7
Bangaskiyar jarumin Roma
(Mattiyu 8.5-13; Yohanna 4.43-54)
1 Bayan Yesu ya gama gaya wa mutanen dukan waɗannan abubuwa, sai ya shiga Kafarnahum. 2 A can, akwai wani bawan wani jarumin yana ciwo, yana kuma a bakin mutuwa. Maigidansa kuwa yana sonsa sosai. 3 Jarumin sojan ya ji labarin Yesu, sai ya aiki waɗansu dattawan Yahudawa wajensa, yana roƙonsa yă zo yă warkar da bawansa. 4 Da suka isa wurin Yesu, sai suka roƙe shi sosai, suka ce, “Wannan mutum, ai, ya dace a yi masa haka, 5 gama yana ƙaunar al’ummarmu ta Yahudawa, har ya gina majami’armu.” 6 Sai Yesu ya tafi tare da su.
Da ya yi kusa da gidan, sai jarumin nan, ya aiki abokai su ce masa, “Ubangiji, kada ka dami kanka, gama ban isa ka shiga gidana ba. 7 Shi ya sa ban ma ga na isa in zo wurinka ba. Amma ka yi magana kawai, bawana zai warke. 8 Gama ni kaina, mutum ne a ƙarƙashin iko, akwai kuma sojoji a ƙarƙashin ikona. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă tafi, ga wani kuma in ce, ‘Zo nan,’ sai yă zo. Nakan kuma ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai yă yi.”
9 Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki sosai. Ya juya ya wa taron da yake bin sa, “Ina faɗa muku, ban taɓa samun irin bangaskiya mai girma haka ko cikin Isra’ila ba.” 10 Sai mutanen da aka aika, suka koma gida, suka tarar bawan ya warke.
Yesu ya tā da ɗan gwauruwa
11 Ba a daɗe ba, sai Yesu ya tafi wani garin da ake kira Nayin. Almajiransa da taro mai yawa suka tafi tare da shi. 12 Da ya yi kusa da ƙofar garin, sai ga wata gawa ana fitowa da ita. Shi ne ɗa kaɗai ga mahaifiyarsa, ita kuma gwauruwa ce. Taro mai yawa daga garin yana tare da ita. 13 Da Ubangiji ya gan ta, sai ya ji tausayinta ya ce, “Kada ki yi kuka.”
14 Yesu ya je ya taɓa akwatin gawar, sai masu ɗaukarsa suka tsaya cik. Sai ya ce, “Saurayi, na ce maka, tashi!” 15 Sai mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuma ya ba da shi ga mahaifiyarsa.
16 Sai tsoro ya kama su duka, suka yabi Allah, suna cewa, “Babban annabi ya bayyana a cikinmu. Allah ya zo domin yă taimaki mutanensa.” 17 Wannan labarin game da Yesu, ya bazu ko’ina a Yahudiya da kewayenta.
Yesu da Yohanna Mai Baftisma
(Mattiyu 11.1-19)
18 Almajiran Yohanna suka gaya masa dukan waɗannan abubuwa. Sai ya kira biyu daga cikinsu, 19 ya aike su wurin Ubangiji, su tambaya su ce, “Kai ne wanda zai zo, ko kuma mu saurari wani dabam?”
20 Da mutanen suka iso wurin Yesu, sai suka ce, “Yohanna Mai Baftisma ne ya aike mu wurinka, mu yi tambaya, ‘Ko kai ne wanda zai zo, ko kuma mu saurari wani dabam?’ ”
21 A daidai lokacin nan, Yesu ya warkar da mutane da yawa masu ciwo, masu cututtuka, da kuma masu mugayen ruhohi. Ya kuma ba makafi da yawa ganin gari. 22 Sai ya amsa wa almajiran Yohanna ya ce, “Ku koma ku faɗa wa Yohanna abin da kuka ji, da abin da kuka gani. Makafi suna ganin gari, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin bishara. 23 Mai albarka ne mutumin da bai yi shakkar bangaskiyar da yake da ita a kaina ba.”
24 Bayan almajiran Yohanna suka tafi, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna ya ce, “Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne? 25 In ba haka ba, to, me kuka je kallo? Mutum mai sanye da tufafi masu kyau ne? A’a, masu sa kayan tsada da suke cikin annashuwa, ai, a fada suke. 26 Amma me kuka je kallo? Annabi? I, ina kuma faɗa muku, ya ma fi annabi. 27 Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa,
“ ‘Zan aiko da ɗan saƙona yă sha gabanka,
wanda zai shirya hanya, a gabanka.’*Mal 3.1
28 Ina faɗa muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yohanna girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi.”
29 (Dukan mutane, har da masu karɓar haraji, da suka ji kalmomin Yesu, sai suka yarda cewa hanyar Allah gaskiya ce, domin Yohanna ne ya yi musu baftisma. 30 Amma Farisiyawa da masanan dokoki, suka ƙi nufin Allah game da su, domin Yohanna bai yi musu baftisma ba.)
31 Yesu ya ci gaba da cewa, “To, da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Kamar me suke? 32 Suna kama da yaran da suke zama a bakin kasuwa, suna kiran juna, suna cewa,
“ ‘Mun busa muku sarewa,
amma ba ku yi rawa ba,
Mun kuma yi muku waƙar makoki,
ba ku kuma yi kuka ba.’
33 Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo, ba ya cin burodi, ba ya shan ruwan inabi, sai kuka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ 34 Ɗan Mutum ya zo yana ci, yana sha, sai kuka ce, ‘Ga mai yawan ci, mashayi, da kuma abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ 35 Amma akan tabbatar da hikima ta gaskiya bisa ga dukan ’ya’yanta.”
Mace mai zunubi ta shafe wa Yesu turare
36 To, ana nan, sai ɗaya daga cikin Farisiyawa ya gayyaci Yesu cin abincin yamma a gidansa, ya kuwa tafi gidan Bafarisiyen, ya zauna a tebur. 37 Da wata mace wadda ta yi rayuwar zunubi a wannan gari ta ji Yesu yana cin abinci a gidan Bafarisiyen, sai ta kawo ɗan tulun turaren alabasta, 38 ta kuma tsaya daga bayansa, wajen ƙafafunsa tana kuka, sai hawayenta sun fara zuba a ƙafafunsa. Sai ta goge su da gashin kanta, ta sumbace su, sa’an nan ta shafa musu turare.
39 Da Bafarisiyen da ya gayyace shi, ya ga wannan, sai ya ce a ransa, “Da mutumin nan annabi ne, da ya san ko wace ce take taɓansa, da kuma irin macen da take, cewa mai zunubi ce.”
40 Sai Yesu ya ce masa, “Siman, ina da abin da zan faɗa maka.”
Shi kuwa ya ce, “Malam sai ka faɗa.”
41 Yesu ya ce, “An yi waɗansu mutum biyu da suke riƙe bashin mai ba da rance. Ana bin guda dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin. 42 Dukan biyun suka gagara biyansa, sai ya yafe musu. To, a ganinka, wa zai fi ƙaunar mutumin nan?”
43 Siman ya amsa ya ce, “A ganina, wanda aka yafe wa mai yawa ne.”
Sai Yesu ya ce, “Ka faɗa daidai.”
44 Sai ya juya wajen macen, ya ce wa Siman, “Ka ga macen nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwa don ƙafafuna ba, amma ta wanke ƙafafuna da hawayenta, ta kuma goge su da gashin kanta. 45 Ba ka yi mini sumba ba, amma tun shigowata a nan, macen nan ba tă daina sumbar ƙafafuna ba. 46 Ba ka shafa mai a kaina ba, amma ta zubo turare a ƙafafuna.
47 “Saboda haka ina gaya maka, zunubanta masu yawa, an gafarta mata, gama ƙaunarta mai yawa ce. Amma wanda aka gafarta wa kaɗan kuwa, yakan nuna ƙauna kaɗan.”
48 Sai Yesu ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.”
49 Sauran baƙin suka fara ce wa juna, “Wane ne wannan, wanda har yake gafarta zunubai?”
50 Yesu ya ce wa macen, “Bangaskiyarki ta cece ki, ki sauka lafiya.”