54
Ɗaukakar nan gaba ta Sihiyona
“Ki rera, ya ke bakararriya,
ke da ba ki taɓa haihuwa ba;
ki ɓarke da waƙa, ki yi sowa don farin ciki,
ke da ba ki taɓa naƙuda ba;
domin ’ya’yan mace mai kaɗaici sun fi na mai miji yawa,”
in ji Ubangiji.
“Ki fadada wurin tentinki,
ki miƙe labulen tentinki da fāɗi,
kada ki janye;
ƙara tsawon igiyoyinta,
ki kuma ƙara ƙarfin turakunta.
Gama za ki fadada zuwa dama da hagu;
zuriyarki za su kori al’ummai
su kuma zauna a kufan biranensu.
 
“Kada ki ji tsoro; ba za ki sha kunya ba.
Kada ki ji tsoron wulaƙanci, ba za a ƙasƙantar da ke ba.
Za ki manta da kunyar ƙuruciyarki
ba kuwa za ki tuna da zargin zaman gwauruwarki ba.
Gama Mahaliccinki shi ne mijinki,
Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila ne Mai Fansarki;
ana ce da shi Allahn dukan duniya.
Ubangiji zai kira
sai ka ce ke mace ce da aka yashe ta tana kuma damuwa a ranta,
macen da ta yi aure a ƙuruciya,
sai kawai aka ƙi ta,” in ji Allahnki.
“Gama a ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke,
amma da ƙauna mai zurfi zan sāke dawo da ke.
Cikin fushi mai zafi
na ɓoye fuskata daga gare ki na ɗan lokaci,
amma da madawwamin alheri
zan ji tausayinki,”
in ji Ubangiji Mai Fansarki.
 
“A gare ni wannan ya yi kamar kwanakin Nuhu,
sa’ad da na rantse cewa ruwan Nuhu ba za su ƙara rufe duniya ba.
Yanzu fa na rantse ba zan yi fushi da ke ba,
ba zan ƙara tsawata miki kuma ba.
10 Ko da duwatsu za su girgiza
a kuma tumɓuke tuddai,
duk da haka madawwamiyar ƙaunata da nake yi miki ba za tă jijjigu ba
ba kuwa za a kawar da alkawarin salamata ba,”
in ji Ubangiji, wanda ya ji tausayinki.
 
11 “Ya ke birni mai shan azaba, wadda hadari ya bulale ki ba a kuma ta’azantar da ke ba,
zan gina ke da duwatsu turkuwoyis,*Ma’anar kalmar Ibraniyancin nan ba ta da tabbas.
zan kafa harsashenki da duwatsun saffaya.Ko kuwa lafis lazuli
12 Zan gina hasumiyarki da jan yakutu,
ƙofofinki kuma da duwatsu masu haske,
dukan katangarki kuma da duwatsu masu daraja.
13 Ubangiji zai koya wa dukan ’ya’yanki maza,
da girma kuma salamar ’ya’yanki zai zama.
14 Da adalci za a kafa ke.
Zalunci zai yi nesa da ke;
ba za ki kasance da wani abin da za ki ji tsoro ba.
Za a kawar da duk wani abin banrazana;
ba zai yi kusa da ke ba.
15 In wani ya far miki, ba daga wurina ba ne;
duk wanda ya far miki zai miƙa wuya gare ki.
 
16 “Duba, ni ne wanda na halicci maƙeri
wanda yake zuga garwashi ya zama harshen wuta
ya kuma ƙera makamin da ya dace da aikinsa.
Ni ne kuma na halicci mai hallakarwa ya yi ɓarna;
17 ba makamin da aka ƙera don yă cuce ki da zai yi nasara,
za ki kuma mayar da magana ga duk wanda ya zarge ki.
Wannan ne gādon bayin Ubangiji,
kuma wannan ita ce nasararsu daga gare ni,”
in ji Ubangiji.

*54:11 Ma’anar kalmar Ibraniyancin nan ba ta da tabbas.

54:11 Ko kuwa lafis lazuli