9
Ayuba
1 Sai Ayuba ya amsa,
2 “Lalle, na san wannan gaskiya ne.
Amma ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah?
3 Ko da mutum yana so yă yi gardama da shi,
ba zai taɓa amsa masa ba ko da sau ɗaya cikin dubu.
4 Hikimarsa tana da zurfi, ikonsa yana da yawa.
Wane ne ya taɓa yin faɗa da shi har ya yi nasara?
5 Yana matsar da manyan duwatsu kafin su sani
kuma yana juya su cikin fushinsa.
6 Yana girgiza ƙasa,
yana girgiza harsashenta.
7 Yana magana da rana sai ta ƙi yin haske;
yana hana taurari yin haske.
8 Shi kaɗai ya shimfiɗa sammai
ya kuma yi tafiya a kan raƙuman ruwan teku.
9 Shi ne ya halicci Mafarauci da Kare da Zomo, da Kaza,
da ’Ya’yanta da tarin taurari a sama, da taurarin kudu.
10 Yana yin abubuwan banmamaki waɗanda ba a iya ganewa,
mu’ujizai waɗanda ba a iya ƙirgawa.
11 Ba na iya ganinsa lokacin da ya wuce ni;
ba na sani ya wuce lokacin da ya wuce.
12 Wane ne ya isa yă hana shi in ya ƙwace abu?
Wa zai ce masa, ‘Me kake yi?’
13 Allah ba ya danne fushinsa;
ko dodannin ruwan da ake kira ayarin Rahab ya tattake su.
14 “Ta yaya zan iya yin faɗa da shi?
Ina zan iya samun kalmomin da zan yi gardama da shi?
15 Ko da yake ba ni da laifi, ba zan iya amsa masa ba;
sai dai roƙon jinƙai zan iya yi ga mahukuncina.
16 Ko da na yi kira gare shi ya amsa mini,
ban yarda cewa zai saurare ni ba.
17 Zai sa hadari yă danne ni
yă ƙara mini ciwona ba dalili.
18 Ba zai bari in yi numfashi ba,
sai dai yă ƙara mini azaba.
19 In maganar ƙarfi ne, shi babban mai ƙarfi ne!
In kuma maganar shari’a ne, wa zai kai kararsa?
20 Ko da ni marar ƙarfi ne, bakina ya isa yă sa in zama mai laifi;
in ba ni da laifi, zai sa in yi laifi.
21 “Ko da yake ba ni da laifi,
ban damu da kaina ba;
na rena raina.
22 Ba bambanci; shi ya sa na ce,
‘Yana hallaka marasa laifi da kuma mugaye.’
23 Lokacin da bala’i ya kawo ga mutuwa,
yakan yi dariyar baƙin cikin marasa laifi.
24 Lokacin da ƙasa ta faɗa a hannun mugaye,
yakan rufe idanun masu shari’a.
In ba shi ba wa zai yi wannan?
25 “Kwanakina sun fi mai gudu wucewa da sauri;
suna firiya babu wani abin jin daɗi a cikinsu.
26 Suna wucewa kamar jirgin ruwan da aka yi da kyauro,
kamar jahurma da ta kai wa namanta cafka.
27 ‘In na ce zan manta da abin da yake damu na,
zan yi murmushi in daina nuna ɓacin rai,’
28 duk da haka ina tsoron duk wahalata,
domin na san ba za ka ɗauke ni marar laifi ba.
29 Tun da an riga an ɗauke ni mai laifi,
duk ƙoƙarina a banza yake.
30 Ko da na wanke jikina duka da sabulu,
na wanke hannuwana kuma da soda,
31 duk da haka za ka jefa ni cikin ƙazamin wuri,
yadda ko rigunan jikina ma za su ƙi ni.
32 “Shi ba mutum ba ne kamar ni wanda zan iya amsa masa,
har da za mu yi faɗa da juna a wurin shari’a.
33 In da akwai wanda zai iya shiga tsakaninmu,
ya ɗora hannunsa a kanmu tare,
34 wani wanda zai sa Allah yă daina duka na,
don yă daina ba ni tsoro.
35 Sa’an nan ne zan iya yin magana ba tare da jin tsoronsa ba,
amma a yadda nake a yanzu ba zan iya ba.