17
An hana cin jini
1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Yi magana da Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji ya umarta. 3 Duk mutumin Isra’ilan da ya yanka sa,*Kalmar Ibraniyanci ta ƙunshi namiji da ta macen sa ne. ɗan rago ko akuya a sansani ko waje da shi 4 a maimakon kawo shi a matsayin hadaya ga Ubangiji a gaban tabanakul na Ubangiji, za a ɗauki wannan mutum a matsayi mai laifin zub da jini, ya zub da jini, kuma dole a raba shi da mutanensa. 5 Wannan ya zama haka saboda Isra’ilawa su kawo wa Ubangiji hadayun da suke yi a filaye. Dole su kawo su ga firist, wato, ga Ubangiji, a ƙofar Tentin Sujada, su miƙa su a matsayin hadayun salama. 6 Firist zai yayyafa jinin a bagaden Ubangiji, a ƙofar Tentin Sujada, yă kuma ƙone kitsen kamar ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. 7 Kada kuma su ƙara yin hadayunsu ga gumaka masu siffar bunsurai waɗanda suka bauta wa. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a gare su wa tsararraki masu zuwa.’
8 “Faɗa musu, ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko wani baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ko sadaka 9 kuma bai kawo shi a ƙofar Tentin Sujada don yă miƙa shi ga Ubangiji ba, dole a raba wannan mutum da mutanensa.
10 “ ‘Duk mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya ci wani jini, zan yi gāba da wannan mutum wanda ya ci jinin, za a kuma raba shi da mutanensa. 11 Gama ran halitta yana a cikin jinin, kuma na ba da shi gare ku don kafara a kan bagade, jini ne yake kafara saboda ran mutum. 12 Saboda haka na ce wa Isra’ilawa, “Babu waninku da zai ci jini, babu wani baƙon da yake zama a cikinku da zai ci jini.”
13 “ ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinku wanda ya ji wa wani dabba ko tsuntsu wanda ake ci ciwo, dole yă tsiyaye jinin yă rufe shi da ƙasa, 14 domin ran kowace halitta yana cikin jini. Shi ya sa na ce wa Isra’ilawa, “Kada ku ci jinin wani halitta, domin ran kowace halitta yana cikin jinin; duk wanda ya ci shi dole a fid da shi.”
15 “ ‘Kowa, ko haifaffe ɗan ƙasa ko baƙo, da ya ci wani abin da aka sami a mace, ko naman jeji ya yayyage, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma; sa’an nan zai tsarkake. 16 Amma in bai wanke rigunansa ya kuma yi wanka ba, alhaki zai kasance a kansa.’ ”