masar da kuma ƙudan zuma daga ƙasar Assuriya. 19 Za su zo su mamaye kwazazzabai da kogwanni cikin duwatsu, a kan dukan ƙayayyuwa da dukan rammukan ruwa.
20 A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da rezan da aka yi haya daga ƙetaren Kogi,Wato, Yuferites. sarkin Assuriya ke nan, yă aske kanku da gashin ƙafafunku, zai kuma aske gemunku. 21 A ranar, mutum zai bar karsana ɗaya da awaki biyu da rai. 22 Kuma saboda yalwa madarar da suke bayarwa, zai kasance da madarar da zai sha. Dukan waɗanda suka rage a ƙasar za su sha madara da zuma. 23 A wannan rana, a kowane wuri inda akwai kuringa dubu da kuɗinsu ya kai shekel dubu na azurfa, ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne kawai za su kasance a can. 24 Mutane za su je can da baka da kibiyoyi, gama ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne za su rufe ƙasar. 25 Game da dukan tuddai da dā ake nome da garemani kuwa, ba za ku ƙara je wurin ba saboda tsoron ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya; za su zama wuraren da ake kai shanu a sake su su yi ta yawo da kansu, tumaki kuma su yi ta gudu.

*7:2 Ko kuwa ya kafa sansani a

7:3 Sheyar-Yashub yana nufin raguwa za tă komo.

7:20 Wato, Yuferites.