43
Mai Ceto kaɗai na Isra’ila
1 To, fa, ga abin da Ubangiji yana cewa,
shi da ya halicce ka, ya Yaƙub,
shi da ya siffanta ka, ya Isra’ila,
“Kada ka ji tsoro, gama na fanshe ka;
na kira ka da suna; kai nawa ne.
2 Sa’ad da kuka bi ta ruwaye,
zan kasance tare da ku;
sa’ad da kuka bi ta koguna,
ba za su kwashe ku ba.
Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta,
ba za tă ƙone ku ba;
harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.
3 Gama ni ne Ubangiji, Allahnku,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila, Mai Cetonku;
na bayar da Masar don fansa,
Kush da Seba a maimakonku.
4 Da yake ku masu daraja da kuma girma ne a idona,
saboda kuma ina ƙaunarku,
zan ba da mutane a maimakonku,
al’umma kuma domin ranku.
5 Kada ku ji tsoro, gama ina tare da ku;
zan kawo yaranku daga gabas
in kuma tattara ku daga yamma.
6 Zan ce wa arewa, ‘Ku miƙa su!’
Ga kudu kuma, ‘Kada ku riƙe su.’
Kawo ’ya’yana maza daga nesa
’ya’yana mata kuma daga iyakar duniya,
7 kowa da ake kira da sunana,
wanda aka halitta saboda ɗaukakata,
wanda na siffanta na kuma yi.”
8 Jagoranci waɗanda suke da idanu amma suke makafi,
waɗanda suke da kunnuwa amma suke kurame.
9 Dukan al’ummai su taru
mutane kuma su tattaru.
Wane ne a cikinsu ya yi faɗar wannan
ya kuma yi mana shelar abubuwan da suka riga suka faru?
Bari su kawo shaidunsu don su tabbatar cewa sun yi daidai,
don waɗansu su ji su kuma ce, “Gaskiya ne.”
10 “Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji,
“bawana kuma wanda na zaɓa,
saboda ka sani ka kuma gaskata ni
ka kuma fahimci cewa ni ne shi.
Kafin ni babu allahn da aka siffanta,
ba kuwa za a yi wani a bayana ba.
11 Ni kaɗai, ni ne Ubangiji,
kuma in ban da ni babu wani mai ceto.
12 Na bayyana na ceci na kuma furta,
Ni ne, ba wani baƙon allah a cikinku.
Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji, “cewa ni ne Allah.
13 I, kuma tun fil azal ni ne shi.
Babu wani da zai amshi daga hannuna.
Sa’ad da na aikata, wa zai iya sauyawa?”
Jinƙan Allah da rashin amincin Isra’ila
14 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila,
“Saboda ku zan aika Babilon
in kawo dukan Babiloniyawa kamar masu gudun hijira,*Ko kuwa Kaldiyawa
a cikin jiragen ruwa waɗanda suke taƙama da su.
15 Ni ne Ubangiji, Mai Tsarkin nan,
Mahaliccin Isra’ila, Sarkinku.”
16 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
shi da ya yi hanya ta cikin teku,
hanya ta cikin manyan ruwaye,
17 wanda ya ja kekunan yaƙi da dawakai,
mayaƙa da kuma ƙarin mayaƙa tare
ya kwantar da su a can, ba kuwa za su ƙara tashi ba,
ya kashe hayaƙi daga lagwani,
18 “Ku manta da abubuwan da suka riga suka faru;
kada ku yi tunanin abin da ya riga ya wuce.
19 Duba, ina yi abu sabo!
Yanzu yana faruwa; ba ku gan shi ba?
Ina yin hanya a cikin hamada
rafuffuka kuma a cikin ƙeƙasasshiyar ƙasa.
20 Namun jeji suna girmama ni,
diloli da mujiyoyi ma haka,
domin na tanada musu ruwa a hamada
da rafuffuka a ƙeƙasasshiyar ƙasa,
don a ba da abin sha ga mutanena, zaɓaɓɓuna,
21 mutanen da na yi saboda kaina
don su furta yabona.
22 “Duk da haka ba ku kira bisa sunana ba, ya Yaƙub,
ba ku gajiyar da kanku saboda ni ba, ya Isra’ila.
23 Ba ku kawo mini tumaki don hadaya ta ƙonewa ba,
balle ku girmama ni da hadayunku.
Ban nawaita muku da hadaya ta gari ba
balle in gajiyar da ku da bukatar turare.
24 Ba ku saya wani turaren kalamus domina ba
ko ku gamshe ni da kitsen hadayunku.
Amma kun nawaita ni da zunubanku
kuka kuma gajiyar da ni da laifofinku.
25 “Ni kaɗai ne na shafe
laifofinku, saboda sunana,
ban kuma ƙara tunawa da zunubanku ba.
26 Ku tunashe ni abin da ya riga ya wuce,
bari mu yi muhawwara wannan batu tare;
ku kawo hujjarku na nuna rashin laifinku.
27 Mahaifinku na farko ya yi zunubi;
masu magana a madadinku suka yi mini tayarwa.
28 Saboda haka zan kunyata manyan baƙi na haikalinku,
zan tura Yaƙub ga hallaka
Isra’ila kuwa yă zama abin dariya.