29
1 Ayuba ya ci gaba da jawabinsa,
2 “Da ma ina nan lokacin da ya wuce baya can,
kwanakin da Allah yake lura da ni,
3 lokacin da fitilarsa take haske a kaina
na yi tafiya cikin duhu tare da haskensa.
4 Kwanakin da nake tasowa,
lokacin da abokantakar Allah ta sa wa gidana albarka,
5 lokacin da Maɗaukaki yana tare da ni,
kuma ’ya’yana suna kewaye da ni,
6 lokacin da ake zuba madara a inda nake takawa,
duwatsu kuma suna ɓulɓulo mini man zaitun.
7 “Sa’ad da na je ƙofar birni na zauna
a bainin jama’a,
8 matasan da suka gan ni sukan ja gefe
tsofaffi kuma suka tashi tsaye;
9 sarakuna suka yi shiru
suka rufe bakunansu da hannuwansu;
10 Muryar manya ta yi tsit
harshensu ya manne a rufin bakunansu.
11 Duk wanda ya ji ni ya yaba mini
waɗanda suka gan ni kuma sun amince da ni,
12 domin na ceci matalauta waɗanda suka nemi taimako,
da marasa mahaifi waɗanda ba su da wanda zai taimake su.
13 Mutumin da yake bakin mutuwa ya sa mini albarka.
Na faranta wa gwauruwa zuciya.
14 Na yafa adalci ya zama suturata;
gaskiya ita ce rigata da rawanina.
15 Ni ne idon makafi
kuma ƙafa ga guragu.
16 Ni mahaifi ne ga masu bukata;
na tsaya wa baƙo.
17 Na karya ƙarfin mugaye
na ƙwato waɗanda suke riƙe da haƙoransu.
18 “Na yi tunani cewa, ‘Zan mutu a cikin gidana,
kwanakina da yawa kamar turɓayar ƙasa.
19 Jijiyoyina za su kai cikin ruwa,
kuma raɓa za tă kwanta a rassana dukan dare.
20 Ɗaukakata za tă kasance tare da ni garau,
bakana koyaushe sabo ne a hannuna.’
21 “Mutane suna mai da hankali su saurare ni,
suna yin shiru don su ji shawarata.
22 Bayan da na yi magana, ba su ƙara ce kome ba.
Maganata ta shige su.
23 Sukan jira ni kamar yadda ake jiran ruwan sama.
Sukan sha daga cikin maganganuna kamar mai shan ruwan bazara.
24 Sa’ad da na yi musu murmushi da ƙyar sukan yarda;
hasken fuskata yana da daraja a gare su.
25 Na zaɓar masu inda za su bi na kuma zauna kamar sarkinsu;
na zauna kamar sarki a cikin rundunansu;
ina nan kamar mai yi wa masu makoki ta’aziyya.