4
Debora
1 Bayan rasuwar Ehud, Isra’ilawa suka sāke aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji. 2 Saboda haka Ubangiji ya sayar da su ga Yabin sarkin Kan’ana wanda yake mulki a Hazor. Shugaban mayaƙansa shi ne Sisera, wanda yake zaune a Haroshet Haggoyim. 3 Domin Yabin sarkin Kan’ana yana da kekunan yaƙin ƙarfe ɗari tara, ya ji wa Isra’ilawa ƙwarai har shekara ashirin, sai suka yi kuka ga Ubangiji, don taimako.
4 A lokacin Debora annabiya, matar Laffidot ce take bi*A al’adance mahukunta da Isra’ila. 5 Takan yi zaman shari’a a ƙarƙashin Dabinon Debora tsakanin Rama da Betel, a ƙasar tudu ta Efraim, Isra’ilawa kuwa sukan zo wurinta don tă yi musu shari’a. 6 Sai ta aika a kira mata Barak ɗan Abinowam daga Kedesh a Naftali, ta ce masa, “Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce ka, ‘Je ka, ka ɗauki mutane Naftali da na Zebulun dubu goma tare da kai, ka yi jagoransu zuwa Dutse Tabor. 7 Zan jawo Sisera, shugaban mayaƙan Yabin, da keken yaƙinsa da mayaƙansa zuwa Kogin Kishon in ba da su a hannunku.’ ”
8 Barak ya ce, “In kika tafi tare da ni, zan tafi; amma in ba ki zo tare da ni ba, ba zan tafi ba.”
9 Debora ta ce, “To, shi ke nan, zan tafi tare da kai. Amma saboda yadda ka ɗauki wannan batun, darajar ba za tă zama taka ba, gama Ubangiji zai ba da Sisera a hannun mace.” Saboda haka Debora ta tafi tare da Barak zuwa Kedesh, 10 a can Barak ya kira Zebulun da Naftali. Mutum dubu goma suka kuma bi shi, Debora kuma tana tare da shi.
11 To, Heber Bakene ya riga ya bar Keniyawa, zuriyar Hobab, ɗan’uwan†Ko kuwa baban matar Musa, ya kafa tentinsa wajen babban itace a Za’anannim kusa da Kedesh.
12 Sa’ad da aka gaya wa Sisera cewa Barak ɗan Abinowam ya haura zuwa dutsen Tabor, 13 sai Sisera ya tattara keken yaƙinsa na ƙarfe ɗari tara wuri ɗaya da dukan mutanen da suke tare da shi daga Haroshet Haggoyim zuwa Kogin Kishon.
14 Sa’an nan Debora ta ce wa Barak, “Je ka! Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da Sisera a hannunka. Ba Ubangiji ya riga ya sha gabanka?” Saboda haka Barak ya gangara zuwa Dutsen Tabor, da mutum dubu goma biye da shi. 15 Da matsowar Barak, Ubangiji ya murƙushe Sisera da dukan sarakunansa da mayaƙansa da takobi, Sisera kuwa ya gudu da ƙafa ya bar keken yaƙinsa. 16 Amma Barak ya bi keken yaƙin da mayaƙan har Haroshet Haggoyim. Aka karkashe dukan mayaƙan Sisera ba ko ɗayan da ya tsira.
17 Amma Sisera, ya tsere da ƙafa zuwa tentin Yayel, matar Heber Bakene, domin suna da abokantaka da Yabin sarkin Hazor da kuma kabilar Heber Bakene.
18 Yayel ta fito ta taryi Sisera ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ka shigo, ka shigo ciki. Kada ka ji tsoro.” Saboda haka ya shiga cikin tentinta, sai ta rufe shi da bargo.
19 Sai ya ce, “Ina roƙonki, ki ba ni ruwa in sha, ina jin ƙishirwa.” Sai ta buɗe salkar madara, ta ba shi ya sha, sai ta kuma rufe shi.
20 Ya ce mata, “Ki tsaya a ƙofar tenti, in wani ya zo ya tambaye ki, ‘Akwai wani a nan?’ Ki ce masa ‘a’a.’ ”
21 Amma Yayel, matar Heber, ta ɗauki turken tenti da guduma ta tafi wurinsa da sauri sa’ad da yake barci saboda gajiya. Ta kafa masa turken a gindin kunnensa ta haɗa shi da ƙasa, har ya mutu.
22 Sai ga Barak mai bin sawun Sisera, Yayel kuwa ta fito don marabtarsa, ta ce, “Shigo, zan nuna maka mutumin da kake nema.” Saboda haka ya shiga ciki tare da ita, sai ga Sisera kwance da turken a gindin kunnensa, matacce.
23 A ranar Allah ya yi kaca-kaca da Yabin, sarkin Kan’ana a gaban Isra’ila. 24 Isra’ilawa kuwa suka ƙara ƙarfi gāba da Yabin, sarkin Kan’aniyawa, har suka hallaka shi.