22
Hukunci a kan mugayen sarakunan Yahuda
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ka gangara zuwa fadan sarkin Yahuda ka yi shelar wannan saƙo a can ka ce, ‘Ka ji maganar Ubangiji, ya sarkin Yahuda, kai da kake zaune kan gadon sarautar Dawuda, kai, da fadawanka da mutanenka waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi. Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka yi abin da yake gaskiya da kuma daidai. Ka kuɓutar da wannan da aka yi masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka yi abin da ba daidai ba ko ka cuci baƙo, maraya ko gwauruwa, kuma kada ka zub da jini marar laifi a wannan wuri. Gama in ka lura da bin waɗannan umarnai, to, sarakunan da suke zaune a gadon sarautar Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan fada, suna hawan kekunan yaƙi da dawakai, fadawansu da mutanensu suna musu rakiya. Amma in ba ku kiyaye waɗannan umarnai ba, in ji Ubangiji, na rantse da kaina cewa wannan fada za tă zama kufai.’ ”
Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da wannan fadar sarkin Yahuda,
“Ko da yake kina kamar Gileyad a gare ni,
kamar ƙwanƙolin Lebanon,
tabbatacce zan maishe ki hamada,
kamar garuruwan da ba mazauna.
Zan aika da mai hallakarwa a kanki,
kowane mutum da makamansa,
za su kuma yayyanka gumaguman al’ul na ki masu kyau
su jefa su cikin wuta.
“Mutane daga al’ummai da yawa za su ratsa cikin wannan birni su kuma tambayi juna suna cewa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan babban birni?’ Amsar kuwa za tă zama, ‘Domin sun keta alkawarin Ubangiji Allahnsu, suka yi sujada suka kuma bauta wa waɗansu alloli.’ ”
10 Kada ku yi kuka domin sarkin da ya mutu ko ku yi makoki saboda rashinsa;
a maimako, ku yi kuka mai zafi saboda wanda aka kai zaman bauta,
domin ba zai ƙara dawowa ba
ko ya ƙara ganin ƙasarsa ta haihuwa.
11 Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da Shallum*A kan kuma kira shi Yehoyahaz ɗan Yosiya, wanda ya gāji mahaifinsa a matsayin sarkin Yahuda amma bai bar wurin nan ba, “Ba zai ƙara dawowa ba. 12 Zai mutu a inda suka kai shi zaman bauta; ba zai ƙara ganin wannan ƙasa ba.”
13 “Kaiton wanda ya gina gidansa ta hanyar rashin adalci,
ɗakunansa na sama kuma ta hanyar rashin gaskiya,
yana sa mutanen ƙasarsa suna aiki a banza
ba ya biyansu wahalarsu.
14 Yana cewa, ‘Zan gina wa kaina babban fada
da manyan ɗakuna.’
Ta haka sai ya yi musu manyan tagogi
ya manne musu al’ul
ya yi musu ado kuma da ruwan ja.
 
15 “Wannan zai mai da kai sarki ne
in kana da al’ul a kai a kai?
Mahaifinka bai kasance da abinci da abin sha ba?
Ya yi abin da yake gaskiya da kuma daidai
saboda haka kome ya kasance da lafiya da shi.
16 Ya kāre muradin matalauta da mabukata,
ta haka kome ya tafi masa daidai.
Ba abin da ake nufi da ba san ni ke nan ba?”
In ji Ubangiji.
17 “Amma idanunka da zuciyarka
sun kahu kawai a kan ƙazamar riba,
da a kan zub da jinin marar laifi
da kuma a kan danniya da zalunci.”
18 Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda,
“Ba za su yi kuka dominsa ba,
‘Kaito, ɗan’uwana! Kaito, ’yar’uwata!’
Ba za su yi kuka dominsa ba,
‘Kaito, maigidana! Kaito, darajarsa!’
19 Za a binne shi kamar jaki
za a ja shi a ƙasa a jefar
a bayan ƙofofin Urushalima.”
 
20 “Ka haura zuwa Lebanon ka yi kuka,
bari a ji muryarka a Bashan,
yi kuka daga Abarim,
gama an murƙushe dukan abokanka.
21 Na ja maka kunne sa’ad da kake zama lafiya,
amma sai ka ce, ‘Ba zan saurara ba!’
Wannan halinka ne tun kana matashi;
ba ka yi mini biyayya ba.
22 Iska za tă koro dukan makiyayanka
abokanka kuma za su tafi zaman bauta.
Sa’an nan za ka sha kunya a kuma walaƙanta ka
saboda dukan muguntarka.
23 Kai da kake zama a ‘Lebanon,’Wato, fada a cikin Urushalima (duba 1Sar 7.2)
kai da kake sheƙa a gine-ginen al’ul
za ka yi nishi sa’ad da zafi ya auka maka,
zafi kamar na mace mai naƙuda!
24 “Muddin ina raye,” in ji Ubangiji, “ko kai, YehohiyacinDa Ibraniyanci Koniya, wani suna na Yehohiyacin; haka ma a 28. ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda, ka zama zoben hatimin dama a hannuna na dama, zan kwaɓe ka. 25 Zan ba da kai ga waɗanda suke neman ranka, waɗanda kake tsoro, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga Babiloniyawa. 26 Zan jefar da kai da mahaifiyar da ta haife ka zuwa wata ƙasa, inda babu ɗayanku da aka haifa a wurin, a can kuma za ka mutu. 27 Ba za ka ƙara dawo ƙasar da kake marmarin dawowa ba.”
28 Wannan mutum Yehohiyacin ne da aka rena, fasasshen tukunya,
abin da babu wanda yake so?
Me ya sa za a jefar da shi da ’ya’yansa
a jefar da su a ƙasar da ba su sani ba?
29 Ya ke ƙasa, ƙasa, ƙasa,
ki ji maganar Ubangiji!
30 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Ka rabu da wannan mutum sai ka ce marar ’ya’ya,
mutumin da ba zai yi nasara a rayuwarsa ba,
gama babu zuriyarsa da za tă yi nasara
babu wani da zai zauna a kursiyin Dawuda
ko ya ƙara yin mulkin Yahuda.”

*22:11 A kan kuma kira shi Yehoyahaz

22:23 Wato, fada a cikin Urushalima (duba 1Sar 7.2)

22:24 Da Ibraniyanci Koniya, wani suna na Yehohiyacin; haka ma a 28.