14
Yesu ya ta’azantar da almajiransa
“Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri. In kuwa na tafi na shirya muku wuri, sai in dawo in ɗauke ku ku kasance tare da ni don ku kasance inda nake. Ai, kun san hanyar zuwa inda za ni.”
Yesu shi ne hanyar zuwa gun Uba
Sai Toma ya ce masa, “Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, to, ta yaya za mu san hanyar?”
Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina. Da kun san ni, da za ku san Ubana ma. Daga yanzu, kun san shi kun kuma gan shi.”
Filibus ya ce, “Ubangiji, ka nuna mana Uban, wannan kuwa zai biya bukatarmu.”
Yesu ya amsa ya ce, “Ba san ni ba, Filibus, duk da daɗewan nan da na yi tare da ku? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Ka nuna mana Uban’? 10 Ba ka gaskata cewa ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina ba? Kalmomin da nake gaya muku ba na kaina ba ne. Ai, Uban da yake raye a cikina ne yake aikinsa. 11 Ku gaskata ni sa’ad da na ce ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina. Ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan banmamakin su kansu. 12 Gaskiya nake gaya muku, duk wanda yake da bangaskiya gare ni, zai yi abubuwan da ni nake yi. Zai ma yi abubuwa masu girma fiye da waɗannan, don zan tafi wurin Uba. 13 Kuma zan yi duk abin da kuka roƙa cikin sunana, don Ɗan ya kawo ɗaukaka ga Uban. 14 Za ku iya roƙe ni kome a cikin sunana, zan kuwa yi.
Yesu ya yi alkawarin Ruhu Mai Tsarki
15 “In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina. 16 Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada, 17 Ruhun gaskiya. Duniya ba ta iya karɓarsa, don ba ta ganinsa ba ta kuma san shi ba. Amma kun san shi, saboda yana zama tare da ku zai kuma kasance a cikinku. 18 Ba zan bar ku marayu ba; zan zo wurinku. 19 Ba da daɗewa ba, duniya ba za tă ƙara ganina ba, amma za ku gan ni. Don ina raye, ku ma za ku rayu. 20 A ranan nan za ku sani ina cikin Uba, ku kuma kuna cikina, ni kuma ina cikinku. 21 Duk wanda yake da umarnaina yana kuma yin biyayya da su, shi ne wanda yake ƙaunata. Wanda yake ƙaunata kuwa Ubana zai ƙaunace shi, ni ma zan ƙaunace shi, in kuma bayyana kaina gare shi.”
22 Sai Yahuda (ba Yahuda Iskariyot ba) ya ce, “Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu amma ba ga duniya ba?”
23 Yesu ya amsa ya ce, “Duk mai ƙaunata, zai yi biyayya da koyarwata. Ubana zai ƙaunace shi, za mu kuwa zo wurinsa mu zauna tare da shi. 24 Wanda ba ya ƙaunata ba zai yi biyayya da koyarwata ba. Waɗannan kalmomin da kuke ji ba nawa ba ne; na Uba ne da ya aiko ni.
25 “Duk wannan na faɗa ne yayinda ina tare da ku. 26 Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya muku kome, zai kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku. 27 Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.
28 “Kun dai ji na ce, ‘Zan tafi in kuma sāke dawo wurinku.’ In har kuna ƙaunata, za ku yi farin ciki cewa za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni. 29 Na faɗa muku tun kafin yă faru, domin in ya faru, ku gaskata. 30 Ba zan ƙara yi muku magana ba, gama mai mulkin duniyan nan yana zuwa. Ba shi da iko a kaina, 31 amma dole duniya ta koya cewa ina ƙaunar Uba, ina kuma yin yadda Ubana ya umarce ni.
“Ku zo, mu bar nan.