41
Mai taimakon Isra’ila
1 “Ku yi shiru a gabana, ku tsibirai!
Bari al’ummai su sabunta ƙarfinsu!
Bari su zo gaba su yi magana;
bari mu sadu a wurin shari’a.
2 “Wa ya zuga wannan daga gabas,
yana kiransa cikin adalci ga yin hidima?*Ko kuwa / wanda nasara ke samunsa a kowane mataki
Ya miƙa masa al’ummai
ya kuma yi nasara da sarakuna a gabansa.
Ya mai da su ƙura da takobinsa,
zuwa inda iska ke hurawa ta wurin bugun da ya yi musu.
3 Ya fafare su ya kuma yi tafiyarsa lafiya ƙalau,
a hanyar da ƙafafunsa ba su taɓa bi ba.
4 Wane ne ya taɓa yin haka ya kuma sa ya faru,
yana kira ga tsararraki daga farko?
Ni, Ubangiji ina can tun farkonsu
ni kuma ina can har ƙarshe, Ni ne shi.”
5 Tsibirai sun gan shi suka kuma ji tsoro;
iyakokin duniya sun yi rawar jiki.
Suka kusato suka kuma zo gaba;
6 kowa na taimakon wani
yana ce wa ɗan’uwansa, “Ka ƙarfafa!”
7 Masassaƙi yakan ƙarfafa maƙerin zinariya,
kuma shi mai gyara da guduma ya yi sumul
yakan ƙarfafa mai harhaɗawa.
Ya ce game da haɗin, “Ya yi kyau.”
Yakan buga ƙusoshi su riƙe gunkin don kada yă fāɗi.
8 “Amma kai, ya Isra’ila, bawana,
Yaƙub, wanda na zaɓa,
zuriyar Ibrahim abokina,
9 na ɗauke ka daga iyakar duniya,
daga kusurwoyi masu nesa na kira ka.
Na ce, ‘Kai bawana ne’;
na zaɓe ka ban kuwa ƙi ka ba.
10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;
kada ka karai, gama ni ne Allahnka.
Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;
zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.
11 “Duk wanda ya yi fushi da kai
tabbatacce zai sha kunya da ƙasƙanci;
waɗanda suka yi hamayya da kai
za su zama kamar ba kome ba su kuma hallaka.
12 Ko ka nemi abokan gābanka,
ba za ka same su ba.
Waɗanda suke yaƙi da kai
za su zama kamar ba kome ba.
13 Gama ni ne Ubangiji Allahnka,
wanda ya riƙe ka da hannun damana
ya kuma ce maka, Kada ka ji tsoro;
zan taimake ka.
14 Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub marar ƙarfi,
ya ƙaramin Isra’ila,
gama ni kaina zan taimake ka,” in ji Ubangiji,
Mai Fansarka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
15 “Duba, zan sa ka cikin abin sussuka,
saboda kuma mai kaifi mai haƙora da yawa.
Za ka yi sussukar duwatsu ka ragargaza su,
ka kuma farfashe tuddai su zama kamar yayi.
16 Za ka tankaɗe su, iska kuma ta kwashe su,
guguwa kuma za tă warwatsa su.
Amma za ka yi farin ciki a cikin Ubangiji
ka kuma ɗaukaka a cikin Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
17 “Matalauta da mabukata suna neman ruwa,
amma babu kome;
harsunansu sun bushe saboda ƙishi.
Amma Ni Ubangiji zan amsa musu;
Ni, Allah na Isra’ila, ba zan yashe su ba.
18 Zan sa koguna su malalo a ƙeƙasassun tuddai,
maɓulɓulan ruwa kuma a kwaruruka.
Zan mai da hamada tafkunan ruwa,
busasshiyar ƙasa kuma ta zama maɓulɓulan ruwa.
19 Zan sa a hamada ta tsiro da
al’ul da itacen ƙirya, da itacen ci-zaƙi, da zaitun.
Zan sa itace mai girma a ƙasashe masu sanyi ya tsiro a ƙeƙasasshiyar ƙasa,
tare da fir da kuma saifires,
20 don mutane su gani su kuma sani,
su lura su kuma fahimci,
cewa hannun Ubangiji ne ya aikata haka,
cewa Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya sa abin ya faru.
21 “Ka gabatar da damuwarka,” in ji Ubangiji.
“Ka kawo gardandaminka,” in ji Sarki na Yaƙub.
22 “Ka shigar da gumakanka don su faɗa mana
abin da zai faru.
Faɗa mana abubuwan da suka riga suka faru,
domin mu lura da su
mu kuma san abin da zai faru a ƙarshe.
Ko kuwa ku furta mana abubuwan da za su faru,
23 faɗa mana abin da nan gaba ta ƙunsa,
don mu san cewa ku alloli ne.
Ku yi wani abu, mai kyau ko mummuna,
don mu ji tsoro da fargaba.
24 Amma ku ba kome ba ne
kuma ayyukanku banza da wofi ne;
duk wanda ya zaɓe ku abin ƙyama ne.
25 “Na zuga wani daga arewa, ya kuwa zo,
wani daga inda rana ke fitowa wanda yake kira bisa sunana.
Yana takawa a kan masu mulki kamar da taɓarya,
sai ka ce maginin tukwane yana taka laka.
26 Wa ya faɗi wannan tun daga farko, don mu sani,
ko kafin ya faru, don mu ce, ‘Ya faɗi daidai’?
Ba wanda ya faɗa wannan,
ba wanda ya riga faɗe shi,
ba wanda ya ji wata magana daga gare ku.
27 Ni ne na farkon da ya ce wa Sihiyona, ‘Duba, ga su nan!’
Na ba wa Urushalima saƙon labari mai daɗi.
28 Na duba amma ba kowa
ba wani a cikinsu da zai ba da shawara,
ba wani da zai ba da amsa sa’ad da na tambaye su.
29 Duba, dukansu masu ƙarya ne!
Ayyukansu ba su da riba;
siffofinsu iska ne kawai da ruɗami.