16
Misalin manaja mai wayo
Yesu ya ce wa almajiransa, “An yi wani mai arziki wanda aka yi wa manajansa zargin yin banza da dukiyarsa. Sai ya kira manajan, ya tambaye shi, ‘Me nake ji haka a kanka? Ka kawo lissafin aikinka, domin ba za ka iya cin gaba da aikinka ba.’
“Sai manajan ya ce cikin tunaninsa, ‘Maigidana zai kore ni daga aiki, me zan yi? Ba ni da ƙarfin noma, kuma ina jin kunyan yin bara. Na san abin da zan yi, don mutane su karɓe ni a gidajensu, bayan an kore ni daga aiki a nan.’
“Sai ya kira kowane ɗaya da maigidansa yake bin bashi. Ya tambayi na farkon ya ce, ‘Nawa ne maigidana yake bin ka?’
“Ya amsa ya ce, ‘Garwar mai na zaitun guda ɗari tara.’
“Manajan ya ce, ‘Ga takardarka, ka zauna maza ka mai da shi ɗari huɗu.’
“Ya kuma tambayi na biyun, ‘Kai fa, nawa ne ake bin ka?’
“Sai ya amsa ya ce, ‘Buhunan alkama dubu.’
“Ya ce, ‘Ga takardarka, ka mai da shi ɗari takwas.’
“Maigidan kuwa ya yabi manajan nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama ’yan duniyan nan suna da wayon yin hulɗa da junansu fiye da ’yan haske. Ina gaya muku, ku yi amfani da dukiya na wannan duniya, domin ku sami wa kanku abokai. Saboda bayan dukiyar ta ƙare, za a karɓe ku a wuraren zama da sun dawwama.
10 “Duk wanda ana amincewa da shi cikin ƙaramin abu, ana kuma amincewa da shi cikin babba. Kuma duk marar gaskiya cikin ƙaramin abu, zai zama marar gaskiya cikin babba. 11 In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya? 12 In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiyar wani ba, wa zai ba ku dukiya naku, na kanku?
13 “Babu wani bawa mai iya bauta wa iyayengiji biyu ba. Ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗayan, ko kuwa ya dāge ga yi wa ɗaya bauta, sa’an nan ya rena ɗayan. Ba za ku iya ku bauta wa Allah tare da bauta wa Mammon (wato, Kuɗi) a lokaci ɗaya ba.”
(Mattiyu 11.12,13; 5.31,32; Markus 10.11,12)
14 Da Farisiyawa masu son kuɗi suka ji wannan duka, sai suka yi wa Yesu tsaki. 15 Ya ce musu, “Ku ne masu mai da kanku marasa laifi a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abu mai daraja a gaban mutane, abin ƙyama ne a gaban Allah.
Ƙarin koyarwa
16 “An yi shelar Doka da Annabawa har zuwa lokacin Yohanna. Tun daga lokacin nan, bisharar mulkin Allah ne ake wa’azinta, kowa kuma yana ƙoƙarin kutsa kai ya shiga. 17 Gama ta fi sauƙi sama da ƙasa su shuɗe, da a ce ɗigo guda ɗaya na rubutun, ya fita ya fāɗi daga cikin Doka.
18 “Duk wanda ya saki matarsa ya auri wata mace, zina ne yake yi. Kuma mutumin da ya auri macen da aka sake, zina ne yake yi.
Mai arziki da Lazarus
19 “An yi wani mutum mai arziki wanda yakan sa tufafi masu ruwan shunayya, da kuma na lallausan lilin, yana kuma cikin rayuwar jin daɗi kullum. 20 A ƙofar gidansa kuma akan ajiye wani mai bara, mai suna Lazarus, wanda jikinsa duk gyambuna ne. 21 Shi kuwa yakan yi marmarin cin abin da yakan fāɗi daga tebur na mai arzikin nan. Har karnuka ma sukan zo su lashe gyambunansa.
22 “Ana nan, sai mai baran ya mutu, kuma mala’iku suka ɗauke shi zuwa gefen Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi. 23 A cikin jahannama ta wuta, inda yana shan azaba, ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim can nesa, da kuma Lazarus a gefensa. 24 Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’
25 “Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba. 26 Ban da wannan duka ma, tsakaninmu da kai, akwai wani babban rami da aka yi, yadda waɗanda suke son ƙetarewa daga nan zuwa wurinku, ba za su iya ba, kuma ba mai iya ƙetarewa daga wurinku zuwa wurinmu.’
27 “Ya amsa ya ce, ‘To, ina roƙonka, ya uba, ka aiki Lazarus zuwa gidan mahaifina, 28 gama ina da ’yan’uwana biyar maza. Bari yă ba su gargaɗi, don kada su ma su zo wurin nan mai azaba.’
29 “Ibrahim ya amsa ya ce, ‘Suna da Musa da Annabawa, ai, sai su saurare su.’
30 “Sai ya ce, ‘A’a, ya uba, Ibrahim, in dai wani ya tashi daga matattu ya je wurinsu, za su tuba.’
31 “Amma ya ce masa, ‘In ba su saurari Musa da Annabawa ba, kai, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su saurare shi ba.’ ”