7
Baƙin cikin Isra’ila
Tawa ta ƙare!
Ina kama da wanda yake tattara ’ya’yan itatuwa
a lokacin kalar ’ya’yan inabi;
babu sauran nonon inabin da za a tsinka a ci,
babu kuma ’ya’yan ɓaure na farko-farkon da raina yake marmari.
An kawar da masu tsoron Allah daga ƙasar;
babu sauran mai adalcin da ya rage.
Dukan mutane suna kwanto don su zub da jini;
kowa yana farautar ɗan’uwansa da tarko.
Dukan hannuwansu sun gwaninta wajen yin mugunta;
shugabanni suna nema a ba su kyautai,
alƙalai suna nema a ba su cin hanci,
masu iko suna faɗar son zuciyarsu,
duk suna ƙulla makirci tare.
Mafi kyau a cikinsu yana kama da ƙaya,
mafi gaskiyarsu ya fi shingen ƙaya muni.
Ranar da Allah zai ziyarce ku ta zo,
ranar da masu gadinku za su hura ƙaho.
Yanzu ne lokacin ruɗewarku.
Kada ka yarda da maƙwabci;
kada ka sa begenka ga abokai.
Ko ma wadda take kwance a ƙirjinka,
ka yi hankali da kalmominka.
Gama ɗa yakan ce wannan ba mahaifinsa ba ne,
diya kuma takan tayar wa mahaifiyarta,
matar ɗa takan yi gāba da uwar mijinta,
abokan gāban mutum su ne iyalin cikin gidansa.
 
Amma game da ni, zan sa bege ga Ubangiji,
ina sauraron Allah Mai Cetona;
Allahna kuwa zai ji ni.
Isra’ila za tă tashi
Kada ku yi farin ciki, ku maƙiyana!
Ko da yake na fāɗi, zan tashi.
Ko da yake na zauna a cikin duhu,
Ubangiji zai zama haskena.
Domin na yi masa zunubi,
zan fuskanci fushin Ubangiji,
har sai ya dubi batuna
ya kuma tabbatar da ’yancina.
Zai kawo ni zuwa wurin haske;
zan ga adalcinsa.
10 Sa’an nan maƙiyina zai gani
yă kuma sha kunya,
shi da yake ce da ni
“Ina Ubangiji Allahnka?”
Zai gani, yă kuma ji kunya.
Ko yanzu ma za a tattake shi
kamar taɓo a tituna.
 
11 Ranar gina katangarka tana zuwa,
a ranar za a fadada iyakokinka.
12 A wannan rana mutane za su zo gare ka
daga Assuriya da kuma biranen Masar,
daga Masar ma har zuwa Yuferites
daga teku zuwa teku,
kuma daga dutse zuwa dutse.
13 Duniya za tă zama kufai saboda mazaunanta,
saboda ayyukansu.
Addu’a da yabo
14 Ka yi kiwon mutanenka da sandarka,
garken gādonka,
wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi,
a ƙasa mai kyau ta kiwo,* Ko kuwa a tsakiyar Karmel
bari su yi kiwo a Bashan da Gileyad
kamar a kwanakin dā.
 
15 “Kamar a kwanakin da kuka fito daga Masar,
zan nuna musu al’ajabaina.”
 
16 Al’ummai za su gani su kuma ji kunya,
za a kuma ƙwace musu dukan ikonsu.
Za su kama bakinsu
kunnuwansu kuma za su zama kurame.
17 Za su lashi ƙura kamar maciji,
kamar dabbobi masu rarrafe a ƙasa.
Za su fito daga maɓuyarsu da rawan jiki,
za su juya cikin tsoro ga Ubangiji Allahnmu
su kuma ji tsoronku.
18 Wane ne Allah kamar ka,
wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu?
Ba ka zama mai fushi har abada
amma kana marmari ka nuna jinƙai.
19 Za ka sāke jin tausayinmu;
za ka tattake zunubanmu a ƙarƙashin sawunka
ka kuma tura dukan kurakuranmu zuwa cikin zurfafan teku.
20 Za ka yi wa Yaƙub aminci,
ka kuma nuna jinƙai ga Ibrahim,
kamar yadda ka yi alkawari da rantsuwa ga kakanninmu
tun a kwanankin dā.

*7:14 Ko kuwa a tsakiyar Karmel