61
Shekarar tagomashin Ubangiji
Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina,
domin Ubangiji ya shafe ni
domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta.
Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci,
don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru
in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu
don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji
da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu,
don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki,
in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona,
in maido musu rawani mai kyau
a maimako na toka,
man murna
a maimako na makoki,
da kuma rigar yabo
a maimako na ruhun fid da zuciya.
Za a ce da su itatuwan oak na adalci,
shukin Ubangiji
don bayyana darajarsa.
Za su sāke gina kufai na dā
su raya wurare da aka lalace tun da daɗewa;
za su sabunta biranen da aka rurrushe
da aka lalace tun zamanai masu yawa da suka wuce.
Baƙi za su yi kiwon garkunanki;
baƙi za su yi miki noman gonaki da gonakin inabinki.
Za a kuma kira ku firistocin Ubangiji,
za a kira ku masu hidimar Allahnmu.
Za ku ci wadatar waɗansu al’ummai,
kuma a cikin dukiyarsu za ku yi taƙama.
 
A maimakon kunyarsu
mutanena za su sami rabi riɓi biyu,
a maimakon wulaƙanci
za su yi farin ciki cikin gādonsu;
ta haka za su gāji rabo riɓi biyu a ƙasarsu,
da kuma madawwamin farin ciki zai zama nasu.
 
“Gama ni, Ubangiji, ina ƙaunar adalci;
na ƙi fashi da aikata laifi.
Cikin adalcina zan sāka musu
in kuma yi madawwamin alkawari da su.
Za a san da zuriyarsu a cikin al’ummai
’ya’yansu kuma a cikin mutane.
Dukan waɗanda suka gan su za su san
cewa su mutane ne da Ubangiji ya sa wa albarka.”
 
10 Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji;
raina yana farin ciki a cikin Allahna.
Gama ya suturce ni da rigunan ceto
ya yi mini ado da rigar adalci,
yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist
kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja.
11 Gama kamar yadda ƙasa takan sa tsire-tsire su tohu
lambu kuma ya sa iri ya yi girma,
haka Ubangiji Mai Iko Duka zai sa adalci da yabo
su tsiro a gaban dukan al’ummai.