64
1 Da ma za ka tsage sammai ka sauko,
ai, da duwatsu za su yi rawar jiki a gabanka!
2 Kamar sa’ad da wuta takan ci rassa
ta sa ruwa ya tafasa,
ka sauko ka sanar da sunanka ga abokan gābanka
ka kuma sa al’ummai su yi rawan jiki a gabanka!
3 Gama sa’ad da ka aikata abubuwan bantsoron da ba mu sa tsammani ba,
ka sauko, duwatsu kuma suka yi rawar jiki a gabanka.
4 Tun fil azal babu wanda ya taɓa ji,
babu kunnen da ya gane,
babu idon da ya ga wani Allah in ban da kai,
wanda ya aikata waɗannan al’amura a madadin waɗanda suke sa zuciya a gare shi.
5 Kakan taimaki waɗanda suke murnan yin abin da yake daidai,
waɗanda sukan tuna da hanyoyinka.
Amma sa’ad da muka ci gaba da yin zunubi,
kakan yi fushi.
Ta yaya za mu sami ceto ke nan?
6 Dukanmu mun zama kamar wanda yake marar tsabta,
kuma dukan ayyukanmu masu adalci sun zama kamar ƙazaman tsummoki;
duk mun zama kamar busasshen ganye,
kamar iska haka zunubanmu sukan share mu.
7 Babu wanda yake kira bisa sunanka
ko ya yi ƙoƙarin riƙe ka;
gama ka ɓoye fuskarka daga gare mu
ka kuma sa muka lalace saboda zunubanmu.
8 Duk da haka, Ubangiji, kai ne Ubanmu.
Mu yumɓu ne, kai kuma mai ginin tukwane;
dukanmu aikin hannunka ne.
9 Kada ka yi fushi fiye da kima, ya Ubangiji;
kada ka tuna da zunubanmu har abada.
Da ma ka dube mu, muna roƙonka,
gama dukanmu mutanenka ne.
10 Biranenka masu tsarki sun zama hamada;
har Sihiyona ma ta zama hamada; Urushalima ta zama kango.
11 Haikalinmu mai tsarki da kuma mai daraja, inda kakanninmu suka yabe ka,
an ƙone da wuta,
kuma dukan abubuwan da muke ƙauna sun lalace.
12 Bayan dukan wannan, ya Ubangiji, ba za ka yi wani abu ba?
Za ka yi shiru ka hore mu fiye da kima?