4
1 “In za ka komo, ya Isra’ila,
ka komo gare ni,”
in ji Ubangiji.
“In ka kau da gumakanka masu banƙyama daga gabana
ba ka ƙara karkace ba,
2 kuma in cikin gaskiya da adalci
ka rantse, ‘Muddin Ubangiji yana raye,’
to al’ummai za su sami albarka ta wurinsa
kuma a cikinsa za su ɗaukaka.”
3 Ga abin da Ubangiji yana ce wa mutanen Yahuda da kuma na Urushalima.
“Ku nome ƙasarku
kuma kada ku yi shuka cikin ƙayayyuwa.
4 Ku yi wa kanku kaciya ga Ubangiji
ku yi wa zukatanku kaciya,
ku mutanen Yahuda da mutanen Urushalima,
in ba haka ba hasalata za tă sauko ta ci kamar wuta
saboda muguntar da kuka aikata
za tă ci ba wanda zai kashe ta.
Masifa daga Arewa
5 “Ku yi shela a Yahuda ku kuma furta a Urushalima ku ce,
‘Ku busa ƙaho a ko’ina a ƙasar!’
Ku tā da murya da ƙarfi ku ce,
‘Ku tattaru!
Bari mu gudu zuwa birane masu katanga!’
6 Ku tā da tuta don zuwa Sihiyona!
Ku gudu ku nemi mafaka ba tare da jinkiri ba!
Gama ina kawowa masifa daga arewa,
mummunan hallaka kuwa.”
7 Zaki ya fito daga ruƙuƙinsa;
mai hallakarwar al’ummai ya kama hanya.
Ya bar wurinsa
don yă lalace ƙasarku.
Garuruwanku za su zama kufai
babu mazauna.
8 Saboda haka ku yafa tufafin makoki,
ku yi makoki da kuka,
gama fushin Ubangiji
bai juye daga gare mu ba.
9 “A wannan rana,” in ji Ubangiji,
“sarki da shugabanni za su fid da zuciya,
firistoci za su razana,
annabawa kuma za su yi mamaki.”
10 Sai na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka, yaya ka ruɗi mutanen nan da kuma Urushalima gaba ɗaya haka ta wurin cewa, ‘Za ku zauna lafiya,’ sa’ad da takobi yana a maƙogwaronmu.”
11 A lokacin za a faɗa wa mutanen nan da kuma Urushalima cewa, “Iska mai zafi daga tuddan hamada za tă hura zuwa wajen mutanena, amma ba don ta sheƙe ko ta rairaye; ba; 12 iska mafificin ƙarfi da ta fito daga gare ni.*Ko kuwa ta zo ta wurin umarnina Yanzu na zartar da hukuncina a kansu.”
13 Duba! Yana zuwa kamar gizagizai,
kekunan yaƙinsa suna zuwa kamar guguwa,
dawakansa sun fi gaggafa sauri.
Kaiton mu! Mun shiga uku!
14 Ya Urushalima, ki wanke mugunta daga zuciyarki ki sami ceto.
Har yaushe za ki zauna riƙe da mugayen tunani?
15 Murya ta shela daga Dan,
tana furtawa masifa daga tuddan Efraim.
16 “A faɗa wa al’ummai wannan,
a furta wannan game Urushalima.
‘Sojoji masu ƙawanya suna zuwa daga ƙasa mai nisa,
suna tā da kirarin yaƙi a kan biranen Yahuda.
17 Sun kewaye ta kamar masu gadin fili,
domin ta yi mini tawaye,’ ”
in ji Ubangiji.
18 “Halinki da ayyukanki
sun kawo wannan a kanki.
Hukuncinki ke nan.
Yana da ɗaci!
Ya soke ki har zuciyarki!”
19 Azabana, azabana!
Ina birgima cikin zafi.
Azabana, azabar zuciyata!
Zuciyata yana bugu a cikina,
Ba zan yi shiru ba.
Gama na ji karan ƙaho;
na ji kirarin yaƙi.
20 Masifa kan masifa;
dukan ƙasar ta zama kufai.
Cikin ɗan lokaci aka rurrushe tentuna nawa,
mafakata ba zato.
21 Har yaushe zan dubi tutar yaƙi
in kuma ji karar ƙaho?
22 “Mutanena wawaye ne;
ba su san ni ba.
Su ’ya’ya ne marasa azanci;
ba su da fahimi.
Suna da dabarar aikata mugunta;
ba su san yadda za su aikata alheri ba.”
23 Na dubi duniya,
na ga cewa marar siffa ce babu kome;
sammai kuma,
haskensu ya tafi.
24 Na dubi duwatsu,
sai na ga suna makyarkyata;
dukan tuddai kuwa suna lilo.
25 Na duba, sai na ga ba kowa;
kowane tsuntsu a sarari da ya tsere.
26 Na duba, sai na ga ƙasa mai amfani ta zama hamada;
dukan garuruwanta sun zama kufai
a gaban Ubangiji, a gaban zafin fushinsa.
27 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Dukan ƙasar za tă zama kufai,
ko da yake ba zan hallaka ta gaba ɗaya ba.
28 Saboda haka duniya za tă yi kuka
sammai a bisa kuma za su yi duhu,
domin na yi magana kuma ba zan fasa ba,
na yanke shawara ba kuwa zan janye ba.”
29 Da jin motsin mahayan dawakai da maharba
kowane gari ya ruga da gudu.
Waɗansu suka shiga kurmi;
waɗansu suka hau cikin duwatsu.
Dukan garuruwan sun fashe tas;
babu wani da yake zama a ciki.
30 Me kike yi, ya wadda aka ragargaza?
Me ya sa kika sanya mulufi
kika sa kayan adon zinariya?
Me ya sa kika sa wa idanunki tozali?
Kin yi kwalliyarki a banza.
Masoyanki sun bar ki;
suna neman ranki.
31 Na ji kuka kamar na mace mai naƙuda,
nishi kamar na wadda take haihuwa ɗanta na fari,
kukan Diyar Sihiyona tana haki, da ƙyar take numfashi,
tana miƙa hannuwanta tana cewa,
“Wayyo ni kaina! Na suma;
an ba da raina ga masu kisana.”