16
Ayuba
1 Sai Ayuba ya amsa,
2 “Na ji abubuwa da yawa kamar waɗannan;
dukanku ba ku iya ta’aziyya ba!
3 Dogayen surutanku ba sa ƙare ne?
Me yake sa kuke ta yin waɗannan surutai har kuke cin gaba da yin gardama?
4 Ni ma zan iya yin maganganu kamar yadda kuke yi
in da kuna cikin halin da nake;
zan iya faɗar duk abubuwan da kuke faɗi,
in kaɗa muku kaina.
5 Amma bakina zai ƙarfafa ku;
ta’aziyyar da za tă fito daga bakina za tă kawar muku da ɓacin zuciyarku.
6 “Duk da haka in na yi magana, ba na samun sauƙi;
in ma na yi shiru zafin ba ya tafiya.
7 Ba shakka ya Allah ka gajiyar da ni;
ka ɓata gidana gaba ɗaya.
8 Ka daure ni, ya kuma zama shaida;
yadda na rame sai ƙasusuwa, wannan ya sa ake gani kamar don ni mai zunubi ne shi ya sa.
9 Allah ya kai mini hari ya yi kaca-kaca da ni cikin fushinsa
yana cizon haƙoransa don fushin da yake yi da ni;
ya zura mini ido.
10 Mutane suka buɗe baki suka yi mini riyar reni;
suka yi mini ba’a
suka haɗu suka tayar mini.
11 Allah ya bashe ni ga mugayen mutane,
ya jefa ni hannun mugaye.
12 Dā ina zamana lafiya kome yana tafiya daidai;
amma ya ragargaza ni; ya shaƙe ni a wuya;
ya murƙushe ni na zama abin barata gare shi;
13 maharbansa sun kewaye ni.
Ba tausayi, ya soke ni a ƙodata
har jini ya zuba a ƙasa.
14 Ya ji mini rauni a kai a kai
ya auko mini kamar mai yaƙi.
15 “Ina makoki saye da tsummoki
na ɓoye fuskata a cikin ƙura.
16 Fuskata ta yi ja don kuka
idanuna sun kukumbura;
17 duk da haka hannuwana ba su aikata ɓarna ba
kuma addu’ata mai tsabta ce.
18 “Ya duniya, kada ki ɓoye jinina;
bari yă yi kuka a madadina!
19 Ko yanzu haka shaidata tana sama;
wanda zai tsaya mini yana sama.
20 Shi mai yin roƙo a madadina abokina ne
yayinda nake kuka ga Allah;
21 a madadin mutum ya yi roƙo ga Allah
kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.
22 “Shekaru kaɗan suka rage
in kama hanyar da ba a komawa.