45
“Ga abin da Ubangiji ya faɗa wa shafaffensa,
ga Sairus, wanda hannun damansa yana riƙe da shi
don yă ci al’ummai a gabansa
ya kuma tuɓe makaman sarakuna,
don yă buɗe ƙofofi a gabansa
don kada a kulle ƙofofi.
Zan sha gabanka
in baje duwatsu;
zan farfashe ƙofofin tagulla
in kuma kakkarye ƙyamaren ƙarfe.
Zan ba ka dukiyar duhu,
arzikin da aka ajiye a asirtattun wurare,
saboda ka san cewa ni ne Ubangiji,
Allah na Isra’ila, wanda ya kira ka da suna.
Saboda sunan Yaƙub bawana,
Isra’ila zaɓaɓɓena,
na kira ka da suna
na ba ka matsayin bangirma,
ko da yake ba ka san ni ba.
Ni ne Ubangiji, kuma babu wani;
in ban da ni babu wani Allah.
Zan ƙarfafa ka,
ko da yake ba ka san ni ba,
saboda daga fitowar rana
har zuwa fāɗuwarta
mutane za su san cewa babu wani in ban da ni.
Ni ne Ubangiji, kuma babu wani.
Ni ne na siffanta haske na kuma halicci duhu,
ni ne nake ba da nasara in kuma jawo bala’i;
ni, Ubangiji ne ke aikata dukan waɗannan abubuwa.
 
“Ku sammai, ku sauko da adalci kamar ruwan sama;
bari gizagizai su zubar da yayyafi kamar adalci.
Bari ƙasa ta buɗe,
bari ceto ya tsiro,
bari adalci ya yi girma tare da shi;
ni, Ubangijine, na sa ya faru.
 
“Kaitonka mai gardama da Wanda ya yi ka,
da wanda yake kasko a cikin kasko a ƙasa.
Yumɓu ya iya ce wa magini,
‘Me kake yi?’
Aikinka na iya cewa,
‘Ba shi da hannuwa’?
10 Kaiton wanda yake cewa mahaifinsa,
‘Me ka manta?’
Ko kuwa ga mahaifiyarsa,
‘Me kin haifa?’
 
11 “Ga abin da Ubangiji yana cewa,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila, da kuma Mahaliccinsa.
Game da abubuwan da ke zuwa,
kun tambaye ni game da ’ya’yana,
ko kuwa kun ba ni umarni game da aikin hannuwana?
12 Ai, ni ne wanda ya yi duniya
na kuma halicci mutum a kanta.
Hannuwana ne sun miƙe sammai;
na umarci rundunar sararin sama.
13 Zan tā da Sairus*Da Ibraniyanci shi cikin adalcina.
Zan sa dukan hanyoyinsa su miƙe.
Zai sāke gina birnina
ya kuma ’yantar da mutanena masu bautar talala,
amma ba don wata haya ko lada ba,
in ji Ubangiji Maɗaukaki.”
14 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Kayayyakin Masar da hajar Kush,Wato, yankin Nilu na Bisa
da waɗannan dogayen Sabenawa,
za su ƙetaro zuwa wurinku
za su kuma zama naku;
za su bi bayanku,
suna zuwa cikin sarƙoƙi.
Za su rusuna a gabanku
su roƙe ku, suna cewa,
‘Tabbas Allah yana tare da ku, babu kuma wani;
babu wani allah.’ ”
 
15 Tabbatacce kai ne Allah wanda ya ɓoye kanka,
Ya Allah da Mai Ceton Isra’ila.
16 Dukan masu yin gumaka za su sha kunya;
za su fita da kunya gaba ɗaya.
17 Amma Ubangiji zai ceci Isra’ila
da madawwamin ceto;
ba za ku sāke shan kunya ko ƙasƙanci ba,
har abada.
 
18 Gama ga abin da Ubangiji yana cewa,
shi da ya halicci sammai,
shi ne Allah;
shi da ya sarrafa ya kuma yi duniya,
ya kafa ta;
bai halicce ta don ta zama ba kome ba,
amma ya yi ta don a zauna a ciki,
ya ce,
“Ni ne Ubangiji,
kuma babu wani.
19 Ban yi magana asirce ba,
daga wani wuri a ƙasar duhu ba;
ban faɗa wa zuriyar Yaƙub,
‘Ku neme ni a banza ba.’
Ni, Ubangiji maganar gaskiya nake yi;
na furta abin da yake daidai.
 
20 “Ku tattaru ku zo;
ku taru, ku masu gudun hijira daga al’ummai.
Masu jahilci ne waɗanda suke ɗaukan gumakan katakai suna yawo,
waɗanda suke addu’a ga allolin da ba za su cece su ba.
21 Furta abin da zai kasance, ku gabatar da shi,
bari su yi shawara tare.
Wa ya faɗa wannan tuntuni,
wa ya yi shelar sa a kwanakin dā?
Ba ni ba ne, Ubangiji?
Kuma babu Allah in ban da ni,
Allah mai adalci da kuma Mai Ceto;
babu wani sai ni.
 
22 “Ku juyo gare ni ku sami ceto,
dukanku iyakokin duniya;
gama ni ne Allah,
kuma babu wani.
23 Da kaina na rantse,
bakina ya furta cikin dukan mutunci
kalmar da ba za a janye ba.
A gabana kowace gwiwa za tă durƙusa;
ta wurina kowane harshe zai rantse.
24 Za su yi zance game da ni su ce, ‘A cikin Ubangiji kaɗai
akwai adalci da kuma ƙarfafawa.’ ”
Duk wanda ya yi fushi da shi
zai zo wurinsa ya kuma sha kunya.
25 Amma a cikin Ubangiji dukan zuriyar Isra’ila
za su sami adalci za su kuwa yi yabo.

*45:13 Da Ibraniyanci shi

45:14 Wato, yankin Nilu na Bisa