15
1 Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da Musa da Sama’ila za su tsaya a gabana, zuciyata ba za tă komo ga mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana! Su tafi! 2 In kuma suka tambaye ka, ‘Ina za mu tafi?’ Sai ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“ ‘Waɗanda aka ƙaddara ga mutuwa, ga mutuwa za su;
waɗanda aka ƙaddara ga takobi, ga takobi za su;
waɗanda aka ƙaddara ga yunwa, ga yunwa za su;
waɗanda aka ƙaddara ga zaman bauta, ga zaman bauta za su.’
3 “Zan aika musu da iri masu hallakarwa guda huɗu,” in ji Ubangiji, “takobi zai kashe, karnuka za su kwashe, tsuntsaye da namun jeji kuma su cinye su kuma hallaka. 4 Zan sa su zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya saboda abin da Manasse ɗan Hezekiya sarkin Yahuda ya aikata a Urushalima.
5 “Wa zai ji tausayinki, ya Urushalima?
Wa zai yi makoki dominki?
Wa zai dakata ya tambayi lafiyarki?
6 Kin ƙi ni,” in ji Ubangiji.
“Ki ci gaba da ja da baya.
Ta haka zan ɗibiya hannuwana a kanki in hallaka ki;
ba zan ƙara nuna miki jinƙai ba.
7 Zan sheƙe ki da abin sheƙewa
a ƙofofin birnin ƙasar.
Zan kawo baƙin ciki da hallaka a kan mutanena,
gama ba su canja hanyoyinsu ba.
8 Zan ƙara yawan gwaurayensu
su fi yashin teku yawa.
Da tsakar rana zan kawo mai hallakarwa
a kan iyaye mata na samarinsu;
farat ɗaya zan kawo musu
wahala da razana.
9 Mahaifiya ’ya’ya bakwai za tă suma
ta ja numfashinta na ƙarshe.
Ranarta zai fāɗi tun lokacin bai yi ba;
za tă sha kunya a kuma wulaƙanta ta.
Zan sa a kashe raguwa da takobi
a gaban abokan gābansu,”
in ji Ubangiji.
10 Kaitona, mahaifiyata, da kika haife ni,
mutumin da dukan ƙasa take faɗa take kuma gardama da shi!
Ban ba da bashi ko in ci bashi ba,
duk da haka kowa yana zagina.
11 Ubangiji ya ce,
“Tabbatacce zan cece ka don alheri;
tabbatacce zan sa abokan gābanka su yi roƙo gare ka
a lokacin masifa da kuma lokacin wahala.
12 “Mutum zai iya karye ƙarfe
ƙarfe daga arewa, ko tagulla?
13 “Dukiyarku da arzikinku
zan ba da su ganima, babu tara,
saboda duka zunubanku
ko’ina a ƙasar.
14 Zan bautar da ku ga abokan gābanku
a ƙasar da ba ku sani ba,
gama fushina zai yi ƙuna kamar wuta
da za tă yi ƙuna a kanku.”
15 Ka gane, ya Ubangiji;
ka tuna da ni ka kuma lura da ni.
Ka yi mini ramuwa a kan masu tsananta mini.
Cikin jimirinka, kada ka ɗauke ni;
ka tuna yadda na sha zagi saboda kai.
16 Sa’ad da maganganunka suka zo, na cinye su;
suka zama abin farin ciki zuciyata kuma ta yi murna,
gama ana kirana da sunanka,
Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki.
17 Ban taɓa zauna a cikin ’yan tawaye ba,
ban taɓa yi murna da su ba;
na zauna ni kaɗai domin hannunka yana a kaina
ka kuma sa na cika da haushi.
18 Me ya sa wahalata ba ta ƙarewa
mikina kuma ba ya warkuwa?
Za ka zama mini kamar rafi mai yaudara ne,
kamar maɓulɓulan da ta kafe ne?
19 Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa,
“In ka tuba, zan maido da kai
don ka bauta mini;
in ka ambaci maganganu masu kyau, ba marasa kyau ba,
za ka zama kakakina.
Bari wannan mutane su juyo gare ka,
amma kada ka juye gare su.
20 Zan mai da kai katanga ga wannan mutane,
katanga mai ƙarfi na tagulla;
za su yi yaƙi da kai
amma ba za su yi nasara a kanka ba,
gama ina tare da kai
don in kuɓutar in kuma cece ka,”
in ji Ubangiji.
21 “Zan cece ka daga hannuwan mugaye
in ɓamɓare ka daga hannun marasa tausayi.”