21
Annabci a kan Babilon
Abin da Allah ya faɗa game da Hamada da take kusa da Teku.
Kamar guguwa mai share cikin ƙasar kudu,
mai hari ya zo daga hamada,
daga ƙasar mai banrazana.
 
An nuna mini mugun wahayi,
mai bashewa ya bashe, mai washewa ya washe.
Elam, ki yi yaƙi! Mediya, ki yi kwanto!
Zan kawo ƙarshen dukan nishe-nishen da ta jawo.
 
Game da wannan jikina yana ciwo,
zafi ya kama ni, kamar na mace mai naƙuda;
na razana game da abin da na ji,
na yi mamakin abin da na gani.
Gabana tana ta fāɗuwa,
tsoro ya sa ina rawan jiki;
hasken da nake marmari
ya zo da razana gare ni.
 
Sun shirya teburori,
sun shimfiɗa dardumai,
sun ci, sun sha!
Tashi, ku hafsoshi,
sa mai a garkuwoyi!
Ga abin da mai girma ya ce mini,
“Tafi, ka sa mai tsaro
ka kuma sa ya ba da rahoton abin da ya gani.
Sa’ad da ya ga kekunan yaƙi
tare da ƙungiyoyin dawakai,
mahaya a kan jakuna,
ko mahaya a kan raƙuma,
to, fa ya zauna a faɗake,
ya kintsa sosai.”
Mai tsaron kuma ya yi ihu,
“Kowace rana, ranka yă daɗe, nakan tsaya a hasumiyar tsaro;
kowane dare nakan tsaya a wurin aikina.
Duba, ga wani mutum tafe a keken yaƙin
tare da ƙungiyar dawakai.
Ya kuma mayar da amsa,
‘Babilon ta fāɗi, ta fāɗi!
Dukan siffofin allolinta
kwance a ragargaje a ƙasa!’ ”
 
10 Ya mutanena, an ragargaje ku a masussuka,
na faɗa muku abin da na ji
daga Ubangiji Maɗaukaki,
daga Allah na Isra’ila.
Annabci a kan Edom
11 Abin da Allah ya faɗa game da Duma,*Duma yana nufin shiru Ko kuwa natsattse, wani sunan Edom.
Wani ya kira ni daga Seyir,
“Mai tsaro, me ya rage a daren?
Mai tsaro, me ya rage a daren?”
12 Mai tsaro ya amsa,
“Safiya ta gabato, haka kuma dare.
In za ka yi tambaya, to, yi tambaya;
sai ka sāke zuwa, ka tambaya.”
Annabci a kan Arabiya
13 Abin da Allah ya faɗa game da Arabiya.
Ku ayarin Dedanawa,
ku da kuka sauka a jejin Arabiya,
14 ku kawo ruwa don ƙishirwa;
ku da kuke zama a Tema,
ku kawo abinci don masu gudun hijira.
15 Sun gudu daga takobi,
daga takobin da aka janye,
daga bakan da aka tanƙware
da kuma daga zafin yaƙi.
16 Ga abin da mai girma ya ce mini, “Cikin shekara ɗaya, kamar yadda bawan da aka bautar da shi bisa ga yarjejjeniya zai lissafta, dukan sojojin Kedar za su zo ga ƙarshe. 17 Waɗanda suka yi rai na maharba, jarumawan Kedar, za su zama kaɗan.” Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa.

*21:11 Duma yana nufin shiru Ko kuwa natsattse, wani sunan Edom.