6
Abokan gāba sun kewaye Urushalima
“Ku gudu neman mafaka, mutanen Benyamin!
Ku gudu daga Urushalima!
Ku busa ƙaho a Tekowa!
Ku ba da alama a Bet-Hakkerem!
Gama masifa tana zuwa daga arewa,
mummunar hallaka ce kuwa.
Zan hallaka Diyar Sihiyona,
kyakkyawa da kuma mai laulayi.
Makiyaya da garkunansu za su taso mata;
za su kafa tentunansu kewaye da ita,
kowanne yana lura da sashensa.”
 
“Mu shirya don yaƙi da ita!
Ku tashi, bari mu fāɗa mata da tsakar rana!
Amma, kaito, rana tana fāɗuwa,
inuwar yamma kuwa sai ƙaran tsawo take.
Saboda haka ku tashi, bari mu fāɗa mata da dare
mu rurrushe kagaranta!”
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,
“Ku sassare itatuwan
ku tula ƙasa kewaye da Urushalima.
Dole a hukunta wannan birni;
saboda ya cika da zalunci.
Kamar yadda rijiya takan ba da ruwarta,
haka birnin yake da muguntarsa.
Ana jin labarin rikici da hallaka a cikinsa;
ciwonsa da mikinsa kullum suna a gabana.
Ki ji gargaɗi, ya Urushalima,
ko kuwa in juya daga gare ki
in mai da ƙasarki kufai
don kada wani ya zauna a cikinta.”
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,
“Bari su yi kalan raguwar Isra’ila
a yi kalan sarai yadda ake yi wa inabi;
ka sāke miƙa hannunka a kan rassan,
kamar mai tattara inabi.”
 
10 Ga wa zan yi magana in kuma gargaɗar?
Wa zai saurare ni?
Kunnuwansu sun toshe*Da Ibraniyanci marar kaciya
don kada su ji.
Maganar Ubangiji ta zama abin zargi a gare su;
ba sa jin daɗinta.
11 Amma ina cike da fushin Ubangiji,
kuma ba na iya kannewa.
 
“Ka kwararo shi a kan yara a titi
da kuma a kan samarin da suka tattaru;
za a kama miji da mata a cikinsa,
tsofaffi da suka tsufa tukub.
12 Za a ba da gidajensu ga waɗansu,
tare da gonakinsu da matansu,
sa’ad da na miƙa hannuna
gāba da waɗanda suke zama a ƙasar,”
in ji Ubangiji.
13 “Daga ƙarami zuwa babba,
dukansu masu haɗama ne don riba;
har da annabawa da firistoci,
dukansu suna aikata rashin gaskiya.
14 Sukan ɗaura mikin mutanena
sai ka ce mikin ba shi da matsala.
Suna cewa, ‘Lafiya, Lafiya,’
alhali kuwa ba lafiya.
15 Suna jin kunyar halinsu na banƙyama?
A’a, ba sa jin kunya sam;
ba su ma san yadda za su soke kai ba.
Saboda haka za su fāɗi tare da fāɗaɗɗu;
za a hamɓarar da su sa’ad da na hukunta su,”
in ji Ubangiji.
16 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba;
ku nemi hanyoyin dā,
ku tambaya inda hanyar mai kyau take, ku yi tafiya a kanta,
za ku kuwa sami hutu wa rayukanku.
Amma kun ce, ‘Ba za mu bi ta ba.’
17 Na naɗa muku masu tsaro a kanku na kuma ce,
‘Ku saurari karan ƙaho!’
Amma kuka ce, ‘Ba za mu saurara ba.’
18 Saboda haka ku, ya al’ummai;
ku lura Ya shaidu,
abin da zai faru da su.
19 Ki ji, ya duniya.
Zan kawo masifa a kan waɗannan mutane,
sakayyar ƙulle-ƙullensu,
domin ba su saurari maganata ba
suka kuma ƙi dokata.
20 Babu riba a kawo mini turare daga Sheba
ko rake mai zaƙi daga ƙasa mai nisa?
Ba zan karɓi hadayunku na ƙonawa ba;
ba na jin daɗin sadakokinku.”
21 Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Zan sa abin tuntuɓe gaban mutanena.
Mahaifi da ’ya’yansa maza za su yi tuntuɓe a kan juna;
maƙwabci da abokansa za su hallaka.”
22 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Duba, sojoji suna zuwa
daga ƙasar arewa;
babbar al’umma ce ta yunƙuro
daga iyakokin duniya.
23 Suna riƙe da baka da māshi;
mugaye ne kuma marasa tausayi.
Motsinsu kamar ƙugin teku ne
yayinda suke hawan dawakansu;
suna zuwa a jere kamar wanda ya yi shirin yaƙi
don su fāɗa miki, ya Diyar Sihiyona.”
 
24 Mun ji labari a kansu,
hannuwanmu kuwa suka yi laƙwas.
Azaba ta kama mu,
zafi kamar na mace mai naƙuda.
25 Kada ku fita zuwa gonaki
ko ku yi tafiya a hanyoyi,
gama abokin gāba yana da takobi,
kuma akwai razana ko’ina.
26 Ya mutanena, ku sanya tufafin makoki
ku yi birgima a toka;
ku yi kuka mai zafi
irin wanda akan yi wa ɗa tilo,
gama nan da nan mai hallakarwa
zai auko mana.
 
27 “Na maishe ka mai jarrabawar ƙarfe
mutanena ne kuwa ƙarfen,
don ka lura
ka kuma gwada hanyoyinsu.
28 Su duka masu taurinkai ne, ’yan tawaye,
suna yawo suna baza jita-jita.
Su tagulla ne da ƙarfe;
dukansu lalatattu ne.
29 Mazuga yana zuga da ƙarfi
don yă ƙone dalma da wuta,
amma tacewa yana tafiya a banza;
ba a fitar da mugaye.
30 Ana ce da su azurfar da aka ƙi,
gama Ubangiji ya ƙi su.”

*6:10 Da Ibraniyanci marar kaciya