3
An Tsawata wa Shugabanni da Annabawa
1 Sa’an nan na ce,
“Ku kasa kunne, ku shugabannin Yaƙub,
ku masu mulkin gidan Isra’ila.
Ya kamata ku san shari’a,
2 ku da kuke ƙin abu mai kyau kuke ƙaunar mugunta,
ku da kuke feɗe mutanena
kuke tuge nama daga ƙasusuwansu;
3 ku da kuke cin naman mutanena,
ku feɗe fatar jikinsu
kuke kakkarya ƙasusuwansu,
kuke yayyanka su gunduwa-gunduwa kamar naman da za a toya,
kamar naman da za a sa a dafa.”
4 Sa’an nan za su kira ga Ubangiji,
amma ba zai amsa musu ba.
A wannan lokaci zai ɓoye fuskarsa daga gare su
saboda irin muguntar da suka yi.
5 Ga abin da Ubangiji ya faɗa,
“Game da annabawa
masu ɓad da mutanena,
in wani ya ciyar da su,
sai su ce akwai ‘salama’
amma in bai ciyar da su ba,
a shirye suke su kai masa hari.
6 Saboda haka dare yana zuwa a bisanku, ba tare da wahayi ba,
kuma duhu, ba tare da duba ba.
Rana za tă fāɗi wa annabawa,
yini kuma zai zama musu duhu.
7 Masu gani za su ji kunya,
masu duba kuma za su ji taƙaici.
Dukansu za su rufe fuskokinsu
gama ba amsa daga Allah.”
8 Amma game da ni, ina cike da iko
ta wurin Ruhun Ubangiji
da kuma adalci da ƙarfi,
don a sanar da Yaƙub laifofinsa,
ga Isra’ila kuma zunubinsa.
9 Ku ji wannan, ku shugabannin gidan Yaƙub,
ku masu mulkin gidan Isra’ila,
ku da kuke ƙyamar gaskiya,
kuka karkatar duk abin da yake na gaskiya;
10 kuka gina Sihiyona ta wurin zub da jini,
Urushalima kuma ta wurin mugunta.
11 Hukunce-hukuncen shugabannin ƙasar na cin hanci ne,
firistocinta kuma suna koyarwa don a biya su,
annabawanta kuwa suna yin annabci don neman kuɗi.
Duk da haka suna jingina a kan Ubangiji suna cewa,
“Ba Ubangiji yana tare da mu ba?
Ba bala’in da zai zo mana.”
12 Don haka, saboda ku,
za a nome Sihiyona kamar gona,
Urushalima kuma ta zama tarin juji,
tudun haikali kuwa zai zama kurmin ƙayayyuwa.