33
“Amma yanzu, Ayuba, ka saurari abin da zan ce;
ka sa hankali ga kowane abin da zan faɗa.
Zan yi magana;
kalmomina suna dab da fitowa daga bakina.
Abin da zan faɗa gaskiya ne daga cikin zuciyata;
bakina zai faɗi gaskiyar abin da na sani.
Ruhun Allah ne ya yi ni;
numfashin Maɗaukaki ya ba ni rai.
Ka amsa mini in za ka iya;
ka yi shirin fuskanta ta.
Ni kamar ka nake a gaban Allah;
ni ma daga ƙasa aka yi ni.
Kada ka ji tsorona,
ba abin da zai fi ƙarfinka.
 
“Amma ka faɗa na ji,
na ji daidai abin da ka faɗa,
‘ni mai tsarki ne marar zunubi;
ina da tsabta kuma ba ni da laifi.
10 Duk da haka Allah ya same ni da laifi;
ya ɗauke ni maƙiyinsa,
11 ya daure ƙafafuna da sarƙa;
yana tsaron duk inda na bi.’
 
12 “Amma na gaya maka, a nan ba ka yi daidai ba,
gama Allah ya fi mutum girma.
13 Don me ka yi masa gunaguni
cewa ba ya amsa tambayoyin mutum?
14 Gama Allah yana magana,
yanzu ga wannan hanya, yanzu kuma ga wata hanya
ko da yake ba lalle mutum yă lura ba.
15 A cikin mafarki, cikin wahayi da dare,
sa’ad da barci mai zurfi ya fāɗo a kan mutane
lokacin da suke cikin barci kan gadajensu,
16 mai yiwuwa yă yi musu magana a cikin kunnuwansu
yă razana su da gargaɗinsa,
17 don a juyar da su daga abin da yake yi da ba daidai ba
a kuma hana su daga girman kai,
18 don a kāre su daga fāɗuwa cikin rami,
a kāre su daga hallaka ta wurin takobi.
 
19 “Ko kuma mutum yă sha horo
ta wurin kwanciya da ciwo da rashin jin daɗi cikin ƙasusuwansa,
20 yadda zai ji ƙyamar abinci,
har yă ƙi son abinci mafi daɗi.
21 Naman jikinsa ya lalace ba wani abu mai kyau a ciki
kuma ƙasusuwansa da suke a rufe da tsoka yanzu duk sun fito.
22 Ransa yana matsawa kusa da rami,
ransa kuma kusa da ’yan aikan mutuwa.
23 Duk da haka, in akwai mala’ika a gefensa kamar matsakanci,
ɗaya daga cikin dubu,
da zai gaya wa mutum abin da yake daidai gare shi,
24 yă yi masa alheri yă ce,
‘Kada ka bari yă fāɗa cikin rami,
na samu fansa dominsa.’
25 Sa’an nan fatar jikinsa za tă zama sabuwa kamar ta jariri;
za tă zama kamar lokacin da yake matashi.
26 Ya yi addu’a ga Allah ya kuwa samu alheri a wurinsa,
yana ganin fuskar Allah yana kuma yin sowa don murna;
Allah ya mayar da shi ya zama mai adalci.
27 Sa’an nan sai ya zo wurin, wurin mutane ya ce,
‘Na yi zunubi, na kauce wa abin da yake daidai,
amma ban samu abin da ya kamata in samu ba.
28 Ya fanshi raina daga fāɗawa cikin rami,
kuma zan rayu in ji daɗin hasken.’
 
29 “Allah ya yi wa mutum duk waɗannan,
sau biyu, har ma sau uku.
30 Ya juyo da ransa daga fāɗawa cikin rami,
don hasken rai ya haskaka a kansa.
 
31 “Ka sa hankali da kyau, Ayuba, ka saurare ni;
ka yi shiru zan yi magana.
32 In kana da abin da za ka ce, ka amsa mini;
yi magana, domin ina so in ’yantar da kai.
33 Amma in ba haka ba, sai ka saurare ni;
yi shiru, zan kuma koya maka hikima.”