3
An shari’anta al’ummai
“A waɗancan kwanaki da kuma a wancan lokaci,
sa’ad da zan maido da arzikin Yahuda da Urushalima,
zan tattara dukan al’ummai
in kuma kawo su Kwarin Yehoshafat* Yehoshafat yana nufin Ubangiji ya shari’anta; haka ma a aya 12.
Can zan yi musu shari’a
game da gādona, mutanena Isra’ila,
gama sun warwatsar da mutanena a cikin al’ummai
sun kuma raba ƙasata.
Sun jefa ƙuri’a a kan mutanena
suna kuma sayar da yara maza don karuwanci,
sun sayar da ’yan matan domin ruwan inabi
wanda za su sha.
“Yanzu mene ne damuwarku da ni, ya Taya da Sidon da kuma dukan mazaunan yankunan Filistiya? Kuna ƙoƙari ku sāka mini don abin da na yi ne? In kuna sāka mini ne, to, da gaggawa zan mayar muku da sakayya a kanku. Gama kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe dukiyata mafi kyau kun kai cikin haikalinku. Kun sayar da mutanen Yahuda da na Urushalima ga mutanen Hellenawa, don ku aika da su nesa da ƙasarsu.
“Duba, zan dawo da su daga wuraren da kuka sayar da su, in kuma yi muku abin da kuka yi musu. Zan sayar da ’ya’yanku maza da mata ga mutanen Yahuda, su kuma za su sayar da su ga mutanen Sabenawa, al’umma da take nesa da ku.” Ubangiji ya faɗa.
Ku yi shelar wannan ga al’ummai.
Ku yi shirin yaƙi!
Ku tā da jarumawa!
Bari mayaƙa su ja kusa su kai hari.
10 Ku bubbuge garemaninku su zama takuba
da kuma laujenku su zama māsu.
Bari raunana su ce,
“Ni mai ƙarfi ne!”
11 Ku gaggauta, dukanku al’ummai daga kowane ɓangare,
ku tattaru a can.
 
Ka sauko da mayaƙanka, ya Ubangiji!
 
12 “Bari a tā da dukan al’ummai;
bari su kutsa zuwa Kwarin Yehoshafat
gama a can zan zauna
in shari’anta dukan al’ummai daga kowane ɓangare.
13 Ku fito da lauje,
gama girbi ya nuna.
Ku zo, ku tattaka inabin,
gama wurin matsewar ruwan inabi ya cika
randunan tarawa kuma sun cika har suna zuba,
muguntarsu da girma take!”
 
14 Dubun dubbai
suna a cikin kwarin yanke shawara!
Gama ranar Ubangiji ta yi kusa
a cikin kwarin yanke shawara.
15 Za a duhunta rana da wata,
taurari kuma ba za su ba da haske ba.
16  Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona
tsawa kuma daga Urushalima;
duniya da sararin sama za su yi rawan jiki.
Amma Ubangiji zai zama mafakar mutanensa,
mafaka ga mutanensa Isra’ila.
Albarka domin mutanen Allah
17 “Sa’an nan za ku san cewa ni, Ubangiji Allahnku,
ina zaune a Sihiyona, dutsena mai tsarki.
Urushalima za tă zama mai tsarki;
baƙi ba za su ƙara mamaye ta ba.
 
18 “A wannan rana duwatsu za su ɗiga da sabon ruwan inabi,
tuddai kuma za su malmalo madara;
dukan rafuffukan Yahuda za su yi ta gudano da ruwa.
Maɓulɓula kuma za tă fito daga gidan Ubangiji
haka ma ruwa a kwarin itatuwan ƙirya. Ko kuwa kwarin Shittim
19 Amma Masar za tă zama kango,
Edom kuma hamada marar amfani,
saboda kama-karyar da aka yi wa mutanen Yahuda,
a ƙasar da aka zub da jinin marasa laifi.
20 Za a zauna a Yahuda har abada
Urushalima kuma daga tsara zuwa tsara.
21 Alhakin jininsu, wanda ban gafarta ba,
zan gafarta.”
 
Ubangiji yana zama a Sihiyona!

*3:2 Yehoshafat yana nufin Ubangiji ya shari’anta; haka ma a aya 12.

3:18 Ko kuwa kwarin Shittim