25
Shekaru saba’in na zaman bauta
Magana ta zo wa Irmiya game da dukan mutanen Yahuda a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wadda ta kasance shekara ta fari ta Nebukadnezzar sarkin Babilon. Saboda haka Irmiya annabi ya ce wa dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima. Shekaru ashirin da uku, daga shekara ta goma sha uku ta Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda har zuwa wannan rana, maganar Ubangiji ta zo mini na kuma yi muku magana sau da sau, amma ba ku saurara ba.
Ko da yake Ubangiji ya aika dukan bayinsa annabawa gare ku sau da sau, ba ku saurara ba, ba ku kuma kula ba. Sun ce, “Ku juye yanzu, kowannenku, daga mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku, za ku kuwa iya zauna a ƙasar da Ubangiji ya ba ku da kuma kakanninku har abada abadin. Kada ku bi waɗansu alloli don ku bauta ku kuma yi musu sujada; kada ku tsokane ni in yi fushi da abin da hannuwanku suka yi. Sa’an nan ba zan kawo muku lahani ba.”
“Amma ba ku saurare ni ba,” in ji Ubangiji, “kun tsokane ni da abin da kuka yi da hannuwanku, kuka kuma kawo lahani wa kanku.”
Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Domin kun ƙi ku saurara ga maganata, zan kira dukan mutanen arewa da bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon,” in ji Ubangiji, “zan kuma kawo su su yi gāba da wannan ƙasa da mazaunanta da kuma gāba da dukan al’ummai da suke kewaye. Zan hallaka su sarai in kuma mai da su abin bantsoro da abin dariya, za su kuma zama kufai har abada. 10 Zan kawar da muryoyin farin ciki da murna daga gare su, muryoyin amarya da na ango, ƙarar dutsen niƙa da hasken fitila. 11 Dukan wannan ƙasa za tă zama kango, kuma waɗannan al’ummai za su bauta wa sarkin Babilon shekaru saba’in.
12 “Amma sa’ad da shekaru saba’in ɗin suka cika, zan hukunta sarkin Babilon da kuma al’ummarsa, ƙasar Babiloniyawa, saboda laifinsu,” in ji Ubangiji, “in kuma mai da ita kango har abada. 13 Zan kawo wa wannan ƙasa dukan abubuwan na yi magana a kanta, dukan abubuwan da aka rubuta a wannan littafi, abubuwan da Irmiya kuma ya yi annabci a kan dukan al’ummai. 14 Su kansu al’ummai da sarakuna masu yawa za su bautar da su; zan sāka musu bisa ga ayyukansu da aikin hannuwansu.”
15 Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa mini, “Ka karɓi kwaf ruwan inabin nan na fushina a wurina, ka sa dukan al’umman da na aike ka gare su, su sha. 16 Sa’ad da suka sha, za su yi ta tangaɗi su kuma yi hauka saboda takobin da zan aika a cikinsu.” 17 Saboda haka na karɓi kwaf daga hannun Ubangiji na sa dukan al’ummai waɗanda ya aiko ni wurinsu su sha.
 
18 Urushalima da garuruwan Yahuda, sarakunan da fadawanta, don su mai da su kufai da kuma abin bantsoro da ba’a da la’ana, yadda suke a yau;
19 Fir’auna sarkin Masar, ma’aikatansa, fadawansa da dukan mutanensa, 20 da dukan baƙin da suke can;
dukan sarakunan Uz;
dukan sarakunan Filistiyawa (waɗannan na Ashkelon, Gaza, Ekron da mutanen da aka bari a Ashdod);
21 Edom, Mowab da Ammon;
22 dukan sarakunan Taya da Sidon;
sarakunan bakin teku a ƙetaren teku;
23 Dedan, Tema, Buz da dukan waɗanda suke a manisantan wurare;
24 dukan sarakunan Arabiya da dukan sarakunan baƙin da suke zama a hamada;
25 dukan sarakunan Zimri, Elam da Mediya;
26 da kuma dukan sarakunan arewa, nesa da kuma kusa, bi da bi, dukan mulkokin duniya.
Bayan dukansu kuma, sai sarkin Sheshak ma yă sha.
 
27 “Sa’an nan na faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku sha, ku bugu ku kuma yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku ƙara tashi saboda takobin da zan aiko muku.’ 28 Amma in suka ki su karɓi kwaf ɗin daga hannunka su sha, ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa dole ku sha! 29 Ga shi, na sa masifa tă yi aiki cikin birnin da ake kira da sunana, kuna gani za ku tafi ba hukunci? Ba za ku tafi ba hukunci ba, gama ina kawo wa dukan mazaunan duniya takobi, in ji Ubangiji Maɗaukaki.’
30 “Yanzu ka yi annabcin dukan waɗannan maganganu a kansu ka kuma ce musu,
“ ‘Ubangiji zai yi ruri daga bisa;
zai yi tsawa daga mazauninsa mai tsarki
ya kuma yi ruri da ƙarfi a kan ƙasarsa.
Zai yi ihu kamar waɗanda suke matsin ’ya’yan inabi,
yi ihu a kan dukan waɗanda suke zaune a duniya.
31 Hayaniya za tă taso har iyakar duniya,
gama Ubangiji zai kawo tuhume-tuhume a kan al’ummai;
zai kawo shari’a a kan dukan ’yan adam
ya kuma kashe mugaye da takobi,’ ”
in ji Ubangiji.
32 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,
“Duba! Masifa tana yaɗuwa
daga al’umma zuwa al’umma;
hadari mai girma yana tasowa
daga iyakar duniya.”
33 A lokacin waɗanda Ubangiji ya kashe za su kasance a ko’ina, daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Ba za a yi kuka dominsu, ba za a tattara su don a binne ba, amma za su zama kamar juji da an tsiba a ƙasa.
34 Ku yi kuka ku kuma yi makoki, ku makiyaya;
ku yi ta birgima a ƙura, ku shugabannin garke.
Gama lokacin da za a yanka ku ya zo;
za ku fāɗi ku kuma farfasa kamar tukunyar yumɓu mai kyau.
35 Makiyaya ba za su sami wurin da za su gudu su tafi ba,
shugabannin garke ba za su sami wurin kuɓuta ba.
36 Ji kukan makiyaya,
kururuwan shugabannin garke,
gama Ubangiji yana hallaka wurin kiwo.
37 Rafi mai gudu a hankali zai zama kango
saboda zafin fushin Ubangiji.
38 Kamar zaki zai bar wurin ɓuyarsa,
ƙasarsu kuma za tă zama kufai
saboda takobin masu danniya
da kuma saboda zafin fushin Ubangiji.